← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 133

Sashe 81

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauri Officer police din ke shiga prison din matan wasu mata masu ma'aikatan prison din matan biye dashi harzuwa gaban wani daki da aka rubuta _dark room_ ajiki, yawanci dakine da ake saka wayanda sukai laifi suyi kwana da Kwanaki aciki, makulli officer ya karba daga hannun daya daga cikin guards din dasuka biyoshi yabude kofan kafin yatura kofan da karfi dan tsakurkurin dakin ya bayyana da sauri wacce ke ciki tasa duka hannayenta tarufe fuskanta dan jitayi hasken kaman anzuba mata yaji a idanu takasa bude ido, da sauri officer yace "kufito da ita ku kaita waje an sallameta" daya daga cikin guard dinne tace "wai munhuta da jaraban _Barkono_ kenan" suka shiga kafin suwani irin fizgota gashinta ya barbaje ya rufemata fuskanta sukajata suka fito da ita kaman sun dauko mattacen rago har zuwa gaban kanta prison inda kake karban abubuwan da mutum yazo dashi prison yasaka yabasu kayansu, officer dake bayansu ne yace "kai yarinyar nan case din senate president ne yace ai release nata with immediate effect banda lokacin dazan jiraku nemo mata kayanta ku fitar da ita ahaka ta tafi da kayan gidan yarin mun bata, ku fitar da ita ta nemi hanyan gidan ubanta" da sauri sukace "yes sir" janta suka sakeyi kaman wata kayan wanki suka fito daga prison din......
Kika fitarmin da book waje? To banyafe miki ba
Yanacikin waya kaman ance yadaga kai yaga ya hango some security guard harsu hudu sunajan wata da baya iya hango fuskanta sabida gashi daya rufe kanta gabaki daya har wuyanta kaman wata animal, shi in his life he hates inhumane treatment daidai sunzo zasu wuce ta gaban motarshi yabude yafito da sauri duk suka tsaya sukace "sannu Dr" bai tsaya amsa gaisuwan suba yace "why are you people treating a prisoner like an animal jibi yanda kuka janta, by the way ina zaku kaita?" daya daga cikinsu ne tace "Sir an sallameta dama tuntuni ta addabemu a prison mun daketa mun daketa kaman jaka she's so violence shine daga baya muka kulleta a dark room dan ita tafasama yarinyar dakama surgery dazu ciki da karfe which anyi hani da sharp object a prison shine take receiving serious punishment, yanzu kuma kawai oga yazo yace ansallameta mufitar da ita waje ta nemi hanyar gidan ubanta" ahankali ya girgiza kai yace "kuji tsoron Allah no matter what, no matter how she is she's entitled to her constitutional right, wanan abin kuma is maltreatment, look at her condition how do u people expect her taje gida dakanta tamasan inda kanta yakene?" tabe baki daya daga cikin matan tayi tace "pls sir we are only doing our job, kai u are just a per-term doctor bakasan how things run in this school ba, kuma yarda ita mukoma ciki pls" sukabi ta gefenshi sukadanyi nesa kadan da inda yake suka wani irin jefar da ita kaman wata mushe sanan suka koma ciki batare dasun kalli ko inda yakeba.

Tsayawa yayi yana kallon yanda yarinyar ke akulle he took an oath a proffesion dinshi yay protecting life and to help anyone that is in need of medical attention bari yadauke ta yakaita asibiti inta warke properly saita koma gidansu kokuma yatayata kiran iyayenta suzo su dauke ta, tunanin hakan yasa ya shiga mota yatada yaja harzuwa inda suka jefar da ita sanan ya kashe motan yafito yazo inda take ahankali ya tsugunna yay bismillah yadauketa ko kadan batada nauyi sanan yabude bayan motan shi ya sakata yamaida kofan yarufe sanan yakoma gaba ya shiga yaja motar yana kallonta ta glass din gaban motar har lokacin fuskanta arufe da gashi.
In kika karanta batare dakin biyaba Allah ya isa.

Kaman wacce aka tsungulla tadaga hannu ahankali tadaura kan gashin dasuka rufe mata idanu tajasu ta matsar dasu gefe fuskar Aneesa ya bayyana, idanunta sunyi bakinkirin ta labka wani irin uban kwalli kaman wata yar daba, fuskarta yay baki, pink lips dinta ne yakenan jajir kaman fresh meat, ahankali take bude ido dayake glass din motar tinted ne motan babu wani haske sosai yasa ta iya bude idanun kadan kafin ahankali tabude idanun duka fuskarta babu alamun ko digin dariya, idanunta sunyi wani iri kaman bana Aneesa ba ahankali take kallon saman motan zuwa ko ina na motan ahankali har idanunta suka sauka akan mutumin dake tuki abinshi hankalinshi akan tukin da yakeyi wani soft music natashi, wani irin daga kafanta tayi ahankali tajawoshi ta daidai inda hannunta zaikai ahankali tasa hannu taja wando ta sama, saiga wata yar wuka ta bayyana acikin bakar safar dake kafanta dake cikin kumbos din kafarta na prison, ciro wukantayi tawani irin tashi zaune tamike tsaye tadane bayan kujeran driver kaman wata yar biri takama kan Dr tadaura wukan akan wuyanshi cikin wani irin murya kaman ta rikakkiyar yar daba tace "waye kai? Me nakeyi a motar ka? Ina zaka kaini? Kasan waka dauko kuwa?" tai maganan tana kara rike kanshi gam ko motsi baya iyayi takara danna wukar akan makogoronshi kaman wacce ke shirin yanka rago motarsu a kwana kwana kaman zasuyi hatsari amma ko dar.
[09/04, 07:29] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

5️⃣3️⃣

Cikin wani irin yanayi na wanda ke kokarin kwatan kanshi yadan bugi hannunta dake wuyanshi trying to free kanshi da kyar yace "a....am..a..." baikai ga karasa maganan ba motar nasu tawani irin yin gefen hanya ta doshi wani babban bishiyar mango zai daki bishiyan dakenan gefen titi cikeda karfin hali irin na kwararren namijin daya iya tukin mota ya take burki da duka karfinshi hakan yasa tayoyin motar suka wani irin yin kara motar ta tsaya bayan sunyi kaman zasu fadi, hannun Aneesan yarike da kyar yanaja daga wuyanshi da kyar yace "pls....am....a....Doctor, likit....." ganin yana shirin mutuwa yasa ta janye hannun nata daga wuyanshi ya shiga tari kafin ta zagayo tadan hanyan dake in between kujerun gaban, tawani irin tsugunna kan wajen tai pointing mishi wukan hanun nata tana kallon yanda yake tari, ganin tarin yaki tsayawa yasa tadau goran ruwan datagani a motar ta bude tamikamai ahankali yasa hannu yakarba batare daya kalleta ba yakafa abaki saida ya shanye ruwan tass sanan ya cillar da goran kasa, saida yaji dama dama, tarin yadan natsu kafin ahankali yadago kanshi tareda juyowa ya kalleta hada ido yayi da Aneesan data tsugunna tana mai pointing yar wukan hannunta ko kyafta ido batayi kaman yay gamo da yar aljanna, saida gabanshi yafadi, gabaki daya sorrounding din idanunta sunji bakin lalle kwayar idanunta ne kawai fari, gashinan nata yay daka daka ya barbaje akan fuskanta ya sauka har kafadarta ya rurufe mata kunnuwa, cikin wani irin yanayi na mugun jin haushin ta yace "are you mad?" gyadamai kai tayi tace "yes" cikeda masifa yace "are you mad kasheni kikeso kiyi ne?" ko gezau batayiba da tambayanshi cikin dakewan murya tace "ba kashe ka zanyi ba, but zan kasheka yanzu in baka bani amsar tambayata ba, nace waye kai? Me nakeyi acikin motarnan" cikida fushi yace "naga some guards sun fitoda ke wai a sakeki suka yardake, they dumb u like a piece of gabbage, you don't look good bamakisan inda kanki yakeba shine I took you to drop you at any nearby clinic abaki taimakon dakike bukata, inhar kika tashi saiki tafi gida kokuma kisa akira iyayen ki suzo su dauke ki, but ni ba mugu bane and banda anybad intention akanki" tunda yake maganan take kallonshi saikuma takoma kan kujeran gefenshi ta zauna da kyau tana linke wukanta tace "yau wata daya da sati biyu kenan rabon da wani ko wata yamin mutunci kokuma yamin taimako, hahahaha" ta kyalkyace da dariya saikuma ta tsayar da dariyan tadan tashi tazo wajenshi da sauri yay baya yana kallonta adan tsorace yace "wai me haka? Kinga fita daga motana tunda dai kin farka kinemi gidanku, jibeki as small as ur are but u are so violence g......" hannunta data daura ahankali kan aljihun riganshi ko alamun tsoro batadashi tana kallon fuskanshi yasa yay shiru shima yana kallonta jidayayi hannunta zafi sosai alamun she's running temperature, wayarshi tazaro daga aljihun gaban rigan ahankali kirar iPhone ce wayar tarike a hannu takoma kan kujeran gefenshi ta zauna.
Chapter 81 · 0% Book details