← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 133

Sashe 13

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tanunamai gefen cikin Khamis, farin hanunshi Aliyu ya kalla ya dunkule ahankali yana kallon Aneesan data cije lebe irin ya dunkule hanunnan da kyau dinan tana kallon hannun tana nunamai cikin Khamis din dake sosa ido, daddagewa Aliyu yayi yabugama Khamis uban nishi aciki atare daga Aliyun har Khamis din sukai ihu harsaida Aneesan takoma baya da gudu dan tsoro sabida ihun da Aliyu yayi yana yarfe hannu kaman zaiyi kuka ya kalleta yace "it's hurt, ahhhh, aucchhhh, alottt" sosai yake yarfe hannu hakan yasa ta matso ahankali tana leken Khamis din daya zube akasa dan naushin ya shigeshi gashi yakasa bude ido balle yarama, tsayawa kusada Aliyun tayi dake yarfe hannun nashi dayay jajir tasaka yatsa abaki tana cija danso take suci uban Khamis sosai, kalle kallen compound din ta shiga yi kafin idanunta su sauka kan rigan Khamis din dayacire ya yar da sauri tai wurin rigan tsugunnawa tayi ta dauka ta shiga wurga rigan tana kaman lilo dashi rigan ya shiga kanannadewa danso take tamaida rigan dorina, binta da kallo Aliyu yake yana murza hanunshi harsaida tagama tazo gabanshi da sauri ta mikamai dorinar rigan tace "gashi yayan mu, rama mana da wanan tunda baka iya fadaba, yimai shegen duka da wanan" tamikamai rigan, karban rigan yayi yana kallon fuskarta, nunamai Khamis din tayi tace "zaneshi karka ragamai, ko akotu irinsu bulala tamanin ake musu kaima yimai 80" da sauri ya kalleta yace "80?" kallonshi tayi akaro nabiyu idanunsu yakara sarkewa faduwa gabanta yayi hakan yasa ta kyafkyafta ido sau biyu ta gyadamai kai batare data iya magana ba ta kawad dakanta, ahankali Aliyu yakarasa inda Khamis din yake azube yana sosa ido ya daddage ya shaudamai ihu yayi. "Aliyu wlh idan idanuna suka bude saina kasheka dagakai har shegiyan na..." zubamai nabiyu Aliyu yayi da karfi hakan yasa Rauda ta rungume Aneesa cikeda murna suka shiga tsalle kaman sunsan juna Aneesa harda tafi wani masifar dadi takeji fiye da tunanin mutum, cigaba da dukanshi Aliyu yayi da rigan sunamai tafi itada Rauda harya yarda rigan ya zauna agefe yana haki yagaji, da sauri ta kalli Rauda tace "ina zuwa bari kuga" da sauri tabude gate tafita jakanta tabude ta ciro wani kwababben bakin lalle da mai saida lallenta yahada mata as sample dan kafin tasiya saitasa ya dama mata tadanyi Zane kadan a hannunta ta wanke dan taga iya bakinshi dan kwanaki tasai lalle ko kadan baya baki dudda hydrogen din datake zubamai, shigowa tayi da sauri rike da ledan lallin ta kalli Aliyu tace "Yayan mu daga shi ka zaunar dashi kaga" kasa mata musu Aliyu yayi Yajuya yadago Khamis din da karfi ya zaunar dashi, tace "yauwa rikemin hanunshi tabaya" tsayawa abayanshi Aliyu yayi yarike hanunshi gam, da kyar Khamis dabaya iya bude ido ke magana yace "wlh duk kun shiga uku koba yauba yau ranan kuc...." bai karasa maganan ba Rauda tazare flat shoe kafarta tai bugamai abaki aiko sai jini, dariya sosai Aneesa tayi dayasa dimples dinta lotsawa tana kallon Raudan tace "dama kinada karfin nan tuntuni kiketamai kuka matsoraciya" takarashe maganan tana dariya sosai kafeta da ido Aliyu yayi ko kyafta ido bayayi kaman ance ta kalli gabanta suka kara hada ido shiru tayi ta saukar da idanunta kasa tadan matsa gaban Khamis din sosai kirjinta na bugawa tana gyara bakin ledan lallen, ahankali ta shiga zanamai bullen mage tundaga gefen bakinshi har zuwa wajen sajenshi uku uku sanan taja wani dogon layi tundaga kan hancinshi har zuwa goshinshi shidai Khamis sanyi sanyi da waiwayi waiwayi yakeji akan fuskarshi amma yarasa me akemai, fashewa da dariya sosai Rauda tayi ganin abinda Aneesa tamai harda bubbuga kafa akasa kaman ba itace tagama kukaba da barkakken riganta, mikewa tsaye Aneesan tayi itama tana kallon fuskanshi ta harari Rauda cikeda murmushi tace "am happy you are now smiling nidai nagudu gida, you guys should run for your lives, kugudu kafin idanunshi subude" ta kwasa da gudu tabude Gate tafita da sauri Rauda tabita tana kwala mata kira tace "baiwar Allah, baiwar Allah baki fadamin sunanki ba to" juyowa Aneesa dake kwashe kayanta nakasa awajen Gate din tayi ta kalli Raudan tai murmushi tareda rataya jakanta akafada tace "sunana Nana Fateema" "can we be friends? Inason ki sosai you are so bold wat a fearless lady, a ina kike? Inane gidan ku? Anan Suleja kike?" Rauda tai maganan tana karasowa gabanta murmushi tasakeyi zatai magana idanunta suka sarke dana Aliyu dake tsaye jikin Gate yazuba mata idanu hanunshi zube a aljihun riganshi yana kallonta sosai gabanta yafadi, dan kyafkyafta ido tayi tana kallonshi kafin ta juya da sauri tama Rauda waving hannu tace "bye Friend" daidai lokacin keke napep na zuwa tareshi tayi ta shiga ciki sukai gaba dukansu tsayawa sukayi a inda suke sukabi keke napep din da kallo har yafita daga layin.
[04/03, 16:28] Aishat Muhammad: [11/02, 05:11] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

9️⃣

_How to subscribe_

_*Zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting*_

_*zaki iya turo katin MTN 300 in baki da banki ta watsap number na 07012181461, sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya*_

For a moment harta manta da matsalan datake ciki dasuke magana da Aneesa not until lokacin da keken data shiga ya bacema ganinta, juyowa tayi ahankali hada ido sukayi da Aliyun dayamata wani irin mugun kallo da baitaba mata irinshi ba kafin yafito daga cikin gidan yay wurin motarshi da sauri tabishi bude mota yayi ya shiga hakan yasa tabude dayan side din ta shiga tana kallonshi batada burin daya wuce yacemata wani abu amma saibaice ba, kunna mota yayi batare dayace mata komiba hannayenshi duk ciwo sukemai yaja motar, sosai taji jikinta yawani irin mugunyin sanyi hakan yasa ta saukar da kanta kasa gabanta sai faduwa yake, da azababben gudu yakejan motar Haryakai kai gidansu uppan baice mataba wani mahaukacin horn yadanna daya daga cikin sojojin gaban Gate yazo yabude musu Gate din yaja motar cikin gidan a tsakar gida yaga Dad sai zirga zirga yake yana sanye da jallabiya mai ruwan goro dayake yau weekend baifitaba yana gida, ganin motar Aliyu yasa tun kafin motar yay parkin yay wurin motar, daidai Aliyu yay Parking yabude motan yafito ranshi abace, tsareshi Dad yayi yadaura duka hannayenshi akan kafadarshi yana nazarin fuskanshi cikeda tashin hankali yace "Son kakirani kana cewa menene menene, banma gane mekake cewaba sai kuma ka katse wayan, were you attack? Nasaka bodyguard bin bayanka gashinan kuma kadawo, wat happen to you Gadanga na iyye? Ya akayi idanun ka sukaija hakk...?" kasa karasa maganan yayi sabida sauka da idanunshi sukayi kan hanun Aliyu, yanda yaga hanun Aliyun yay jajir kaman ya kone da ruwan zafi yasa da sauri yasaki kafadar Aliyun yakamo hanun yarike arude yana kallo yace "wat happen to your hand Son? Maiya sameka, talk to me Aliyu? Me haka hanunka yay jajir where you attack?" Dad yay maganan kaman zaiyi kuka dukya birkice, ganin yanda Dad din ya rude yasa yadan yatsine fuska tareda fizge hanunshi yace "am fine Dad don't worry am fine" yay maganan yana bin gefen Dad yay dayan side din motar, Dad yabishi dasauri yace "don't tell me you are fine Aliyu, mai ya sameka idanunka sukai ja haka hanunka yay ja shi...."cikin fushi yabude kofar motar, lekowa Dad daya biyo bayan Aliyun yana tambayanshi maiya sameshi yayi ganin Rauda zaune kan kujeran gaban motan rigan ta abarke sai rirrike wurin barkewan take da hannu, babu dan kwali sai kuka take gefen fuskarta ya kumbura suntun hakama bakinta, idanun ta sunyi jajir sai wani kukan take ganin Daddy, hadiye wani miyau mai daci Dady yayi cikin wata irin muryan mamaki yace "Rauda?" ya kalli Aliyun yace "tareda Rauda kuka fitane, but you went out alone, a ina ka ganta? Maiya sameta haka? maiya faru? You guys should answer me ha'a" dan cizan lips Aliyu yayi yasaki ahankali yace "I was on my way going to Momma's place Rauda takirani dawani number crying wai Khamis was trying to rape her, da kyar nagano inda take a Suleja....." nan yabama Dad duka labarin daga farko har kashe ranshi duk abace yace "Dad ba cousin dintaba kowa who the hell that Khamis is I've cancelled their marriage, bazan taba bari my sister to marry that kind lowlife of a being that could stood so low har yay kokarin molesting mace ba" cikin bala'in fushi Dady ya kalli yanda take babbaka kuka yace "dan gidanku kimin shiru anan kafin na kikkifeki da mari, ubanme yakaiku har Suleja? Iyye ubanme yakaiku har Suleja, ba wajen mamarshi Mamanki tacemin zai kaikiba, yawon banza kika fara Rauda? Yawon banza?" girgiza ma Dady kai tayi da sauri wasu sababbin hawayen nabin idanunta tace "Dady wlh Mama tace mai wai yakaini yawon bude ido sai dare zai dawo dani, ni kuma tace dole saina bishi dankar nazauna agida Ya Aliyu nanan wai wurinshi zani, shine yakaini gidan" tafashe da kuka sosai mai tsumma zuciya, cikin wani irin tsananin masifa da fada Dady yace "ni Khamis zai lalata ma Y'a, yarana yama haka?" ya kalli Aliyun da Raudan da duk sukai wani iri barinma Aliyu kana ganinshi kasan yau yay abinda bai tabayiba, Dady yay kwafa cikin tsananin jin ciwon yanda Khamis yataba mai yace "zai gane kurenshi, Allah dawo da Kareematun ai zata dawo gidan nan tasame ni, tashi kiwuce ciki ki chanza kayan nan kiyi wanka zan kira muku likita yazo yadubamin ku wlh saiyasan yatabaku, wlh kuwan" yay maganan yana rike habar Raudan yana kallon yanda gefen fuskarta da wajen kunenta yay suntum, sakinta yay ahankali yace "sannu kinji, tafi dakin ku kiyi wanka ki chanza kayan nan kizo falona" gyadamai kai tayi tawuce tana tafiya ahankali.
Chapter 13 · 0% Book details