← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 133

Sashe 80

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sukai flat din Maman su Rauda, agaban dakin CCTV Dady ya tsaya yasaka password sanan yashiga ciki Aliyu biye dashi da sauri Dady yay gaban laptop din kafin yatabe tabe ya kunna footage din ranan, ya tariyo har zuwa daidai inda Aneesa ta shigo part dinshi yace "gashinan ka kalla da idanunka" rungume hannu Aliyu yayi akirji yana kallon footage din tundaga yanda ta tsaya ta kwance zani ta zuba poison din takaimai har zuwa inda tafito da gudu daga flat din, pursing video Dady yayi ya kalli Aliyun dake kallon system din har lokacin rungume da hannayenshi akirji yace "you believe me now, ka yarda da magana ta ko, Aneesa wanted to kill you, taso takaika lahira and listen Aliyu kowaye yace zai tabaka a duniyan nan wlh sainaga bayanshi, Aneesa ba sai randa tagama biyan bashin offense dinta tsaf sanan zaku kara ganinta, I can't forgive yarinyar datasa dana yaje hell yadawo ba, pois......." hannu Aliyu yadaga ma Dady yana juyar dakai tsabagen yanda ya tsani Dady na ambaton Aneesa na neman kashe shi, yace "listen Dad, lemme even turn the table around na fuskance ka ta yanda ka fuskanci zancen" yay dan shiru trying to calm kanshi down danjiyake kaman zai kama da wuta yace "yes, na jika nakumaji dukkan bayanan ka naji yes Aneesa poison me and she tries to kill me and CCTV Camera ya kamata ta hanyar recording komi naji nakuma yarda" yay dan shiru yana sauke ajiyan zuciya kafin ya kalli Dady yanuna kanshi yace "Dady ni Aneesa taso takashe ko? And I think nine dindai yau standing right in front of you alive and healthy harma nake maganan nan dakai kaga koma miye abinda tasoyi bata cimma anniyanta ba, Dad ka saurareni da kyau" yasake yin shiru kafin cikin kakkausar murya yace "ni aka cuta ko nine nai going through all the pains of the poison, so Dad inhar hakane ni dinan da Aneesa taso takashe injika tabani poison na janye maganan, na yafemata sanan koma ina kasa aka kaita ka kira a saketa let Aneesa be reunited da mahaifiyar ta yauyau dinan" wani irin kallo Dady yamai yace "you must be very very silly Aliyu dahar zakai tunani zan iya sakin Aneesa sabida kace, I know the kind of pain you went through Aliyu, nine nasan wahalan dakasha, ikon Allah ne yasa kawai baka mutuba, Gadanga bazan yafema Aneesa ba wlh tunda taso cutar dakai saita biya bashin dataci sanan karka karamin maganan nasa asaketa dan hakan bazai iya faruwa ba" cikin wani irin murya Aliyu yace "Dady you are so cruel, so mean, so heartless and Dad you are so wicked!" dawani irin fushi Dady yadaga hannu zai zubama Aliyu mari. "Aliyu!" saikuma ya tsaya batare daya saukemai marinba, cikin mugun fushi Aliyu yace "slap me Dad, hit me kaman yanda kama Aneesa dayafimini dan u are not that man I use to look at as my hero, mutumin danake ma kallo as the best father in the world, u are not Dad, you are nothing but a heartless wicked Man with no any compassion" da yatsa Dady yanuna Aliyu yace "watch your tongue Aliyu sabida nasoka da yawa na lalataka doesn't mean u are the father am the son dazaka dinga gayamin magana ba, I did what I did to fight for you, sabida kai nai hakan, abinda nayi was for love and justice, bana zalunci she tries to kill you and polisawa sukai arresting nata for attempt murder" wani irin ihu Aliyu yayi kaman zai fasa gidan yace "how can you believe what you saw on CCTV footage Dad? I tot u are way smarter than this? Visuals can be deceptive Dad, sau nawa mukasha gani a movies anyi video dashi wanda yake video yasan baitaba yin abu makamancin abu hakaba, menene computer bayayi? The only thing da computer bayayi shine ya busama dan Adam numfashi, how can you believe this eh?" ahankali ya sassauta murya yace "okay Dad am sorry for yelling at you, kasa asaki Aneesa yau and I promise you cikin just 2 days two days kadai zaka bani I will prove to you cewa this is not a real video is just a set up I promise Dad amma kafara sa asaki Aneesan, Dad Aneesa bazata taba iya kasheni ba, bazata taba iya samin poison a abinci ba I promise you Dad, kasa asaketa kaji Dady" wani kallo Dady yamai cikeda taurin zuciya dakuma tsatsauran ra'ayi yace "No one breaks my policy easily Aliyu inhar akanka ne, batun yau nasha fadaba any body dat dares comes for you will definitely sees my other side, bazan taba sakin Aneesa ba Gadanga harsai tai paying for her crimes and that's final" wani irin kallo Aliyu yakema Dady kaman yanda Dady ke kallonshi kafin yawani irin juya yafita daga dakin azuciye da sauri Dady ya bishi yace "kai Gadanga ina zaka eh? Wai mesa kacika bakin zuciya ne, Gadanga" generator house dinsu Aliyu yayi Dady na binshi da gudu yana kwalamai kira har hakan yasa aka fara fitowa ana kallonsu, jarkan petrol Aliyu ya dauko da sauri Dady yamika hannu zai karba yace "lafiyan ka Gadanga ka haukace ne?" cikin ihu sosai Aliyu kaman wanda zai hadiye zuciya yamutu ya fizge jarkan yace "leave me alone" ya bude jarkan ya shiga antayama kanshi petrol din yana kallon Dady dake kallonshi a mugun rude saida yagama juye fuel din ajikinshi sanan yawani irin jefar da gallon din yatura hannunshi a aljihu yaciro wata sabuwar lighter, ihu Dady yayi yace "kai Aliyu ka haukace ne" yay kanshi cikin wani irin yanayi na kaman zarewa Aliyu yace "don't come here Dad ka tsaya a inda kake, yace badai nine matsalan kaba takaina kake azabtar da yarinya yau zan kona kaina, na kashe kaina, in mutu right in front of your two eyes Dad then you will understand the pain Mum is going through na rabata da yarta dakayi ka kaita chan wata duniyan da babu wanda yasani, Dad Aneesa ita kadaice macen da zuciyan danka ke bugun mawa, I love her, I love Aneesa Dad, how dare you ka kulle min wacce nakeso for a month plus eh Dad" Dad dayadawo kaman zararre yamikama Aliyu hannu cikeda lallashi yace "kaga Gadanga na kayakuri, calm down, kar wanan zuciyan naka yakaika ga halaka Hydar, ka kashe kanka wuta zaka, calm down okay, bani lighter kayakuri" girgiza mai kai Aliyu yayi cikin tsananin fushi yace "kasa ayi realising Aneesa right now Dad, right now Dad kona kashe kaina" da sauri Dad yana girgiza kai yace "to, to to naji, zansa" ya shiga laluben wayanshi dake aljihu yaciro yashiga dannawa dukya rude kaman zararre yace "don't do anything stupid Aliyu kanajina ko, zan kira yanzu" "Hello officer, I.....i...." yana maganan yana kallon Aliyu alamun kyasta lighter Aliyu yayi yace "now Dad" da sauri Dady yace "I withdraw the case against Fateema Aneesa Maikwato, ku saketa re...release her" katse wayan yayi yana maidawa aljihu ya kalli Aliyu yana mikamai hannu yace "done nafada zasu saketa, oya oya bani lighter, bani Gadanga kaji" wani irin kallon Dady yake kafin ahankali yace "ka azabtar da Aneesa right in front of her Mother's eye, Your pregnant wife the woman that was bearing your child in her womb suffered, got sick, always crying pleading kasaki Aneesa kaki, yan uwan baban Aneesa they all came sun rokeka kaki, Dad duk sabida ni wanan Aliyun daba komin komiba kake wulakanta mutane haka, akaina bakasan menene yafiya da hakuri da tausayi ba all this 3 u lost them, Dad now watch kasan Yaya mahaifiya keji idan taga abinda ta haifa nashan azaba" yana maganan ya kyasta lighter.................

Wani irin ihu Dady yayi kaman zai haukace. "Aliiiiyuuuuu......" chak ya tsaya yay shiru ganin hannun daya chape lighter tun kafin wutan yafito daga ciki, hannu Ammi tasa ta mareshi hawaye na zubowa daga idanunta tace "are you mad Aliyu kashe kanka kakeso kayi kamutu kafiri?" fashewa da kuka sosai Aliyu yayi yafada jikin Ammi for the first time yarugumeta. "am sorry Mum, am sorry mum, Mummy forgive me" da goshi tayi daga jikinshi tasa hannu ta sharemai hawaye tareda girgizamai kai tace "never in your life try such things again, Aliyu don't ever go this extreme sabida kanaso amaka abu, wuce kaje kai wanka ka chanza kayan nan" gyadamata kai Aliyu yayi yajuya yanadan dingishi yay hanyar flat dinshi batare daya kalli Dad ba, itama Ammi ta juya da sauri dan yanda ya shafamata petrol warinshi nasata jin amai sosai da sauri ta shiga bathroom dinta tana kaiwa flat dinta.

*_ZILANIOUS PRISON HOME AND CONFINEMENT_*

_Theatre_
Wutan theatre da aka chanza daga Red zuwa fari ne yanuna alamun angama operation din, bude kofa akayi wasu likitoci ne guda uku mata biyu saikuma namijin Dr dasuka saka a tsakiyan su dake rike da folder, folder yamika ma Dr dake gefenshi yace "hold this Dr Farida, write on the surgical procedure, I gat to go now, My Mum has been calling batajin dadi sosai" karban folder tayi tace "ayyah Allah kara sauki Dr Zaid" handglove din hannunshi yacire yazuba a abin sharan dake gaban theater sanan ya wanke hannunshi a wash hand basin din dake wurin ya cire lab coat dinshi yarike hakan ya bayyanar da cooperate dress din dake jikinshi na riga da wando blue da black yay zanzaro, ga neck tie, hannu yadaga musu alamun bye yajuya yafita, masu gadi dake bubbude mai kofa namai sallama harya fita wajen prison din inda ake parking motoci yashiga cikin wata fine jeep yarufo, yana kokarin tada motar ne wayarshi yashiga kara hakan yasa yadauka yakara akunne........
Chapter 80 · 0% Book details