← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 133

Sashe 124

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau jumma'a yaune Walima, Waliman da iyaye both maza da mata, abokan ango, ango, dakuma mata iyaye, da yara da kawayen Amarya.
Wani dankareren Hall aka kama Transcorp Hilton Abuja, inda wanan shahararriyar event planning company na Zeebabyo event planning company na Zainab Babayo aka bama contract din, aiko she killed din dan duk wanda ya shiga Hall din gani zaiyi kaman ya shiga heaven, gawasu hadaddun small chops da aka jejjera akan tables din da Gafaiya's kitchen aka bama contract din and yar mutan Gafai kam executed the work perfectly, sosai manya manyan jama'a yan siyasa suka cika Hall din, in bamaka da gate pass don't even come close, wani irin hadadden Abaya specially customise for Aneesah tasaka wanan hadadden International designer din base in dubai mai suna Walid Atallah ne yamata, shi kanshi Aliyu he couldn't take his eyes off his wife, zaunar da ita akayi kusada Aliyu akan wani hadadden kujera kafin manya manyan Malamai both na Nigeria da kasar waje sufara wa'azi. The first speaker was Mufti Menk yay magana on how to love and what is love aiko ya dagargaza topic din. Second speaker wata babbar malama ce mace mai suna Maryam Lemu tai magana akan patience in Marriage, sai third speaker wani babban malami ne dan Nigeria mai Suna Dr Aliyu Abu Dujana yay magana akan Love making in Islam, so far so good shine best speaker Aliyu dan yay magana sosai filla filla abunku da Dr ya koyar da Love making abubuwan dayakamata kayi itama tayi, harda su kafin ka koma second round inda hali kayi fitsari sanan ka dauro alwala, mutane dayawa koma Ince kusan kowa na wurin walimar nan sun natsu sunajin bayani kuma sun ilmantu sosai, sanan aka fara cin abinci serve yourself kome kakeso kaci abinci sunfi kala hamsin, sai bayan sallan isha'i aka tashi motoci komar da mutane har sunma yi yawa, Aneesah bata yarda tabi Aliyu ba, tana ganin Dady ya kirashi tabi Abdul da Ihsan sukai tahowansu danta lura Aliyu naso yadanyi practice din wa'azin dayaji awurin walimar da itane.
_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_

_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_

Yau Saturday yau aka tashi da gagarumin biki dudda babu daurin aure, Siddiqatuya Culinary art and school aka bama contract din abinci, saiga su Siddiqa anci chief uniform da dalibanta harda su suka ledan hannu na girki wayaga iyayen tsafta suna girki, su Aisha Humaira itace prefect, su Bara Bara Bara'atu kuma mai rubuta noise maker wai su a Culinary school dinsu in ana girki ba'a magana dan ba'aso kawoyin bakinka su shiga cikin abincin kokuma yawu, aiko sai rubuta su sunayen su suke, Nucy ce number 1, sai Rahima, da Mumy Ramlat.

Chan tsakar gida kuma an kira Lubs wato Lubabatu koroso dancing school, inda suketa wassanni suna rawan koroso antaru ana kallonsu, dayan kanopi tsakar gidan kuma M Yara kidan kwarya center ne yanda tana buga kwarya tana wake su Asiya Mu'azu na amshi saidai kawai kiji kugunki na motsi kika kalla saikiga ashe rawa kike tsabagen dadin wakan, ga Habiba Zilani zaune gefen M Yara sai M Yara tai nisa da kidan kwarya da waka sai kiji Habiba Zilani ta kece dawani matsiyacin guda da wanan mininin hancin nata kaman nawa ke kyazaci wusul aka makala a hancin nan tsabagen dadin gudan, hancin nan duk yay zufa tsabagen aikin gudan dayakeyi, su Sumayya, Fateema, da Faidris ne yan tattara kudin liki suna chusama M Yara a lalita wanan lalita yay birjik da kudi yay kato kya zaci kan yarone a lalitar nan duk kudine, ina kallon Fateema na soke yar dubu a acucu mazan kanta 🤣

Daga tsakar gidan kuwa wajajen gate Ummajaga wato jagajaga Yoruba gang ne ke nasu, sun saka kaya buba and iro sun sassaka igiyan ganga awuya suna buga gangan suna rawa. Ummajaga na waka Wali na amshi. Jaga na buga ganga tace "Baba lawoo mowabebe" sai Wali tai wani irin juyi tana kaiwa kasa tace "alubiri, ohni Mama fesabelu alubiri" yanda suke wakan suna juyawa yasa da sauri Abdul yaje ya shiga zuba musu manni, Jaga na ganin haka ta share zufa ta shiga reramai sabon waka. "abokin ango abokin ango, yes sir, abokin ango eboyi, yes sir, abokin ango babatunde yes sir, abokin ango babawa, yes sir, abokin ango waeje wooo" washe baki Abdul yayi shidai baisan me ake cewaba banda abokin ango dayaji amma wakar tamai dadi ya cigaba da manni.

_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_

_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_

Gaban flat din Ammi kuma yan maiduguri ne kanuri people, sunyi lapaya suna rawa ga turaren wuta sun kukkunna Fauzy ce ajjagora tana wani lankwasa Mum Unais na kada kugu tana wani walwala lapayan su adole yan indiyan nijeriya, su Murja da Zeena da Tang na girgixa, bala'in burge wata babbar kawar Ammi Hajiya Fateema Abdullahi sukayi batasan lokacin data sauko daga flat din Ammi ta shiga watsa musu yan dollars ba, ture Fauzy Mum Unais tayi tazo gaban layin rawan nasu dan Hajiya tafi ganinta ta manna mata tana kadama hajiya gyalenta, dariya hajiya tayi ta watsa mata mum Unais tai ihu Fauzy dasu Zeena suka balla mata mugun kallon nan irin wlh shima sai an rabashi daidai shima atoh.
_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_

_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_

Raye Raye akeyi a tsakar gida, su Bara'atu atu na dauko abinci a tray suna kaiwa mutane anaci anasha, Marisupermarket kuma musamman sukazo tattara gorunan ruwa dana drinks dan tana sayarwa da masu yin zobo da kunun aya.

Haka aka ci biki karfe takwas na dare aka tafi dina inda Fancy makeover ne tama Amarya Aneesah makeup na kece raini tai shiga cikin white gown dinta da still Walid Atallah ne designer, awurin dinner dasu Abdul ne suka shiryama Aliyu anyi barin kudi ajebo children gang wedding, duka abokanan Leo harda na C.A saida sukazo, sunyi rawa a karshe kasa daurewa Aliyu yayi agaban kowa ya shiga kissing din Aneesah zokaji ihu suka shiga buga table ana kiran sunanshi. "Leo! Leo!! Leo!! ! Leo!!!! Leooooo" Aneesah jitayi kaman zata suma da sabida kunya yana sakinta tafada jikinshi rungume ta yayi yana murmushi yaja hannunta suka fita daga hall din yasa ta amota sukai gida abinsu baimata komiba yakai ta har flat dinsu ya kashe mata ido yajuya shi kadai yasan plans dinshi na gobe.

_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_

_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_

Washegari aka shirya Aneesah aka mata wankan turare takasa dena kuka tun asuba yau zata rabu da Ammin ta da kowa sai bata baki ake, saida Ammi tai da gaske sanan aka samu tasha tea, karfe goma Daddy ya shigo da kanshi yafito da ita yakaita flat dinshi Aliyu tagani zaune kanshi akasa, wa'azi Dady yamusu mai kashe jiki sanan yabama Aliyu amanar ta yace inhar yaci amanar Aneesah to yasani nashi yaci, aure hakuri ne, saida yamusu waa'zi tatas sanan yafito da su yasasu amota ya shiga yan gida da yan uwa harda Ammi aka shi shiga mota aka rakasu har Airport Aneesah kuka kaman zata sume suka sauka, fitowa tayi ta rungume Ammi sosai saida Ammi ta shiga kuka itama hakan yasa Inna tace "me haka maman Aneesah keda zaki mata fada tabi mijinta su tafi kike kuka kuma?" rungumeta Ammi tayi tsam batare data saketa ba sosai Aliyu yaji sun bashi tausayi, saida Dady yasa baki sanan Ammi tasaketa yakama hannunta tana kuka tana kiran Ammi yasaka a hannun Aliyu yace "kutafi" juyawa ahankali Aliyu yayi rikeda hannunta tana kuka sosai bodyguards din da Dad yahada shi dasu suka bisu su biyu suka shiga Airport din, saida Aliyu ya juyo yaga su Dad sun shiga motocin su sun tafi sanan ya kalli bodyguards din yace "kuje ku amshi tickets dinku na C.A, am taking my wife somewhere else and not a word of this to my parents" cikeda girmamawa sukace yes sir sukai inda zasuyi checking in da luggage dinsu Aliyun danya basu yace sutafi da komi.

Kan kujera Aliyu ya zauna tareda zaunar da ita ahankali, hannunshi yasa yaja gyalenta baya, sanan yasa handky ya goge mata hawaye, kaman zaiyi kuka yace "stop crying baby".

_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_

_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_
Chapter 124 · 0% Book details