← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 133

Sashe 15

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Da sauri ta shiga falonsu hijabin jikinta ta zare tawurga kan kofa tai wajen Ammin ta, zama tayi kusada ita tana kallon fuskarta tace "Ammi na menene? Maiya sami idanunki sukai ja? Kuka kikayi? Mesu Baffa suka gayamiki daya bata miki rai har kikai kuka?" tai maganan cikeda damuwa sosai, yatsa Ammi tasa ta dungure mata kai tareda kakalo murmushi tace "wayace miki kuka nayi eh uwar tsegumi? Toba kukanai ba kwaro ya shiganmin ido dazu saisa idanuna sukai ja, tashi ki dauko sabuwar wayar taki kisaka chaji kinga sun kawo wuta" murmushi tayi dudda tasan da abinda Ammi ke boyemata amma saita share taje ta dauko kwalin tazauna kusada ita tana bude wayan daga kwalin wayan tazauna gefen Ammi tana bude kwalin, fuskarta Ammi ta kalla idanunta suka sauka akan gefen bakinta daya kumbura, hannu ta takai ta taba wurin cikeda mamaki tace "maiya sameki anan Aneesa?" dan zaro ido tayi takai hanunta ta taba wurin sai a lokacin taji zafi shiru tayi takasa magana hakan yasa Ammi tace "maiya sameki anan? Fada kikayi a kasuwa? Eh ina magana kinyi shiru" dan matsawa tayi gefe kadan tana turo baki dan tasan bakaramin aikin Ammi ba ta maka mata duka tace "Ammi wata yarinya fa na taimaka" "kika taimaka wani irin taimako eh spider girl?" Ammi tai magamam cikeda tuhuma, shiru tayi tana zazzaro dara daran manyan idanuwanta dan lashe pink lips dinta dataji are so dry tayi tace "Ammi wani nefa keta janta akasa ya barka mata riga shine na shigan mata daga karshe ma yayanta yazo yako rama mata sanan nadawo" gyadakai Ammi tayi tanamata wani irin shegen kallo tace "aahh ba shakka Spider girl" kasa daurewa Aneesan tayi dudda fada Ammi take mata saida tai dariya sabida yanda Ammi tafadi spider girl din, tallabe mata keya Ammi tayi tace "nikike ma dariya inai miki magana" tabe fuska tayi kaman zatai kuka tana kallon Ammin, Ammi tace "wato saisa kika dade kenan ashe ko daman, Aneesa" Ammi ta kirata cikin kakkausar murya tace "banhanaki shiga shara ba shanu ba eh? Aneesa ina gujemiki matsala bakiji, baki fahimta, bakiji, wai yaya zanyi dakene iyye? Maisa bakijin magana na?" kaman zatai kuka tace "yakuri Ammi bazan karaba to" "yimin shiru anan haka kullun kike cewa, Aneesa karkije kajawo mana bala'i wataran, Allah duk randa kika kara Baffan ki zan kira nafadi mai abinda kikeyi dama sunce ban baki tarbiya mai kyau kinga saisuga balaifina bane" kallon Ammi take tunda tafara masifan hakan yasa tace "Ammi haka sukace wai baki bani tarbiya da kyau?" hararanta tayi tace "wuce kije kisaka waya achaji malama kizo kidaura abincin rana" gyadamata kai tayi ta tashi daga kan kujeran tawuce ta saka wayar chaji sanan tafita tsakar gida dan daura abinci awuta.
***

Ahankali yake bude ido shibaimasan lokacin da baccin gajiyan nan yay awon gaba dashiba, agogon dakin ya kalla yaga karfe biyar na yamman harda yan mintuna, tashi yayi ahankali yashiga bathroom alwala yadauro yafito ya shimfida dadduma akasa yay salla, yana idarwa yatashi gaban wardrobe dinshi yaje ya chanza kayan jikinshi zuwa kayan shan iska, wani brown 3quater da white short sleeve t-shirt yasaka daya kamashi tsamtsam, feffesa turare yayi yazura palm dinshi yafito, fita yayi daga part dinshi yay tsakar gida bayan yadau ball dinshi yana bubbugawa a compound dinsu shi kadai dudda he's missing Dad but baiso yaje side dinshi yaga matayenshi a palorshi, buga ball dinshi yake shi kadai cikeda kwanciyan hankali sosai yaji hanun nashi yadena ciwon kana ganinshi kasan he's so happy, horn din mota yaji anayi ba kakkautawa yasa ya daga kai ya kalli Gate dinsu dan yaga waye yacika mai kunne haka da ihun mota, yana wasa da ball a hanunshi soja yabude gate din motar ya shigo ayanda motar tai parking zaka gane ba lafiya, bubbude kofofin motar akayi aka fito Maman su Rauda ne data watsamai wani kallon tsana dawata mata mai bala'in kama da ita saidai tadan fita tsufa itama tafito daga motar takamo Khamis dake cikin motar tafito dashi ga wanan farin fuskan nashi yasha zanen bakin lalle radau idanun shi abude amma sunyi jajir yana sanye da dogon wandon shaddar shi ta dazu da farin singlet ajikinshi, fashewa yayi da dariya sosai ganin yanda fuskar Khamis din yayi looking so damn funny, yanda yake dariya looks so cute and adorable kasan cewanshi mutun that hardly laugh, dafa cikinshi yayi sabida ciwon dayaji yanamai sabida dariyan da yakeyi ahankali yace "dat girl is so naughty look at wat she did to him" yay maganan yana rungume kwallon a ciki yana kallonsu still yana murmushi dauke kai sukayi sukai falon Dady kana ganinsu kasan bala'i kecin cikinsu.

_Sannu Sannu bata hana zuwa, let's take everything daki daki dan nasamu na isar da desired sakona, love you🥰_
[04/03, 16:28] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

1️⃣0️⃣

_How to subscribe_

_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461, you can also send MTN card ta watsap number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting*_

_Free page_
Cigaba da buga kwallon yayi ko ajikinshi dudda dai yanajin yanda hayaniya ke tashi daga falon Dady amma ko agefen kumatunshi, sauran matayenshi Dady sai bude kofa suke suna fitowa suna tafiya falon Dady, tabe baki yayi yace "I hate this house with passion" cigaba da buga kwallon shi yayi yana wuwurgawa a backboard din dake wurin.
Chapter 15 · 0% Book details