← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 133

Sashe 85

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sosai Baffa yaji kunyan abinda Aneesa tayi, mutumin daya taimaka miki tundaga Abuja yarage miki hanya har kaduna, sanan baki da lafiya yadubaki ya samiki ruwa da sauran su shine zatace ita bata godeba, haba dan Allah. Har kofar gida Baffa yarakoshi yace "dan Allah kayakuri, wlh Aneesa yarinya ce mai tarbiyya da natsuwa situation ne da circumstances yamaida ta haka amma wlh bahaka takeba, dan Allah kayakuri karkakai maganan ta zuci yasa nan gaba ko kanada halin taimako kaki bahaka takeba, ka yakuri dan Allah" akunyace Zaid yace "babu komi Abba, wlh bakomi wlh, ai Aneesa tazama kanwata yanzu" murmushi Baffa yayi cikeda yabawa da natsuwan yaron yace "shiga mota iyali na gida suna jiranka, Allah yamaida kai lpy, mun gode kaji, Allah yayi maka albarka, nagode nagode, kakai gida ka kirani ko hankalina ya kwanta, Allah ya tsare" ahankali yace "Ameen nagode Abba" sanan ya shiga mota Baffa yadagamai hannu yaja motar, saida Baffa yadena hangoshi sanan yawuce masallaci isha'i yayo sanan ya tsaya a shago yasayo madara da milo yadawo ya shigo gidan, matar shi yagani gaban Aneesan da plate din tuwo da miyan kubewa busassa taji kifi tayi tagumi tana kallon Aneesan data dauke kai tana hararan karin ruwan da ake mata.
Sallama Baffa yayi yakarasa shigowa dakin yana kallon Aneesan yadaure fuska yace "meya faru bazata ci abicin bane Maman Hamma?" tagumin datayi Inna ta janye ta sauke numfashi tace "nayi nayi taci wai bazata ci tuwo ba Mai gida" zama Baffa yayi abakin gado baice komiba yace "kawomin ruwan zafi akofi nahada mata shayi" fita Inna tayi Baffa ya kalli Aneesa cikin kakkausar murya danya lura tana bukatan hakan yanzu yanuna mata tuwon dake gabanta yace "dauka kici kona sabamiki, ruwan nan nakarewa zansa acire miki kiyi wanka wanan dauda dakikayi tai yawa, dauka kici nace" yadan daka mata tsawa ahankali tadau ruwan wanke hannun ta wanke hannunta sanan tadau tuwon tafara ci da kyar da kyar kaman tanacin magani Baffa yasamu taci rabi da kyar sanan yahada mata tea yabata tashanye duka, tanacin abincin babu abinda yakeyi sai kallonta Allah ma yaga abinda yagani yaturo Aneesa nan batare data je wurin uwarta ba, da ace Ammi zataga Aneesa ahalin yanzu babu abinda zai hanata kuka, ayanda yake ganinta ma kaman tunda aka kulleta batai wanka ba dan dattin datayi yay over, zufan dake gangarowa daga goshinta yanabi ta gefen fuskar ta ne yake kallo yanda zufan tai dauda, ruwan baki ne tsabagen datti instead of farin ruwan zufa, tashi yayi ahankali yafita waje, wata nurse din anguwan su yakira tabiyoshi abaya, ruwan Baffa yasa tacire mata sanan yasa tawuce bayi wanka tayo tafito batare data wanke gashin kanta ba Baffa yakadata yasa inna tabita bayin, duk kumbure kumburen datake yi saida aka wanke gashin kanan tass ita kanta saida taji dadi sanan Inna tadauko mata wata yar doguwan riga cikin kayanta dan batada mace yaranta hudu dukansu maza, nurse din ta maida mata da karin ruwan ko, minti daya bata karaba wani bacci mai nauyi yay awon gaba da ita, sai munshari take saukewa.

Kiran wayan Ammi daya shigo wayanshi yafargar dashi daga dogon tunanin dayaje, da sauri yadaga kai tareda zaro wayan daga aljihun shi yakara akunne yana gyara zama ganin Aneesa tai juyi ya kara wayan akunne yace "Assalamu Alaykum Maman Aneesah" cikeda damuwa daga ta dayan bangaren Ammi tace "kunhadu Baffa? Kaganta? Ta iso?" "eh naganta, gamata nan taci abinci tai wanka bacci ma take yanzu" ajiyan zuciya Ammi ta sauke, ahankali tace "Baffa yakaganta? Karkamin karya koka boyemin wani abu Baffa kaji dan Allah, nida kaina nariga naji hakan ajikina, kafadamin gaskiya Baffa yakaga Aneesah? Yaya take? How is she coping?" kallon Aneesan yayi kafin ahankali yatashi yafita daga dakin, kofar gida yafita ya zauna kan dakali, anatse yace "kawai kidage da mata addu'a, addu'an uwa bata faduwa kasa, Allah na amsan addu'a uwa nan da nan, Aneesah ta chanza, chanzawa ma na muraran karara kike ganinta, abu na farko yanzu dana lura tanada shi shine taurin kai, ga rashin kunya, dakuma mugun fushi da fada kaman jira take, but karki damu all this hallayan tunda dai Allah yayi tafito daga gidan yarin nan da sati duk zata zubar da dabi'un banzan, karki damu kinji" gyadamai kai Ammi tayi murya chan kasa tace "tom" "to ya batun jamb dinta tayi kokuwa date din yawuce?" ahankali Ammi tace "last week ne date din tariga tai missing" da sauri Baffa ganin yanda Muryan Ammi yay kasa kaman mai shirin yin kuka yace "karki damu next year tayi wani, haka Allah ya tsarama rayuwanta bazata taba iya gujema hakan ba, yanzu kawai kidage da mata addu'a Allah yafito mata da miji nagari, aure nakeso tayi, tunda dai yanzu tariga tai missing jamb din batada wani abu daya rage datake yi agida, bata zuwa shago anan babu komi kinga gwara tai aurenta ko" ahankali Ammi tace "hakane Baffa" dan murmushi yayi yace "karki wani damu duk zata zubar da dabi'un nanne within a short period of time, yanzu abinda take bukata shine soyayyan mu agareta da kauna , sanan mujata ajikinmu mununa mata hanya mai kyau, zakiga tadawo daidai sak Aneesan d'a" fira sukayi sosai da Ammi yanata kwantar mata da hankali yaki fadamata batada lafiya harsukai sallama Ammi ta katse wayan kika fitar dashi waje Allah ya sakamin ban yafemiki ba.

Ajiyan zuciya Ammi tasauke sanan ta tashi ta shiga bayi ta dauro alwala tazo tafara nafilfili, Aneesa takema addu'a dan hankalinta yatashi dataji muryanta, me akeyi da mace yar daba? Addu'a tadage da mata bana wasaba, Allah yasaka mata, Allah ya kawo mata miji nagari wanda zai sota tsakani ga Allah tai aurenta tahuta Aneesa taga rayuwa dayawa, ahaka bacci yay awon gaba da ita akan dadduma tana tunanin Aneesah.

Duk wacce ta karanta min littafi batare data biyaba Allah ya isa.
Aliyu yaci kuka yay kuka saida yaji gefen cikinshi namai ciwo sosai sanan yadena kukan shi kanshi baisan haka son Aneesa yamai illa ba saida Ammi tacemai har abada bazasu kara ganinta ba da kyar yatashi ya dauro alwala yay salla sanan yafito, bodyguard din Dady yakira suka biyoshi kai tsaye flat din Maman su Rauda yayi, bude falon yayi batare dayay knocking ba, babu kowa falon sai cartoon din dake aiki a TV, sama yayi bodyguards din biyeda shi har zuwa dakin CCTV, kasan cewan yaga password din da Dady yasaka dazu yasa ya daddanna yashiga kofar tabudu ya shiga dakin, laptop's din ya shiga disconnecting nasu daga fuse sanan ya nunama bodyguards din yace "ku kaimin su dakina" kwasa suka shiga yi shima yadau kwara daya suka fito daidai Maman su Rauda tafito daga dakinta jin motsi ganin Aliyu da bodyguards sun dau computer yasa tace "kai lafiya zaka shigo flat dina without taking an excuse" batare daya daya kalleta ba yace " I came for this" yanuna mata laptop din da baki sanan yay gaba abinshi Maman su Rauda tabishi da kallo gabanta na faduwa, a falonshi aka sausauke computers din yashiga hada connections dinsu, in less than 15minutes yagama ya kunna komi yadauki aiki, kowani computer da flat and side din dayake kamawa, tashi yayi yakulle kofar falonshi sanan yawuce bedroom ya watso ruwa yafito da only boxer ganin yunwa yakeji sosai yasa yawuce kitchen dinshi yabude fridge kwali dayan farmfresh yogurt yadauko da cup yafito yadawo falon throw pillows ya jejjefa akasa yazauna akai ya bude yogurt din ya tsiyaya yacika cup sanan ya ijiye yasha sosai kafin ya ijiye cup din ya shiga aiki he just promised kanshi Aneesa is Innocent he must find the prove this night kodan Ammi tadawo mai da Aneesa sanan tadena fushi dashi.
Chapter 85 · 0% Book details