← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 133

Sashe 45

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kaman ya jawo tsinke haka tadawo luuu numfashinta na fita sama sama kaman zata suma, cike da masifa sosai kaman zai daketa Aliyu yace "how dare you walk out while am still talking to you" kasa magana tayi sai hanunta datake kokarin fizgewa, kara matse hannun yay da kyau dayasa ta runste ido da karfi sabida zafi, cikin muryan fushi Aliyu yace "get this straight I love you Aneesa, I Love You and I don't share what I Love, koma waye kike tareda su kirabu dasu this should be the last time dazan kara ganin kina magana dawani inba hakaba u will see my other side, and you're not gonna like that, last warning!!!" sakin hanunta yayi azuciye yawuce wajen mota, dago kai tayi tana kallon motan daya bude ya shiga tana shafa inda yarike dake mata mugun zafi idanunta sun cicciko da hawaye zuciyarta na tafarfasa, da sauri tasa hannu ta share hawayen wani irin masifa yataso mata, wajen motan daya shiga tayi kaman zata tashi sama ta window inda yake da glass din yake arufe ta tsaya, glass din tinted ne bata iya ganinshi dukan glass din tayi da duka karfin ta da hannu hawaye na cika idanunta cikeda masifa tace "ba'a sonka din, ba'a sonka din do your worse, ance ba'a sonka din" yanda take bubbuga glass din motar zaka zaci fasawa take shirin yi, ganin hannayenta namata zafi tsabagen bugawa yasa ta tsaya tasake sa hannu ta share hawayen daya zubomata ta juya tana kallon kasan wajen tana neme neme, hango bawon ayaba datayi ata gaban motan yasa takoma gaban motan da sauri ta tsugunna ta dauko bawon ayaban ta jefama gaban motan da duka karfin ta kaman shitake jefamawa tace "baza'a rabu dasu dinba, nafi son dukan su, mezanyi dakai masifaffe dakai, sai feeling kaman ka isa dakowa sai kace wani dan sarki, dan kazo da wanan akwalan motan mai kama da bons, kuma daga yau ka kara dawowa gaban gidanmu saina faffasama tayoyin wanan bakar motan, mummunan mota kawai" ta tsugunna ta kwashi kasa a hanunta ta watsa ma glass din Abdul ya ware ido tareda kama baki yace "toooooo" da yatsa ta nuna motan tace "karka kara zuwa anguwan nan, kuma kaima last warning, Allah kasake zuwa saina dauko tabarya na rotsa glass din gaban nan" tawuce tai gidansu a zuciye Aliyu nabinta da kallo barinma cute feet dinta da babu safa ajiki dan saiyau yaga feet nata da kyau yatun masu kyau dake dauke da white fitted nails farare fat.

Wani irin fashewa da dariya Abdul yayi har yana buga kanshi kan abin tuki. "wayyo Allah na cikina, Mommahhh cikina zai fashe" yarike ciki dahar murdamai yake tsabagen dariya da kyar yay shiru ya kalli Aliyu dayaga ya lumshe ido kaman mai bacci nanko duk yagama ganin abinda Aneesa tamusu yace "ashe yar bala'i ka dauko mana Aliyu, wai wai wai nida Anty barkono, chab" yakara kecewa dawani mahaukacin dariya, bude ido ahankali Aliyu yayi dasukai jajir yazuba mai su, hannu Abdul yadaga cike da dariya yace "sorry, sorry nadena" yay shiru yana shafa baki yana kallon glass din motar dayay jajir dan jar kasane a anguwan yace "wai, I mean look at our glass kaman wayanda suka fito daga rami, Allah yasa motarka tama haka da tawace da yasin saika wanke ta, Leo a ina kasamo barkonon nan?" yakara kwashewa da dariya, hannu Aliyu yasa zai bude motan yafita yabarmai dan he's just adding salt to his wound da sauri Abdul yarike shi yana danne dariyan dake cinshi yace "yakuri, yakuri inato zaka? Ihakuri haba Only Friend, but honestly I love her I mean the girl, damn! Masifanta ya mugun burgeni Leo, am just wondering yanda kaida ita zakuyi rayuwa under the same roof kai zuciya ita zuciya inkuka sami mis understanding sunan gidanka gidan kas....kasa Le..." yasake kecewa da dariya, ji Aliyu yake kaman ya shakeshi yahuta kawai ahankali hawaye ya gangaro daga idanunshi yana kallonshi da sauri Abdul ya tsayar da dariyan kaman ba shine ke dariya ba cikeda damuwa yace "Hey Leo mehaka kuma daga wasa, please stop" handkerchief din cikin aljihun shi yaciro da sauri yamikama Aliyun yana shiga taita yin shi, ahankali ya karba ya share hawayen tareda fuzar da iska mai zafi, bude motan Abdul yayi tareda daukan towel din share glass din motar, dariya yakeso yayi ganin yanda Aneesa taci uban motar da kasa saikuma ya gimtse dariyan dan fess Aliyu zai iya tasa shi agaba yay tamai kuka, share glass din yayi tass amma dudda haka motar nan dole sai taje car wash yakoma ciki ya zauna tareda tada motan yafara tafiya ahankali, agaban wani masallaci yay parkin suka fito sukai salla sanan suka koma mota yatada motar yana kallon hanya batare daya kalli fuskar Aliyun ba yace "if you want to win a woman's heart Leo dole ka sauke mata kai, allow her ta tattakaka yanda takeso tawuce tadawo if possible ma ta zubar da shara akanka, ance duk sarautan sarki a wajen matar shi bawa yake dawowa, I believe you know this girl (Aneesa) morethan I do, I just saw her yau harna gane who she is, kaiko nasan this is not d first time daka fara ganinta u understand who she is and yet kana mata zuciya da zafi agabanta, no no no that's very wrong, I understand how you feel seeing wacce kakeso tareda wani but you have to calm down and act maturely, yarinyar nan barkono ce and ta hanya daya ake winning zuciyan mata irinta" yay maganan tareda dan satan kallon Aliyun ganin yanda ya natsu yana kallonshi yasa yay dan murmushi yace "zan baka misali guda daya, ka dauka anyi serving nnaka abinci dake da yaji sosai abincin yaji barkono, harshen ka da bakinka da labban ka duk suka haukace sabida yaji by the time dazaka dauko sweet kabude daga leda ka jefa abakin kafara tsotsa just give yajin a minute or so zakaga dadin sweet din ya rinjayi yajin tun kanajin yajin har saiyazo yabace all you could feel is sweetness of your sweet, so just be like a Sweet towards this girl and trust me you will win her over, be sweet, be gentle, don't hit it hard take it slow one step at a time, forget baaba zata shigo hannu ne tsaf fine boy like you, Dady's Boy fa for that matter" dan murmushi yayi hakan ba karamin dadi yama Abdul ba daman yay hakane dan yasashi murmushi saikuma yayi fuzar da iska yyi yace "let's go home wlh yunwa nakeji".

Ganin babu Ammi a tsakar gida yasa tasauke ajiyan zuciya alwala ta dauro da sauri tawuce ta shiga dakinsu daidai Ammi ta sallame salla tace "hayaniyan menake taji awaje?" rasa me zatace tayi da kyar bakinta yasamo magana tasoma hadawa tace "wasu yara ke fada shine Yusuf yaraba su, yama tafi dama basu ganni bane shine yanemi gidanmu yazo yaji lafiya" charbi Ammi ta dauka tace "ayya, angode to, zokiyi salla kici abinci kisha maganin dare" hawa man dadduman tayi ta kabbarta salla Ammi kuma ta tashi tana kawomata abincin dazataci da magungunan ta tana idarwa tazauna tanaci bayan tagama tasha maganin da kyar shima dan Ammi tamata da gaske ne, suna falo har aka kira isha'i sukayi sanan suka cigaba da hira.
Chapter 45 · 0% Book details