← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 133

Sashe 42

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ahankali ya sanya hanunshi dasuka dan baci da paint ya janye headphone din kunenshi batare daya waigoba yace "Dad why are you looking at me?" ware ido Dady yayi cikeda mamaki kafin yatashi daga jikin bishiyan yakara so inda Aliyun yake ahankali ya dafa kanshi yace "Son yan zanen ne yau suka tashi, mekake zanawa haka?" Dady yay maganan yana janyo dayan stool din dake gefe ya ijiye ata gaban Aliyun ya zauna yana kallon yanda paint din yabata rigan daya saka. "Aliyu" kallon Dady da sauri yayi yana tsayar da zanen jin yanda yakira shi, ajiye paint brush din yayi acikin cup din ruwan dake kan table yace "Dad, wat is it?" gyara zama Dady yayi yace "I want to talk to you" hannu yasa ya kashe headphone din da waka ke tashi daga ciki Aliyu yayi yace "OK, am listening" dan shiru Dad yayi kaman mai tunani, ahankali yace "aure nakeso zan kara Gadanga na" yay dan shiru yana kallon fuskan Aliyun ganin baiga wani chanji ko wani yanayin tattare dashiba yasa yace "Son kasan bana boyema komi ko, kawai sabida na kasance namijin da banso ina yawan sakin mataye nane bazan ma karya ba da tuni na saki duka mata uku nan danake dasu, basuda mutunci, basu da kirki, ga shegen son abin duniya, they've spoilt all my children Aliyu da yau inda zan fadi namutu yaran wanan ba ruwan su da yaran wanan, cikin dukan ku ku 20 daga kai sai Rauda ne Allah ya tsamo min, am worried Son, how many hours nake samu na zauna agida dazan samu nai uniting yarana, y'ay'ana iyye? Na auro jakunan mata babu abinda suka iya sai koyama yarana bakaken hali da tsanan junan su, mata uku amma banda ta arziki ko daya" yadanyi shiru dan ko kadan baiso yana tunawa da matsalolin gidanshi da hawan jininshi zai iya tashi, ahankali yace "I told you shekaran jiya abinda yasa nai latti was because I helped one woman da yarta batada lafiya na kaisu asibiti ne ko" gyadamai kai Aliyu yayi alamun eh, cigaba da magana Dady yayi yace "Aliyu when I saw how caring and loving that woman is towards her daughter I immediately saw myself in her, na yaba da natsuwan matar, sanan na yaba da tarbiyan data bama yarta, she's good, she's educated duka fanin boko da islamiya ahaka banma riga na tambayeta duka abubuwan data saniba tukunna, Ustaziya, kamilan mace, da natsuwa da kamala, ga fikra, all this abubuwan duniyan nan basu dameta ba, sosai naji ina sonta, nama yan uwan ta magana sufada mata tace ta yarda, dazaran an sallami yarinyar daga asibiti nakeso a daura auren, I don't wanna do anything dazai batama rai I need your support Gadanga na, should I go ahead and marry her?" dan shiru Aliyu yayi yana kallon mahaifin nashi deep down ya tsani yanda Dad ke aure but wani zubin baya blaming nashi danko shi kanshi baiga mata tagari acikin matayen ba, he just hope wanan will give his Dad the peace din dayake nema da kwanciyan hankali tunda dai yaga tsantsan son da Dady ke mata a idanunshi, dan murmushi dake karamai kyau yasakin ma Dady yace "marry her Dad, Allah sanya alheri" ajiyan zuciya Dady ya sauke tareda lumshe ido jiyayi duk wani nauyi da zuciyan shi yamai ya sauka baiso yay auren Aliyu bai yardaba saigashi ya yarda, cikeda tsananin farin ciki yace "thank you Gadanga na, zan kira Momman ka tahada min akwati, kaje gidan kuwa tunda kazo?" yatsine fuska yayi tareda girgiza kai, dan batarai Dady yayi yace "kabar zanen nan kawuce ka shirya, bodyguards dinka su kaika kanajina ko" ahankali yace "to" tashi Dady yayi yace "zan kira a gyara the flat that is next to mine, bari naje office" "bye Dady" "bye Gadanga" fita Dady yayi Aliyu yay shiru yarasa mekemai dadi aduniyan nan mugun so yake yaje asibitin but baiso yahadu da Ammi, Abdul yafado mai arai hakan yasa da sauri yatashi yay part dinshi wanka yashiga yafito ya shirya cikin wata hadaddiyar shadda yaja mota ko inda bodyguards din da Dady yace subishi baiyiba yafice abinshi.

Wuraren 3 na rana Dr ya shigo dakin rikeda leda dake cikeda magunguna yana kallon Aneesan data tashi zaune ta jingina da gado tana shan tea da Ammi tahada mata Baffa na zaune kusada ita rikeda plate da soyayyan kwai kekai tanaci, tarame sosai, raman saiya kara karamata kyau, lips dinta sukai pink suka tattare sosai bana wasaba, baki Dr yarike yace "iyye patient dina da bata son allura ne takecin dadi haka, mesa akabata? " dan murmushi Aneesan tayi akunyace, Baffa yace "yo kaiko bazaka barmin diya taci dadi ba, kukenan saiso kuna chakama mutum karfe daku za'a chakamawa da ansha kallo kuka wiwi zaku dinga yi fa balle yar diyata yar karaman nan" dariya duk akayi adakin Dr yakara so yana duba Aneesan ya bama Ammi ledan magungunan yace "an sallame ku, ga magungunan ta na narubu tamuku yanda zata dinga sha, ki kula da ita da kyau sanan a kiyaye kar sauro yacijeta sanan ta dinga shan maganin ta akai akai, kina yawan bata abinci mai Gina jiki, nariga na sanar da Alhaji nasallameku yama turo mota dazai maidaku gida motan na waje ku shirya sai a fitar da kaya" ya kalli Aneesa dake wasa da tea yace "Allah kara sauki my patient banda rashin ji da tsoron magani kinji ko" gyadamai kai Aneesa tayi tana murmushi ahankali Dr yawuce yafita, kayan su da dama a killace suke tsaf Ammi ta shiga gyarawa, shanye tea Aneesa tayi Ammi ta karba ta gyara komi Baffa ya karbi hijabin Aneesan daga hannun Ammi yasamata sanan yadaga ta tashi tayi ahankali yace "sannu kinji, sa takalmi" takalmi tasaka yana rikeda hannun ta suka fito shikuma Na Sani ya tsaya yataya Ammi kwashe kayan suka fito, da Ammi da Aneesa ne suka shiga jeep din da Dady ya aiko musu da shi sukuma su Baffa suka shiga tasu motar suka tafi gida sukai Suleja.
Chapter 42 · 0% Book details