← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 62

Sashe 61

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yinin Ranar jinsa yayi sakaka gaba É—aya bayada wani kuzari tunanin Aimanah gaba É—aya ya cika masa zuciya addu'a yake Allah ya mallaka masa ita, washe gari jirgin karfe shida na safe yabi zuwa kano, hotal ya kama ya zauna yaÉ—an warware gajiya yai barci wajan goman safiya yatashi yai shiri cikin dakakkiyar shadda blue É—inkin ta zarce ya kafa hula zanna bukar yai matukar kyau bakin takalmi yasa mai matukar kyau wanda suka matukar dacewa da shaddar dake jikinsa, fitowa yayi wajan hotal É—in yana tsayawa mota ta faka a gabansa
"Yasar Mahmud Ahmad" wanda ke tuka motar yafaÉ—a, kai kurum Yasar ya gyaÉ—a alamar e ya shiga motar da driver É—in ya buÉ—e masa mirfin motar ya zauna nan kusada mai tuka motar, ahankali da nutsuwa driver É—in ke bin location har suka karasa gidan su Aimanah, yana sauka a kofar gidan ya kira wayar Aimanah mintina kaÉ—an ta fito inda yake tsaye yana murmushi
"Barka da zuwa kano ya Ustaz" Aimanah tafaÉ—a tana kallon Yasar da ke tsaye kikam yana binta da kallo, Nesa da su kaÉ—an Abbas ya faka motar sa ya kifa kansa saman sitiyarin motar yana sakin numfashi da sauri sauri, É—agowa ya kuma yi yana kallon Aimanah da wani daban ta zage sai dariya take masa, da mugun gudu yatashi motar yai ribas yabar layin batare da yayi abinda yakawo sa ba, Aimanah jerawa sukai zuwa ciki itada Yasar suna magana, har ciki suka shiga tare gaisawa sukai da Mah cikin girmamawa Hanne ta kawo masa ruwa da lemu ta gaidasa ta fita, Azinatu ta fito daga É—aki tana murnar ganin Yasar, kama baki Yasar yayi cikeda mamaki
"Baku tafi ba daman, ai na zaci kun É—au hanya"
"Bamu tafi ba, Mah ta hanamu tafiya sai gobe mu tsaya mu gaisa da Daddyn su Aimanah yau zai dawo daga saudiya" gyaÉ—a kai yayi kana ya ce
"Ina mom É—in to?"
"Sun fita itada Ya Muhd da Ma'aruf" shuru Yasar yayi har sanda Aimanah ta ajje masa plate ɗin dake shaƙe da kayan snack
"Jazakallahu khair" Yasar yafaÉ—a yana kallon fuskar Aimanah, murmushi Aimanah tayi ta zauna kujera dake kallon wacce yake kai, Samosa É—aya ya É—auka yai bisimillah yakai bakinsa, lumshe idanu yayi sakamakon wani musulmin daÉ—i daya ji daga samosan buÉ—e idanunsa yayi kan Aimanah
"Masha Allah Samosan nan yayi daÉ—i sosai, idan munyi aure kullum shi zakina bani ina ci haÉ—eda shayi a birnin madina" dariya Aimanah da Azinatu sukayi a lokaci É—aya, Yasar kuwa sake ware idanuwa yayi yana kallonsu yanda suke dariya
"Wai da nayi magana mai nace ne naga kuna dariya haka" dariyar suka kuma yi Azinatu harda rike ciki tana gangarowa daga saman kujera zuwa kasan carfet
"Yaya Aimanah Allah kisawa Yaya Yasar waigi karfa ya faÉ—i" Yasar bai sake bin takansu ba har sai da yaji ya koshi, kana ya kalli Aimanah
"Kurratu ain kuna da leda na saka sauran snack É—in nan na tafi da su"
"Kai Yaya Yasar karfa kayi abin kunya a gidan surukai"
"Au haka ne fa, Azinatu bari na kama kaina" Aimanah murmushi kawai take tana kallon Yasar wanda shima ita yake kallon, ganin kallon da suke yasa Azinatu ta mike ta basu waje su zanta
"Ina yarana" Yasar ya tambayi Aimanah
"Nima tunda nazo ban saka su a idanuna ba" Aimanah ta basa amsa cikin yanayin damuwa, har sannan kallonta yake yana nazarta fuskarta
"Ba'a nan garin babansu yake ba, ko suna can wajansa a Abuja"
"Suna nan garin wajan Ammi,"
"Ammi ba ita bace mamanki"
"Kakar yaran ce, kanwar Mamana" numfashi Yasar ya fesar kana ya kwantar da kansa saman kujera bayan wani lokaci ya É—ago yana kallon Aimanah wacce ke wasa da zoban dake hannunta
"Wai kina nufin auran zumunchi kuka yi da tsohon mijin naki" kai Aimanah ta gyaÉ—a masa
"Wayyo ni" Yasar yafaɗa yana sake maida kansa saman kujera, Rumana ce ta fito daga ɗakin Mah kunnanta kange da waya da alama waya take da Abbas, dai dai sanda ta karaso inda suke ta katse kiran, kallon Yasar tayi ta kuma maida kallonta ga Aimanah ta taɓe baki ta juya zata koma inda ta fito
"Kizo ku gaisa Rumana, Yasar ne yanzu yazo daga Abuja"
"Ina kwana" Rumana ta faÉ—a daga inda take taci gaba da tafiya batare da ta jira cewar sa ba
"Kanwarki ce? muryarku iri É—aya haka ma tafiyarku"
"E! kanwata ce" Aimanah ta basa amsa
Da gudu yaran suka shigo suna kwaÉ—a kiran
"Amma, Amma" mikewa tsaye Aimanah tayi fuskarta shimfiÉ—e da Murmishi ta buÉ—e hannayanta suka shiga ta rungume su tana sumbatarsu
"Aslam Tasnim ina Islam"
"Tana tareda Abie yanzu zasu shigo ya tsaye kulle mota ne", Aslam yabata amsa, Tasnim bai yi magana ba sai kara riketa da yake yana sauke ajjiyar zuciya,
"Tasnim baka canza ba, kana nan da shurunka"
"Amma ina kika tafi kika barmu, muyita kuka Ammi tace school kika je sai kin daÉ—e zaki dawo" Aslam ya tambayi Aimanah, kafin ta basa amsa ta ga shigowar Mustapha hannunsa rike da Islam dake tafiya a hankali, gaban Aimanah ya buga lokacin da idaninta suka shiga cikin na Mustapha, Musty daya kafe ta da idanunsa tunda ya shigo harya karaso inda take, Islam da gudu ta faÉ—a kan Aimanah tana faÉ—in
"Amma daman da gaske Ammi take zaki dawo, Amma karki kuma tafiya ki barmu muna sonki ko Aslam" Islam ta faÉ—a tana kallon Aslam da baice komai ba yana jikin Aimana da jikinta ya É—auki rawa musamman da Mustapha ya zauna a kujerar da ta ke kai,tana jiyo sanda suke gaisawa da Yasar
"Aimah tunda bazaki gaida ni ba ni bari na gaida ki ina kwana" kasa magana tayi sai ma mikewa da tayi zata bar wajan, hannunta ya riko cikin hannunsa ta tsaya cak, a zafafe ta ce
"Yayanmu shika min hannu"
"Bazan shika ba, inace hannun matata na rike"
"Matarka a ina na zama matarka ada ne zaka iya kirana da wannan sunan na amsa ba yanzu ba daka datse igiyar auranmu guda É—aya"
"Aimah dan Allah dan Allah ki tsaya muyi magana ta fahimta"
"Bakada wannan sauran lokacin a wajena Mustapha, babu sauran wasu kalamai da suka rage da zaka iya gaya min ka barni, ka fita a rayuwata dan Allah" ta faÉ—a cikin Kuka, mikewa yayi daga zaunan da yake yai taku biyu zuwa inda take ya tsaya a gabanta har sannan hannunta na cikin nasa
"ÆŠago idanu ki kalle ni Aimanah, kisa idonki cikin nawa ki gaya min bana sonka Mustapha ni kuma na maki alkawarin daga ranar bazaki sake ganin mai kama dani ba, zan nesance ki nisan da bazamu kuma haÉ—uwa ba har abada" hannunta ta fisfe daga cikin nasa da gudu ta shige É—akinta ta kwanta kan gado tana kuka sosai, yaran bayanta suka biyo ganin tana kuka suka fito suka shiga É—akin Mah

SUMAYYA
Chapter 61 · 0% Book details