← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 62

Sashe 15

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau tun safe Abas ya kira Aimanah yana hanyar dawowa daga jigawa zai zo su gaisa a hanya yake zai koma Abuja, Cus cus ta dafa masa wanda yaji kayan lambu da zallar tsokar naman sa, sai jus na kwa kwa data haÉ—a masa wanda yai sanyi sosai komai ta kai falon Daddy inda yake saukar bakinsa ta ajje sannan ta shiga wanka, sosai tayi kwalliya ta haÉ—e cikin shuwariski lace É—inkin street gwon wacce tabi jikinta kamar a jikinta telan ya haÉ—a kayan babban mayafi tasa sanda ya kirata a waya ya ce gashi a waje
"To ka shigo" ta faɗa a shagwaɓe
"Uhmm uhmm kizo dai ki shigo dani" kashe wayan tayi ta gayawa Mah Abas yazo, tana fita compound yana shigowa gidan tsayawa tayi cak a inda take harya karaso wajan
"Barka da rana sarauniyata"
"Barka dai sarki mai mulkin zuciyar sarauniya" dariya sukayi alokaci daya suna kafe junansu da kallo, sun jima suna kallon juna irin kallon nan da bahaushe ke kira da kallon kuda, Aimanah ita tafara janye idanunta tayi gaba tana faÉ—in
"Kashigo ku gaisa da Mahh" bayanta yabi suka gaisa da Mah sanan Aimanah ta masa jagora zuwa falon bakin Daddy, abincinta zuba masa kinci yayi dole saita basa da kanta
"Allah Kalbie bazan baka ba wancan karan ma saboda hannunka na baka yanzu kuwa alhamdulillah hannu ya warke, kariga da kasan haramcin hakan" hannu yasa yaɗau cokalin yafara cin cuscus ɗin bayan yayi bisimillah sai santi yake mata tareda zuba mata surutu harya cinye bai sani ba😂saida yakai spoon bakinsa yaji ba komai ya kalli plate ɗin gabansa, atare suka kwashe da dariya, sun jima suna hira kafin ya mike zai tafi tayi masa rakiya har wajan gidansu inda yafaka motarsa, wata haɗaɗɗiyar mota ce ta faka a kusa data Abas ma mallakin motar ya fito, gaban Aimanah ya faɗi ta kafe wanda ya fito daga motar da kallo ganin yanda ya wani rame, Abas dake magana ya lura hankalin Aimanah baya garesa ya kalli inda take kallo da sauri yadawo da ganinsa ga Aimanah yaga dai har sannan gayan take kallon gyaran murya Abas yayi wanda yasa Aimanah saurin juyowa ta kalli Abas tana kokarin saita kanta ya watso mata tambayya
"Wane wannan É—in" Aimanah tayi kasa da kanta jikinta na rawa ta kasa kallon Abas
"Kiyi magana mana kinmin shiru, ok na fahimta masoyinki ne Al'mustapha.....?

*Saura kiris adaina fitar da littafin Aimanah za'a daina posting É—insa a ko wanne group sai group na Aimanah real fans group 1 and 2 Idan har kinsan kina son cigaba da karanta Aimanah kuma kinsan zakiyi comment maza yi save É—in wannan number 07039793439 da Mamin Humaidah kiyi mata magana ta whatssapp zatayi adding naki a group É—in dazaki karanta hankalinki kwance batare da ko sisinki ba*
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na goma sha uku*

*Wannan page É—in gaba É—ayansa sadaukarwa ne ga masoya Book na Aimanah Musamman Æ´an Aimanah Real fans group two*

Aimanah takasa cewa komai haka ta kasa haÉ—a idanu da Abas batayi aune ba taga harya shiga mota yana kokarin tada motansa, da sauri ta buÉ—e front seat ta zauna batare data rufe murfin motar ba
"Fita fitarmin a mota Aimanah" É—agowa tayi tana kallon Abas dayake fitar da huci kamar wanda yayi dambe, tuni idanunta suka soma zubda hawaye
"Haba Kalbie shikenan daga na kalli wani waje sai kace wani nake kalla, abar shi ma wani nake kalla shine mai, nidai nasan kaine nake so ba wani ba, kada kallon wani ya ɓata mana wannan lokacin, kai nakeso kaine a zuciyata, bazan taɓa kallan wani kallo irin na soyayya bayan kai ba, Abas kanada matsayi mai girma a zuciyata taya zan iya kallon wani kallon soyayya bayan kana kusa dani?"
"Aimanah ki fitarmin a mota" yafaɗa a zafafe, Aimanah rufo mirfin motar tayi ta gyara zamanta cikin motar tana kallon cikin idanunsa wanda bata hango komai ciki sai zallar rigima da ɓacin rai
"Abas ni kake kora a motarka"
"Na korekin kije kici gaba da kallon masoyinki gashi can ya shiga gidanku"
"Shikenan" Aimanah tafaɗa ranta ɓace, kokarin buɗe murfin motar tayi amma yaki buɗuwa ta lura ansawa motar scurity,
"Ka buÉ—e na fita" hannunsa yasa saman hannunta, lokacin da hannunsa ya haÉ—u da nata taji wani Æ´ar a gaba É—aya jikinta
"Aimanah yanzu saiki iya tafiya ki barni a wannan yanayin?"
"To yaya zanyi dakai Abas na gaya maka gaskiyya kaki fahimta, ka buÉ—e min na fita"
"Hayatie zuciyata tana maki wani irin mahaukacin so wanda ni kaina bazan iya misalta maki kalar saba na riga na faÉ—a irin sosai É—in nan, zuciyata tayi wata irin bugawa a sanda naga kina kallon wani bayan gani a tsaye gabanki, shiyasa nan take zuciyar tawa ta bani Mustapha ne, ina da kishi sosai akan abinda nakeso ki kiyaye karki sake kallon wani namiji inhar muna tare"
"Bazan sake ba Hayatie kaine rayuwata gaba ɗaya, bazan sake ɓata ran masoyi naba wanda ya wanke duk kan wata damuwa a zuciyata, Hayatie ina tsananin so da kaunarka kaunar danake maka takai matakin da bana iya kallon ko wanne ɗa namiji, Kasani a raina kai nasa ba wanda nake gani, ko ruwa na ɗeba ciki zan sha kai nake ganowa, kaine mahaɗin rayuwar da duk zanyi kasan sai da kai, hannunsa dake cikin nata ya damke sosai yana kallon idanunta
"Muyi alkawari Hayatie duk runtse duk wuya É—ayanmu bazai rabu da É—ayansa ba"
"I promise"
"Yes Hayatie I promise" hannu suka haÉ—a tareda jinjinawa, ta zare hannunta a hankali daga nasa
"Idan katafi yau sai yaushe?"
"Sai ranar É—aurin auranmu"
"Haba dai dafa saura dayawa"
"Sati uku yayi saura ai, bazan ma iya ba abaya ma bana sati banzo kano ba bare yanzu da naga ana neman yi min fin karfi"
"Ka kwantar da hankalinka ba wanda zai iya kwace maka ni"
"Na kwantar irin kamar kayi bako ya mutum É—in nan" dariya suka yi sosai kafin Aimanah ta fito da wayarta taÉ—an masa kusa da shi kaÉ—an ta masu picture, guda É—aya tayi masu ta sake saita wayan tana kallonsa
"Captein smile" murmu sawa yayi ta masu hoto ta maida wayanta kan cinyarta
"Amma zaka halarci dinner É—in Uncle Yunus"
"Bazan zo ko wanne event ba amma zanzo wajan É—aurin aure"
"Shikenan ka sauka lafiya" tafaÉ—a bayan ta buÉ—e door na motar ta fita tana É—aga masa hannu harya yice daga layin.

Aimanah sanda ta shiga gida Al'Mustapha ta tarar tareda Mah tana duba lesika da alama shiya zo mata da su, Aimanah Mah kawai tayiwa sannu da gida ta wuce tana gafda shiga É—akinta Mah ta mata magana
"Zo nan Ummu Aimanah" dawowa Aimanan tayi ta zauna kasan carfet gaban kujerar da Mah ke zaune
"Mah gani" Mah bata kulata ba taci gaba da duba lesukan gabanta can tayi magana
"Sunyi kyau Al'Mustapha, tagaya maka kuÉ—insu" Al'Mustapha ya shafi kansa kana ya ce
"Mah na biya kuÉ—in gaba É—aya harna Anty Hasanah"
"Masha Allah Musty muna godiya Allah yakara arziki mai albarka ya cika buri"
"Ameen ameen" Mustapha yafaÉ—a yana kallon Aimanah, Mah kallon Aimanah tayi kana ta maida ganinta ga Al'Mustapha
"Wai banga kun gaisa ba, ince dai ba gaba kuke ba" Aimanah ɓata fuska tayi tareda kautar da kanta can gefe batace komai ba
"Mah Aimanah ta daina kulani rannan dana zo ma kofa ta rufe ta hanani shigowa"
"Aimanah mai kenan gaba kike da shi"
"Mom ni..." kuka ne kawai ya kwace mata ta mike da gudu ta shige É—akinta, shiru Mustapha yayi, har can cikin ransa yakejin kukan nan na Aimanah, Allah Allah yake Mah ta tashi a wajan ya shiga É—akin Aimanah kamar kuwa Mah tasani ta mike ta faÉ—in
"Mustapha bari na adana kayan nan a ɗaki nasan Hasana tana gafda zuwa gidan nan tun safe ma nake saka ran zuwanta kilama gajiya ce ta hanata fitowa ta sha zaman jirgi" Mustapha baice komai ba yabi Mah da kallo harta shiga bedroom ɗinta, yana ganin shigarta kamar wani ɓarawo ya yi wuf ya shige ɗakin Aimanah, kwance ya sameta saman bed tana ta faman kuka kamar ranta zai fita, tsayawa yayi kofar ɗakin yana kallonta har kasan ransa yake jin kukan nan nata, harya shigo ɗakin ya zauna gefan gadon bata sani ba tana faman kuka kukan daya rasa na menene
"Aimaah daina kukan nan please na gaya maki bana son kukanki" da sauri ta ɗago tana kallon sa batace masa komai ba ta maida kanta taci gaba da kukanta, saman gadon ya hau sosai ya zauna harya saka hannu zai taɓata ya tina haramcin hakan da sauri ya mike ya sauka daga gadon, saboda wani abu daban da zuciyarsa ta ɗarsa masa
"A'uzubillah" yafaÉ—a a hankali yana kokarin fita daga É—akin sai dai kuma yakasa fita É—in saboda yanda yakejin zuciyarsa ya tsaya baki kofa
"Aimahh dan Allah ki daina kukan nan na roke ki, ki tsaya muyi magana naji ya yarda yanzu bakya sona ai ko ba soyayya daman can ni É—an uwanki ne"
"Ni kafita bana son ganinka" bai sake tsayawa yace komai ba yasa kai ya fita yayi sa'a Mah bata falon hakan yabasa damar fita daga gidan gaba É—aya, tun daga wannan ranar Aimanah bata sake saka sa a idanunta ba har aka fara bikin Uncle Yunus, Uncle Yunus kanin su Mahh ne babansa wan babansu ma ne, a gidansu yata shi wajan Ana, ana ita ta rikesa bayan rayuwar iyayansa sanadin haÉ—arin mota tun yana É—an shekara goma sha biyu.
Chapter 15 · 0% Book details