← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 62

Sashe 50

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AIMANAH
Islam taji sauki sosai ta murmure, bayan tasha allurai da magunguna yau Aimanah tun safe take aikin bauta sai É—orawa da saukewa take na kawayan Sumayya da suka cika gidan ko wacce kuma da kalar abinda zata ce ayi mata, Lina duk wani motsin Aimanah idanunta na kai har zuwa yanzu da Aimanah ta kawo masu soyayyar taliyar data gama yanzu
"Kai nifa bazanci taliyar nan ba, inaga ko indomie za'a dafa min" feenah ta faÉ—i haka tana kallon Aimanah wacce sam bata iya ko yi masu musu duk abinda suka ce aiwatarwa kawai take
"Ba wani indomie da zata dafa maki in bazaki ci wannan ba ki bar shi" Lina tafaÉ—a a zafafe, feena wani kallo ta mata ta É—auke kai tana murmushi
"Ke Aimanah jeki ki huta kuma ki É—ebi yanda zai isheki keda yaran" juyuwa Aimanah tayi ta koma kicin É—in
"Gaskiyya kawarmu abinda kikewa kishiyarki yayi yawa tunda kin riga kin farraka tsakaninta da mijinki ki barta mana ta huta gara ma kisa ya rubuta mata takardar saki ta bar maki gidanki ki huta"
"Gane min hanya dai Faty da sanda muka tallata mata abin nan kamar ta kirki sai da muka sha fama ta amince mukaje enugu amma yanzu harta zarta mu wajan mugunta"
"Sumy dan Allah ki maido da yarinyar nan wajan nan canfa ba daÉ—i kinsan yanda wajan nan yake ga yara" ca É—in da kawayan Sumy sukai mata shiyasa ta sa Aimanah ta dawo É—akinta itada yaranta, Lina har É—aki tabi Aimanah ta taya ta gyara É—akin

"Ammi karfe biyu na rana ta shigo Abuja, Abas yaje ya ɗakkota, Rumana tana ganin Ammi da Abbas tasha jinin jikinta musamman irin kallo da taga Ammin na mata ko zama batayi ba tafar aikawa Rumana faɗa Ammi ba baya ba wajan faɗa da musamman inka ɓata mata rai, Rumana jikinta yayi sanyi da faɗan da Ammi ta mata sai sannan taga wautarta shekarunsu huɗu da aure sanan ta haihu yanzu kuma ga wata kyautar daga Allah cikin kan kanin lokaci amma tana neman bin hudubar sheɗan ta butulce ma Allah, tana kuka sosai tabawa Ammi hakuri sannan ta nemi Abbas daya yafe mata, da kyar ta lallashi Ammi ta zauna taci abinci ta umarci Abbas daya kaita gidan Aimanah su gaisa ba zama zatayi ba jirgin karfe huɗu zata bi ta koma kano,
Aimanah na tsaye tana mooping anan falo aka turo kofa aka shigo, tsallan murna tayi tana É—ane Ammi gaba É—aya yaran sukayo kanta suna ihun ganin Ammi, Ammi zama tayi kan kujera tana kafe Aimanah da idanu ko gaisuwar da Aimanah take mata bata amsa ba saima tambayya data aikawa Aimanah
"Aimanah lafiyarki kalau kuwa naga kunyi rama gaba ɗayanku keda yaran?" murmushin yake tayi batace komai ba tai kasa da idanunta hawaye na zubo mata ta buɗi baki zata gayawa Ammi halin da suke ciki amma ta kasa bakinta ya mata nauyi maimakon ta faɗi abinda ke cikin zuciyarta sai taji bakinta ya furta saɓanin abinda ke zuciyarta ahankali ta ce
"Ammi muna lafiya kalau, munyi fama da zazzaɓi ne gaba ɗayanmu musamman Islam" Ammi dake rungume da Islam tana shafa kanta ta ce
"Gidan shuru Sumayya bata nan? daman nasan Mustapha yanzu yana office jiya ya kirani mun gaisa ya gaya min abubuwa suka masa yawa shiyasa kwana biyu bakuje kano ba" Kai kurum Aimanah ta É—aga zuciyarta fal zulumi da tunani yanda zatayi da Ammi tun jiya da yamma Mustapha da Sumayya suka fita basu dawo ba sumayya ta kulle store suma Maman Hanif ke aiko masu da abinci, mikewa tayi ta shiga É—akinta jiki na rawa ta kira Maman Hanif ta gaya mata Ammi tazo,
"Gani nan zuwa" maman hanif tace Aimanah ta fito falo wajan Ammi da suke magana da yaran, Maman Hanif ta shigo da katon hijab É—inta fuskarta da murmushi suka gaisa da Ammi, Ammin na tambayarta yara
"Maman Aslam baki kawo wa Ammi abinci ba"
"Nama manta gaba É—aya É—okin ganinta ya mantar dani ana kawowa bako abinci da ruwa"
"Bari to nashiga kicin É—in na É—ora mata ko macaroni ne"
"A'a Maman Hanif bazan ci komai ba adai kawo min lemu da ruwa amma na koshi da abincin nan naci gidan Rumana" maman Hanif ta shiga kicin mintina kaÉ—an ta fito hannunta É—auke da plate mai É—auke da goran ruwa dana lemu, lumshe idanu Aimanah tayi tana jin wani sanyi a zuciyarta
"Ammi gashi, kinga Aimanah duk ta rame jinya tayi sosai har kwana biyu mukayi a hospital Musty ya hana a sanar maku kada hankalinku yata shi" Ammi na murmushi ta ce
"Allah ya kara lafiya" har sannan idanunta nakan Aimanah kamar mai irga kashin wuyan ta, mamaki matuka take na ramar da Aimanah tayi tabbas yazama dole ta bincika mai ya saka Aimanah haka wannan rama ko kusa ko alama bata yarda Aimanah jinya tayi ba, tadaifi zaton akwai abinda Aimanah da Maman Hanif suke ɓoye mata, bata wani jima can ba sanin Abas na waje yana jiranta yasa ta mike
"Zan tafi Aimanah idan abokiyat zamanki tazo ki gaidata da mai gidan" har bakin get Aimanah ta mata rakiya
"Aimanah ga Abbas can ki fito ku gaisa" Aimanah nasa kafarta a bakin kofa taji kamar wacce aka saka mata shoking na nepa da sauri tayi baya har tana shirin faÉ—uwa
"Subhanallah sannu bi ahankali Aimanah" Ammi tafaÉ—a cikin kulawa
"Ammi ki gaida gida bazan iya zuwa mu gaisa da Abbas ba" da sauri ta juya zuwa ciki sabida har sannan bataji jikinta ya koma dai dai ba, saman kujera ta zauna jikinta na rawa sosai ji take ana sake ɗaure mata jiki wata kara ta saki bata sake sanin inda kanta yake ba....✍🏻
[2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da uku*

Sumayya dake tsugunne gaban malam, baya tayi zata faÉ—i ganin Aimanah ta bayyana a gabanta gata nan muraran kwance kan kujera kamar mai rai kamar mara numfashi, ga Maman Hanif nan a gefanta tana faman mata fifita,
"Ran Malam yadaÉ—e ban gane ba, kar dai kace min ta mutu?" Sumayya ta tambaya hankali tashe
"Hhhhhhhhhhhhh, bata mutu ba, saura kiris saura kiris aikinki ya tarwatse yau, wacece wannan?" malam yafaÉ—a yana nuna mata wani kasko dake gabansa Ammi ce ta bayyana zaune cikin jirgi,
"Su ru ka ta ce" Sumayya ta faÉ—a a rarrabe, Ammi gyara zamanta tayi cikin jirgin tareda É—ago da hannunta ta fara tasbihi, wani feshin wuta ne yata shi daya kusa kama fuskar Sumayya data kurawa Ammi idanu
"Zata ɓata mana aiki wannan matar tanada karfin ibada bata inda zamu ci galaba a kanta, tabar gidanki da kudurin binciko abinda yasa kishiyarki da yaranta rama ko mai zai iya tarwatsewa aduk randa ta sake shigowa gidanki"
"Malam ayi wani abin dan Alah, bana so na rasa wannan damar so nake na rayu a haka har karshan numfashi na"
"Wiiiiihuuuuuuuhuuuuuu, zamuyi zamuyi zamuyiiiiiiii" yafaÉ—a da wani irin ihun dayasa Sumayya yin baya sosai da shi
"Nasa Aljani dundurusu yayi komai, zaki biya mu kuÉ—in aikin mu sannan aljani É—an jani zai biya bukatarsa da ke," zaro idanu Sumayya tayi tsoro yasake mamaye zuciyarta aljani kuma yanzu aljani ne zai biya bukatarsa da ita, bata gama tunanin ba taji kamar ana shafarta bata sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa tayi ta ganta kwance a É—akinta, wani tsalle ta buga tareda sakin ihu, dai dai nan Aimanah ta saki wani numfashi Maman Hanif ta ce
"Alhamdulillah Allah mun gode maka, sannu Aimanah"
"Yawwa" Aimanah tace a sanyaye, gaba É—ayansu tsorata sukayi sanda sukaga Sumayya da rabonta da gidan tun jiya fitowa tayi daga É—akinta, cikeda mamaki Maman Hanif ke kallon Sumayya ita dai tana nan falon tun sanda Aimanah ta suma bata bar falon ba bare ta ce anan Sumayya ta shigo amma abin mamaki sai gata daga É—akinta, mintina kaÉ—an kuma sai ga shigowar motar Mustapha
"Sannu maman Aslam ya kike jin jikin"
"Da sauki sai dai kaina ji nake kamar ba nawa ba"
"Sannu shima zai daina kici gaba da ambaton Allah" sallama Maman Hanif taiwa Aimanah ta fita, Aimanah ma É—akinta ta shiga sai dai ko zama batayi ba sai ga Sumayya a É—akin, tsaye tayi jikin kofa tana girgiza jiki
"Kizo ki wankewa Mijina mota" haka kawai tafaɗa ta fita daga ɗakin, jikin Aimanah yana rawa tabi bayan ta sabida wani tsananin tsoronta da ta ji ya kara shigarta fiye dana da, motar tayi datti sosai jikin tayar motar futu futu da jar kasar da alama motar wajan gari akaje da ita, tanayi tana haki ga sanyin ruwa haka ta gama abinda bata taɓa yi ba, tanayi tana goge hawayen takaici, Sumayya na gefe ta kafa kujera tana kallon Aimanah tana mata dariya da wake waken habaici,
Aimanah data koma dakinta kuka ta sha sosai daran ranar batai barci ba raya daran tayi da nafiloli tana kuka tana gayawa Allah halin datake ciki, washe gari sarai ta tashi zuciyarta fes har wani nishaɗi take ji, kasancewar da azumin nafila ranar ta ta shi, abincin da Maman Hanif ta aiko masu da shi gaba ɗaya taba yaran suka cinye duka matukar tausayin yaran take zuwa yanzu yaci ace suna aji suna ɗaukar darasi amma ga yanda rayuwa tayi da su hakan yasa ta bada kaimi wajan addu'ar Allah yafitar da ita daga wannan hali datake ciki, wayar hannunta ma Sumayya ta karɓe ta a gabanta ta bugata da kasa sabida kawai ta ganta suna waya da maman hanif.
Chapter 50 · 0% Book details