← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 62

Sashe 58

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

SUMAYYA
Murmushi take ta dokawa sanda Dr ya basu sakamako tanada ciki na wata huÉ—u wanda ita batayi zato ko tsammani ba
"Mustapha kaga kyautar da Allah ya mana" Musty baice komai ba, saima kallo dayabi Sumayya da shi ita da Dr suka gama maganganunsu suka taho gida bakin Sumayya yaki rufuwa sabifa murna, suna shiga gida Sumayya taga Lina da feenah a zaune cikin falon, turus tayi taja ta tsaya bakin kofa kamar bazata shigo ba sai kuma dai ta shigo ciki tana binsu da kallo
"Lafiya naganku yanzu ba sanarwa zaku zo"
"Da in zamu zo sanarwa muke ai, Sumayya abinda kika yi kinyi adalci kenan ki ce na tura maki vidio ashe ke da manufa kikai haka, to burinki ya cika mijin Lina yamata saki uku yanda ya saketa ya rabata da yaranta wallahi kema yau sai mijinki ya sake ki kila ma ke har sai an haÉ—a maki da duka, yau zamu nuna maki mu yan asalin hau ne, sai kinga hau yau yasin" Feenah ta faÉ—a tanayin gaba zuwa É—akin Sumayya, Lina tabi bayanta da sauri Sumayya ma ta rufa masu baya, Kayan É—akin suka fara watsi da shi harda kayan sawarta, Sumayya ta shako wuyan Lina ta shake duk yanda Feenah taso ta kwaceta ta kasa hakan yasa ta janyo karfan labule ta bugawa Sumayya zafin azabar daya ziyarci idanunta yasa ta hankaÉ—a Feenah tayi baya sai gata ta faÉ—a kan tukunyar tsafin Sumayya, wani bakin hayaki ne yatashi ya dunkule waje É—aya yai sama ya saki kara da rugugi kamar na hadari, Feena da Lina da gudu suka fice daga É—akin dayake futar da tiriri
"Wayyo Allah na shiga uku ni Sumayya shikenan asiri ya tonu shikenan komai ya karye wayyo ni rayuwata, Feenah kun cuce ni nayi dana sanin saninku a rayuwata kun ruguza min komai" ta zube kan gwiwoyinta tana fashewa da kuka
Mustapha kamar wanda aka tasa daga barci haka ya mike firgigit daga kan gadon dayake kwance ya fito yana sake tina mummunan mafarki da yayi, tun da yafito daga É—aki yake kwaÉ—awa Aimanah kira
"Reina! Aimahh!! Aimah!!! wai ina kika shiga ne, Aslam Tasnim Islam Gwaggo Fulani ku fito mana dan Allah kuna ji ina kwaÉ—a maku kira" turus yaja ya tsaya lokacin daya buÉ—e kofar É—akin Aimanah da yayi kura sosai alamar anjima ba'a amfani da É—akin, da hanzari ya karasa É—akin yara ya buÉ—e nan ma kamar na Aimanah ya haÉ—a uwar kura harma tafi ta É—akin Aimanah, hankalinsa ne ya kuma tashi tuna mafarkin da yayi na wulakancin daya rinka yiwa Aimanah da yaranta bama abinda yafi É—aga masa hankali kamar wai a mafarkin da yayi wai ya saki Aimanah" hankaÉ—a kofar É—akin Sumayya yayi ya shiga, Sumayya idanunsa kawai ta kalla tagano tabbas asirinta fa ya riga ya tonu hakan yasa ta fara ja da baya ta haÉ—a hannuwa waje É—aya alamar roko
"Dan Allah kayi hakuri Mustapha son zuciya ne da bin ruÉ—in kawaye yasa na aikata komai, na tuba na bika bazan sake yin asiri ba dan Allah kaje ka dawo da Aimanah zamu zauna lafiya ba faÉ—a ba gaba wallahi ni zan rinka mata komai zan zama kamar baiwarta nidai fatana kawai ka zauna dani" dafe kansa yayi da yaji yana matukar sara masa ya rike kan da hannunsa yana ambaton Allah
"Wai Sumy mai kike faÉ—a haka, kina nufin ba mafarki nayi ba, abubuwan da duk nagani a zahiri ne da gaske na saki Aimah na saki reina wai" Mustapha yafaÉ—a hankali tashe yana matsowa kusa da Sumayya yayinda ita kuma take yin baya harta dangana da bango
"Ka gafarce ni Mustapha aikin asiri ne" wata shaka Mustapha ya kaiwa wuyan Sumayya yana ihu da faÉ—in
"No wallahi no kar ya ne ni na saki Aimanah ina bazaiyu ba" shake wuyan yayi kamar zai kasheta idanunta suka firfito waje
"Sumayya na sake ki na sake ki na sake ki saki uku" yafaɗa yana yin wurgi da ita ta faɗa gefe tai suman wucin gadi, a guje kamar ta ɓaɓɓe ya fita daga ɗakin yaje ya ɗau wayarsa ya na dannawa Ammi kira

AIMANA
Tsabar kagauta da É—okin ganin ahalinta da gudu ta fita daga motar ko gama tsayawa motar É— batayi ba, da gudu Ammi wacce ke gidan tun safe ta fito tazo ta rungume Aimanah suka fashe da kuka tare
"Sannu Aimanah sannu munyi kewarki munyi kuka na rashin ganinki da tunanin halinda kike ciki"
"Saudah wai maye haka kamar wata karamar yarinya kin wani rungumeta kuna kuka" Mah tafaÉ—a sanda ta fito compound É—in
"Barni nayi kuka Yaya Aysha baki san yanda naji ba barni na koka zuciyata ta sami salama" Mah amsar baki tayi ta masu jagora zuwa ciki kasancewar lokacin sallah yayi ko zama basuyi ba akai alwala Moha yabi Ma'aruf zuwa masallaci matan kuma sukai sallah nan cikin gidan É—akin Mah, sai da akai sallah sannan kuma aka shiga gaisawa duk a zaton Mom Ammi itace mahaifiyar Aimanah shiyasa kusan ita tarinka bawa hakuri kan abinda yafaru, Ammi wayarta ce tayi kara alamar kira na shigowa sai da gabanta yafaÉ—i ganin Mustapha ne ke kira, tayi mamaki matuka dan rabon data ga kira irin haka tana tunanin tun kan rabuwarsa da Aimanah hakan yasa ta fita daga falon
"Hello Ammi ki yafemin dan Allah ina Matata da yarana"
"Masha Allah, Allah abin godiya Mustapha kaine da gaske"
"Ammi da gaske nine ina matata da yarana"
"Aimanah gata nan cikin gida yanzu suka zo daga abuja yara kuma suna school sai shida na yamma Shaheed zaije ya É—akko su"
"Ammi kano zan tawo nariga da na datse duka igiyoyin aure na da Sumayya na mata saki uku kafin nazo nan nasan ke ba ganin girman zunubin nan data aikata zakiyi ba, da zuciyarki ta musulumci saiki ce na barta da tun abaya kin barni na sahale mata da duk haka bata faru ba"
"Assha Mustapha saki irin haka ba daÉ—i fa banso kayi uku lokaci guda ba"
"Ammi bazan iya sake zama da mishirika ba, gaba inaga kashe ni zatayi"
"Allah ya kyauta Mustapha, yanzu dai muna tareda baki zan koma ciki sai kazo" sallama sukayi Musty ya koma É—akin Sumayya da har sannan take tsugunne kan kafafunta tana kuka, jawota yayi har compound ya watsota waje ya maida kofa ya rufe, mikewa Sumayya tayi Allah yasa da mayafi a jikinta har jakarta na kafaÉ—arta futa tayi ta tai tafiya mai nisa sannan ta sami inda tasai takalmi kai tsaye tashar mota ta nufa ta hau motar zuwa katsina, cikin motar kuka take sosai tana daÉ—a cin alwashin duk yanda zatayi sai ta koma gidan Mustapha ko zatayi yawo tsirara

Abbas zaune a falo fuskarsa cunkushe da damuwa tsawon watanni a haka yake, Rumana ta kasa gane kansa ita dai zata iya cewa tun bayan ɓatan Aimanah Abbas ya koma haka duk iya kokarinta nason ganin ta goge masa wannan damuwar data bayyana karara a fuskarsa ta kasa, wayar Rumana dake ajje kusa da shi ce tayi kara ya kalli sreen na wayar ganin Ammi ke kira ya mikewa Rumana wayar ya mike zai bar wajan ihun murnar da yaji tayi yasa shi juyowa a fusace zai mata faɗan abinda tayi, tsallan data yi ta rungumesa ya hana shi magana
"Honey Yaya Aimanah yau ta dawo gida Allah alhamdulillah" wata nauyayyar ajjiyar zuciya yayi wacce tasa har Rumana sai da ta kalllesa kallo irin na tuhuma, fuskarsa ta kalla take taga ba wannan kuncin sai wani zallar farin ciki da ya mamaye fuskarsa
"Abbas daman wannan damuwar danake gani a fuskarka tsawon lokaci duk akan ɓatan Aimanah ne, kana nufin har yanzu akwai son Aimanah a ranka ashe farin ciki kayi da Yayanmu ya sake ta" a razane Abbas yaɗago yana kallon Rumana da tsawon rayuwar auransu bata taɓa kiran zallar sunan sa ba sai yau
"Rumy maine haka kuma ni muka..."
"Kimin shuru bakada abinda zaka faɗa min" Rumana da gudu ta faɗa ɗaki Abbas ya rufa mata baya yana kiran sunanta....✍🏻
[2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da bakwai*
Chapter 58 · 0% Book details