← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 62

Sashe 6

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana tsaye jikin motarsa ya zubowa kofar gidan idanu, tunda ta fito yake kalonta ita ko idanunta a kasa harta karasa inda yake tsaye jikin motar sa nesa dashi kaÉ—an ta tsaya ahankali kamar batason yin magana tace
"Ina yini ya hanya?" ta haÉ—e kalaman wajan É—aya batareda ta jira yabata amsa ba, wani daÉ—i ne yakume zuciyar Abas yau É—aya Aimanah ta kulasa harta gaida sa tana tambayar sa hanya
"Lafiya kalau Hayatie yakike ya school?"
"Lafiya! Mah tace kashigo"
"To muje" yafaÉ—i haka yana nuna mata hanya
"kayi gaba na bika a baya"
"Naki wayon saidai mu jera" murnushi tayi suka jera zuwa ciki.

Mas'ud ya gyara zaman sa ya fuskanci Ammi dake cika tana batsewa jin abinda yakawo Mas'ud É—in wajanta, harya gama maganar dayake bata katse sa ba har saida yakai aya
"Mas'ud kafita a idona ina ganin mutumcinka inda nasan abinda yakawo ka kenan da bazan tsaya na saurareka ba"
"Ammi dan Allah kiyi hakuri kinga kuwa yanda Mustapha ya koma, ko ke kika gansa zaki tausaya masa, dan Allah ki masa addu'a kirage fushin nan da kike dashi, fushin ki ma kawai zai iya saka sa a wata masifar da tafi wannan, ki masa addu'a na rantse da Allah ko kaffara bazanyi ba Amarya da Sumayya ba haka suka bar Mustapha ba, ni zuwa nayi muyi magana dake musan mai zamuyi akan lamarin Mustapha, wancan satin fa bakiga yanda yazo office É—ina ba a birkice wai Sumayya ta aikesa ya siyo mata abinci, Mustapha fa Mistaphan da yarinyar nan bata ishe sa kallo ba ace itace yanzu ta aike sa siyan abinci ai daga ji Ammi kinsan akwai wata a kasa"
"To Mas'ud maizan maku yanzi?"
"Yawwa Ammi haka nakeso ki faÉ—a yanzu dai daga farko yakamata mu fara masa abinda zai karya wanan sihirin da aka masa"
"Taya kasan sihiri ne ajikin Mustapha bayan sihiri ma fa harda hali" murmushi Mas'ud yayi kana yace
"Ammi ki yarda dani nafi kowa sanin Mustapha nasan halinsa wallahi mace tayi kaÉ—an ta hana sa zuwa gareki kema kin sani kinsan soyayyar da biyayyar sayake maki, ki duba yanda duk ya birki ce yakoma kamar ba mutum ba, cemin fa yayi yana son ganin ki inya É—akko hanya zai zo gidan nan gaba É—aya saiya manta hanya"
"Naji Mas'ud zan haɗa masa maganin karya sihiri jibi kazo ka karɓar masa"
"Yawwa Malama Ammi" mirmushi kawai Ammi tayi sukayi sallama Mas'ud ya shiga É—akin Umma sukayi sallama, wajan fitowara daga gidan ne ya haÉ—u da Murjana zata shigo gidan itama, ko kallon inda take baiyi ba balle ya amsa gaisuwar datayi masa, Murjana tafaÉ—a É—akin Amarya bako sallama tafara magana

"Mai wannan gayan na gidansu Aimanah yazo yi gidan nan?"
"Murjana kenan ni ina zan san maiya zo yi banma san ya zo ba, kin faÉ—o min É—aki ba sallama"
"Amarya nifa wallahi badan badan ba da sai nace nima a kama min shi ya shigo hannu nayi wuf dashi kawai gayan yana birgeni, harfa gaida sa nayi yaki amsawa" Murjana tafaɗi haka tana zumɓuro baki irin na shagwaɓaɓɓun yara
"Murja ba ba irin wannan nakeso ki aura ba mai nasama yaci balle yaba nakasa, kijira akwai tanadin danake maki wanda zakiyi farin ciki da hakan"
"A'a nida gaskiyya Amarya banason wani ni Mas'ud nakeso, kuma dole ki san yanda zakiyi na aure shi ko na tone asirin da muka binne a makabarta...✍🏻

07039793439
[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

Shafi na Biyar

"Murjana mai nake ji kina faɗa? akul ɗinki wallahi duk randa kikayi wannan gangancin saina matukar saɓa maki sannan kisa a ranki bazaki auri Mas'ud ɗin ba Salim zaki aura ɗan kawata matar minista ana kai ki inda zaki huta kina cusa kanki cikin wahala mai za'ayi da Mas'ud har maye kuda balle romansa"

"Amarya salim kuma ni bana son sa bazan aure saba kin san maganar dayake min ne É—an iska ne fa"

"Ke wai Murjana sai yaushe zaki waye? yar soyayyar nan dayake nuna maki ce iskanci? maye a ciki danya rike hannunki ya sumbata ai soyayyace"

"Ni! ni!! ni!!! bana sonsa wallahi abani wanda nakeso ko nayi ba dai dai ba" Murjana tafaɗi haka tana buga kafa irin na shagwaɓaɓɓun yara ta wuce ɗakin Amarya tana cigaba da faɗar maganganu, Amarya tabita da idanu harta shige ɗakin, tashi Amarya tayi daga wajan ta danna wayarta tasoma magana kasa kasa.

"Boka tsito mai dogon zamani barka da dare" da wata iriyar murya kamar bata mutane ba yasoma magana wacce ke futowa da wani ihu

"Barka dai doguwa mai dogon zunubi maike tafe dake a wannan daran?"

"Tsito yarinyar nan Murjanatu keson bani matsala a kan yaron nan Mas'ud kadai san maganar"

"Mai dogon zunubi ki bar wannan maganar komai namu zai iya lalacewa in muka shiga shirgin yaron nan a tsaye yake kan addu'a da azkhair gashi mayan karatun kur'ani na duba ta ko'ina naga bazamu sami riba akan yaron nan ba, ita kuma Murjana yau zanyi aiki a kanta zata manta da duk wani sirrinki data sani zamu rike zuciyarta sai yanda kikayi da ita, daga karshe gobe kizo anan zaki kwana kin dai san aikin basai na maki bayani ba"

Hmmm Amarya taja Numfashi kafin tace "Tsito na gane amma ina cikin jini hakan bazaiyu ba sai nayi tsarki"

"Yawwa hakan yayi daman ina neman jinin al'adar mace wadda tai haihuwa biyu bata sake ba zanyiwa wani É—an majalissa aiki, kizo goben da wurwuri"

Jiki a sanyaye ta amsa masa da "To" ta ajje wayarta tana mita "Gaskiyya boka kana takuramin kai kullum cikin jaraba kai aba ba wani girman kirki ba".

*MUSTAPHA*

A hanakali yake cakalar abincin da sam ba daÉ—i ci kawai yake saboda yana tsoron masifar Sumayya wacce ke zaune fegansa ita hankali kwance take cin abincin bata da wata damuwa, wayar Mustapha datayi kara ita taja hankalinsu gaba É—aya, yakai hannu zai É—auki wayar Sumayya tariga sa É—auka, "Aboki" Sumayya ta faÉ—a tana tsare Mustapha da idanuwa, mika masa wayar tayi
"gashi wannan sarkin nacin ne Mas'ud É—aga kiran kuma kasa a hansfree," haka yayi kamar yanda tace É—in
"Barka da dare Amini na fatan ka wuni lafiya yau gaba É—aya banji kaba"

"Aboki abubuwa ba sauki aikin office ya rikeni ban samu shigowa wajan kaba kamar yanda nace, kasan inata shirye shiryan tafiya india cost É—in nan na wata uku a satin nan nakeson tafiya"

"Yayi kyau ashe da ban kira ka ba sai lokacin tafiyar yayi sannan zaka faÉ—a? ka gayawa Ammi?" kwarewa Mustapha yayi sakamakon Ammi dayaji an ambata gabansa yai wani irin faÉ—uwa

"Wace Ammi?" Mustapha ya ambaci hakan hankalinsa kwance, Mas'ud saurin jingina yayi da fuskar gadonsa take wasu hawaye masu É—imi suka zubo masa yasoma sharewa kamar bazaice komai ba sai kuma yamagantu

"Mustapha Ammi ce baka sani ba? ashe nima baka sanni ba?"

"Freind ka yarda dani na rantse ban santa ba nakasa tuna inda nasan sunan a kasan zuciyata inaji kamar na santa" Mas'ud katse kiran yayi ya kifa kansa saman cinyarsa yafashe da kukan tausayin É—an uwan nasa "Yazama dole a kaina insha Allah saina fito dake daga wannan mummunan duhun daka faÉ—a"

Sumayya daÉ—i ne ya mamaye zuciyarta jin aikin da boka tsito yayi masu jiya, aiki yayi sun sa yamasu aikin da gaba É—aya Mustapha zai manta da mahaifiyarsa su mallake dukiyar sa gaba É—aya itada Amarya, zuciyar ta fal daÉ—i ta wuce É—akinta ta kira Amarya tana faÉ—a mata yanda Mustapha sukayi da Mas'ud, Amarya tayi farin ciki sosai daman ta riga da ta yadda da aikin tsito daga ka faÉ—a ne bukata zata biya, har rawa rayi tai juyi a cikin É—akinta, Murjana na mata dariya, tsakar gida ta fito tayi ko sa'a Ammi ta fito daga É—akin Momy uwar gidansu, Amarya ta fashe da dariyar keta tayi tsalle tai juyi ta fara yar waka "Daka haifi gwammana gwara ka haifi matar gwamna saini Amarya surikar Mustapha yau ya gwangwaje ni da kujerar hajji, Æ´a mace kyautar Allah wata ta haifi maza ta haifawa wasu ita da banza É—aya suke a wajan É—anta"

Ammi murmushi tayi harta soma tafiya zuwa É—akinta sai kuma ta tsaya ta maida martani dan tasan kai tsaye Amarya da ita take

"Amarya ki fita sabgata zan matukar saɓa maki a gidan nan, nafa sani nariga nasan komai aikin asirin, na riga na bar maki shi ke da yarki na godewa Allah dayasa ba shi kaɗai na haifa ba bare abin yadaman"

"Saude ni kike gayawa na ma É—anki asiri inace nan nan yazo har É—akina yace yanason Æ´ata Sumayya daman sai da nace masa bazan basaba yanace saboda nasan kun riga kun tsane ni a gidan nan" Amarya tafaÉ—i tareda fashewa da kuka, Alhaji Kamal da yaji kukan Amarya fitowa yayi daga É—akinsa

"Ya isa nace ya isa wai mayake damun kune da daran nan zaku tayarwa da mutane hankali, ke Saudat na fuskanci tunda akayi auran nan kin tashi hankalinki kin tisa naja'atu a gaba kamar ita tace Mustapha zoka auri yata" Momy tai saurin kallon mijin nasu cikeda mamakin sauyawarsa a jiyan nan mafa sunyi magana akan auran Mustapha da Sumayya har yace yana tausayin Ammi ganin yanda É—anta ya juya mata baya ko gidan ya shigo shi da Sumayya basa shiga inda Amni take É—akin Amarya kawai zasu shiga su gama abinda zasuyi har subar gidan baya ko kallon É—akin Ammi

"Alhaji laifin Ammi ka gani ai kuwa idan ba'a tausayawa Ammi ba ba'a ga laifinta ba, inace jiyan nan..."

"Ya isheki haka Asiya daman ai na lura kun takurawa Naja a gidan nan da da take faɗar kun haɗe mata kai bana yarda yanzu naga zahiri, ke Amarya shige ɗakinki barni da matan nan zanyi maganinsu a kanki zan iya aika ko wacce gidan su" Momy mamaki yakashe ta ta dafe baki🤔kawai tana kallon Amarya, Ammi batace komai ba ta karasa ɗakinta, Amarya ma komawa ɗakinta tayi tana jinjinawa aikin Boka tsito dan jiyan har Alhaji Kamal tace a haɗa duka a ɗinke bakinsa akan auran nan yadaina ganin laifinta, saura Momy ma zatayi maganinta itama.
Chapter 6 · 0% Book details