Sashe 5
Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Amincin Allah yatabbata a gareki tauraruwata fatan kin tashi lafiya, Dan Allah inaso abani dama na kira wayan nan muyi magana bakon masoyi ne,_ Bakon masoyi Aimanah tafaÉ—a a fili batareda tasan ta faÉ—a ba Anty Ummi dataji abin data faÉ—a dariya kurum tayi taci gaba da danna wayarta, minti kaÉ—an tsakani wayar Aimanah tayi ring kamar bazata É—aga ba ganin lambar da'akai mata tex ce yanzu, saida ta kusan katsewa sannan ta amsa kiran kara wayan tayi a kunnanta tai shuru batace komai ba
"Haba kyakkyawata kika kashe wayanki jiya"
"Malam mai yasa kake da naci ne bani kake nema ba, wannan ba lambar da kake nema bace nagaya maka tun jiya, Dan Allah kadaina kirana kana takuramin"
"Uhm uhm ke nake nema ba kece jiya muka haÉ—u a shoprite ba kika bani lambarki?" dariya Aimanah tayi kana tace
"Kaine wai ina kasami lambata?"
"Sirri ne amma ki tambayi Antynki"
"Anty Ummi" Aimanah ta faÉ—a ahankali
"Indai itace wacce kuke tare jiya to ki tambayeta, Aimanah tsaya ki saurare ni dan Allah nazo da lamari mai girma agareki Anty Ummi tabani labarin soyayyarki da Mustapha da tambarin da kika yiwa maza, ki sani kamar yanda mata ba halinku É—aya ba haka maza muma ba halinmu É—aya ba, ina sonki so irin so na aure bada wasa nazo ba dan Allah kibani dama naje ga iyayanki su bani damar zantawa dake mu fahimci juna manya su shiga a tsaida ranar auranmu, niba yaro bane bazanyi soyayya irinta yara ba"
"Soyayya kuma daman har yanzu akwai wannan kalmar, ni babu ita a wajena, a zuciyata da wajena tuni an kashe so" Aimanah na gama faÉ—ar haka ta katse kiran ta ajje wayar ta wuce É—akinta da sauri, Anty Ummi tabi Aimanah ta kallo tana girgiza kanta hannu tasa ta É—auki wayar Aimanah dake ring sun jima suna magana da Abas daga karshe tamasa kwatancan gidansu Aimanah dake kano.
Abas bashida kowa daya sani a kano hakan yasa yasha wuya sosai kafin yasamo gidansu Aimanah da Yaya Mus'af sukayi magana ya nema masa izinin ganin Aimaha Daddy yace yabasa dama yaje inhar sun dai daita zaiyi farin ciki da hakan, cikeda É—oki Abas ya É—auki hanyar Abuja baishiga garin da wuri ba lokacin dare yayi goma saura na dare hakan yasa kawai ya wuce gidansa, cikeda takaicin rashin shugowarsa garin da wuri,kasancewar washe gari lahadi shiyasa dayayi sallar asuba yakoma barci bai tashi ba sai sha biyu na rana, yayi mamakin irin baccin dayayi "Barcin gajiya" yafaÉ—a ahankali yana murmushi shi kaÉ—ai, wanka yayi haÉ—eda É—auro alwala yafito, tsab ya shirya cikin Sky blue É—in yadi ya fita masallaci, ahanyar dawowarsa daga masallacin ne yakira wayar Yaya Mus'af bayan sun gaisa ya bukaci yabasa adress na gidan Yaya Mansur yasan koya kira Aimanah ba É—agawa zatayi ba yana tinanin ma tasa lambar sa a blacklist sabida jiya yayita kiran layin baya tafiya, Ya Mus'uf yabashi adress bayan sun gama wayan ya kira Yaya Mansur yamasa bayani Abas da abinda zai kawosa gidan, Mansur yayi farin ciki sosai duk da daman Ummi ta gaya masa haÉ—uwar su da Abas É—in a Shoprite harma da kiran dayakewa Aimanah bata É—agawa duk yasani zuba mata idanu kawai yayi yana jiran Abas yakawo kansa, Yaya Mansur ya kalli Anty Ummi yace
"Masoyiya inada bako fa mai zaki shirya masa?"
"Duk abinda kace Masoyi"
"Ok asamar masa abu mai sauki na snack yana hanya, yanzu Mus'af yafaÉ—amin Abas zai zo" yafaÉ—a ahankali yana kallon inda Aimanah take itada yara saboda karta ji abinda yafaÉ—a,
"Wai da gaske kai nayi farin ciki muna da babban bako,
"Aimanah bar yaran nan da Abbansu mu shiga kicin, koma dai jeki kawai ki shirya, kiyi gayu sosai babban waje zamu"
"Allah Anty kice na kure wankana" Aimanah tafaÉ—a cikeda É—oki, Anty tawuce kicin tana dariya yayin da Aimanah ta shige É—akin su Zaheed nan komai nata yake anan ta sauka tunda tazo, gefan gado ta zauna tareda kira a wayarta
"Mah bakiyi kewa ta ba?"
"Kefa Aimanah kin fiya rigima kewa kuma kamar wata karamar yarinya nan da watani ma aure zan maki ki tafi gidan mijinki " Mah tafaÉ—i haka tana dariya
"Shikenan Mah bazan dawo ba anan zanyita zama tunda bakwa nemana, kuma ni bazanyi aure ba"
"Muna nemanki mana amma yaya zamuyi tunda Yayanku ya rike ki, kilama kinzo Abuja kenan, jiyan nan Daddy ke cewa yakamata ki dawo Monday zaku koma school nan da kwana takwas"
"Mom nadawo Abuja fa da zama kika ce?"
"Au Suɓul da baka ne, inake ina Abuja wannan garin sai su Zaheed"
"Mom gobe zan dawo, garin nan ya isheni ba inda nake fita fa daga gida sai gida inkinga mun fita to shoping mukaje"
"A'a karki tawo gobe, kijira sai friday muna Kaduna nida Daddynku gidan ba kowa sai Alhamis zamu koma gida"
"Mom mai ake a Kaduna?"
"Daddy yazo samina shine muka tawo tare"
"Wow Mom kuna lokaci fa keda Daddy yanzu nan da Kaduna saida kika biyosa?"
"Ki kiyaye ni Baby, kyalesa zanyi yatafi shi kaɗai yammatan zamanin nan su kallemin shi, ina bazanyi wannan saken ba, abaya ba'amin kishiya ba yanzu ba zan bada wannan damar ba" dariya Aimanah tayi tareda kashe wayar tana dariya sosai, yanda Mahh da Daddy suke wani abin kamar sabbin aure😂da sauri tamike ta shige bathroom tana faɗin "Ainamah yi wanka ki shirya kafin Anty Ummi tazo tasaki a gaba tana mita" ilai kuwa tana fitowa daga wanka saiga Anty Ummi ta shigo
"Nashiga aljannah ni Sa'adatu daman wai baki gama shiryawa ba to maza ana jiranmu" closet ta buÉ—e tazarowa Aimanah wata doguwar riga ta atamfa data sha stonework sai walwali take
"Saka wannan inkin gama shiryawa ki sameni a falo ina jiraki"
Aimanah a nutse tagama shiryawa ta ta feshe jikinta da kalolin turare masu sanyin kamshi ta kafa É—aurin É—an kwali kalar na yammatan wannan zamanin sosai tayi kyau, wayarta ta É—auke ta kashe solpie tana murmushi
"Mustapha" tafaÉ—a a hankali tunawa da tayi ko wanne lokaci in tayi kwalliya irin haka takanyi hoto ta tura masa yayita yabawa.
Jiki a sanyaye ta fito falon, Anty Ummi ta tarar tsaye gaban danning tagama haɗa abubuwa saman babban plate, "Kai tawan Masha Allah kyau iya kyau, karɓi wannan kaiwa su Yayanki falon baki, yayi bako leena bata nan taje kasuwa" Aimanah bata kawo komai a ranta ba ta ɗauki plate ɗin ta wuce, bakinta ɗauke da sallama tashiga falon kanta a kasa ta ajje farantin hannunta kan babban teble ɗin dake tsakiyar ɗakin ta juya zata fita ta jiyo muryar Yaya Mansur nacewa
"Ke baki iya gaisuwa ba" da sauri ta jiyo ta kalli yayan nata ta tsugunna har kasa tana gaida bakon wanda bata É—ago taga ko waye ba, taji dai muryasa kamar tasan muryar amma bata wani damu dataga wane ba ta fita, taÉ—an soma tafiya taji muryar Ya Mansur na kiranta ta tsaya cak batare data jiyo ba
"Malama koma ciki bakonki ne, ki tsaya ki saurare sa da kyau kiji da abinda yazo, duk da mun riga da mungama magana, shi zaki aura nagaji da wannan halin naki"
"Yaya kafa.." "Kimin shiru malama ba kanki fa aka fara soyayya ba'ayi aure ba ni tawa masoyiyar ma mutuwa tayi haka na hakura na auri wata wuce ki shuge ki bani guri kuma kika masa hauka na rugurguzaki wallahi"
"Yaya nifa bazan iya..."
"Zaki wuce ciki ko saina zaneki" Yaya Mansur yafaɗi haka yana nannaɗe hannun rigarsa, da sauri Aimanah ta shige falon ranta ɓace, Yaya Mansur yayi murmushi yasa kai ya wuce
Abas yabi Aimanah da kallo wacce ta zauna saman kujera bata ko É—ago ta kallesa ba
"Amincin Allah ya tabbata a gareki tauraruwa ta" kallo É—aya Aimanah ta masa bata sake kallon saba tayi kasa da kanta tana goge hawaye, har Abas yagama maganganun dazaiyi bata kula saba tana kallo yafice bayan yayi mata sallama, Abas mutum mai naci da kafiya akan abinda yake sone hakan ne yasa bai gajiya ba wajan zuwa gidan yaya Mansur, haka kullum yakan turo mata messages na barka da safiya, haka da dare ma zai mata messages na zafafan kalaman soyayya, tun Aimanah na share sa bata É—aka kiran wayarsa harta soma É—aga kiran koda bazata ce masa komai ba, suna a wannan yanayin Aimanah ta koma kano haka yamaida kano wajan zuwansa duk da bashida kowa acan, daga karshe har mahaifiyarsa Hajiya Hafsat saida ya taso Hajiyarsa tazo har gida ranar Allah yasa mutanan gidan suna nan Aimanah bataje school ba haka Mah bata fita aiki ba ranar aikin dare ne da ita, Ainamah na zaune a falo tana kallo jefi jefi tana danna wayarta matar tayi sallama ta shigo, Ainamah ta amsa sallamar cikin girmamawa ta gaida matar kana ta mike ta kira Mah, Mah mace wayayya dason mutane ta gaida matar duk da kuwa bata santa ba, sai bayam sun gaisa ne hajiya Hafsatu ke cewa Mah
"Sunana Hafsatu mahaifiyar Abas dake son Aimanah"
"Kai madallah sannu da zuwa ya gida ina Abas É—in ko ya koma Abuja?"
"Yan nan yanzuma tare muke dashi ya tisani a gaba da mitar nazo naga Aimanah nace taso shi" Aimanah tayi kasa da kanta tana murmushi jin abinda hajiyar ke cewa, mikewa tayi zata bar wajan Mah tace
"Ki shigo dashi" batace komai ba tayi hanyar fita daga falon, ta duba compound na gidan bata ga motarsa ba kamar yanda yasaba shigowa da ita ciki duk sanda yazo, wajan mai gadinsu ta karasa cikin girmamawa ta gaidasa kana tace
"Baba matar data shigo yanzu batare suke da wani ba?"
"E! tare suke da Abas yana waje can yafaka motarsa bai shigo ba yadai zo nan mun gaisa" buÉ—e kofa tayi ta fita,