← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 62

Sashe 12

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.....Idanunsa yabuÉ—e waÉ—anda yaji sunyi masa wani irin nauyi zabura yayi ya fisge kanula É—in karin ruwan dake hannunsa yamike yana kiran "Aimanah! Aimah!!!" yafaÉ—a da wani irin sauti da yai amsa kuwa a cikin asibitin, nan da nan likitoci sukayo kansa, wani jirin ne yasake É—ibansa yai luu zai faÉ—i kafin ya kai kasa É—aya daga cikin Nurse É—in dake É—akin yai saurin tare sa yafaÉ—i a jikinsa
Sumayya gefe ta koma ta É—ora hannu aka ta fashe da kuka ta fita waje ta kira Amarya a waya "Wayyo Amarya na shiga uku shi kenan na kaÉ—ai komai ya warware muna asibiti Mustapha ya birkice sai faman kiran sunan Aimanah yake, Mama dan Allah ki koma wajan boka tsito komai fa ya ruguje"
"Sumayya garin yaya kikayi wannan gangancin?"
"Mama banida masaniya akan komai kawaifa yadawo gida yafaÉ—i na kira asibiti suka zo suka É—aukemu yanzu kuma ya farka yana kiran sunanta"
"Bari na shirya naje wajan Tsito muji wannan masifa daga ina da rana tsakan nan"
Sumayya ta koma É—akin da Mustapha ke ciki ta tarar har anyi masa allurar barci cikin turancin daya daga cikin Likitocin yake gaya mata ta zauna nan kusa da shi ta kula da shi yana tashi ta kira su, Mustapha ya kwashe awanni yana barci kafin yabuÉ—e idonsa karaf idanunsa kan fuskar Sumayya saurin mayar da idanunsa yayi ya rufe yai shiru kamar mai barci, komai yasoma dawo masa a kwanyarsa "Nooo!!!" yafaÉ—a da ihu tareda mikewa duka a lokaci É—aya, wuyan Sumayya ya shaka
"Ke kika ja komai ina Aimanah ina Ammi?" Sumayya idanu zare ta kasa magana saboda shakar dayayi mata wanda takeji kamar za'a zare mata rai magana takeso tayi ta roke sa yayi hakuri ya kyaleta amma ta kasa, dan kansa ya saki wuyan nata tareda haÉ—ata da bango, gefan gadon ya koma ya zauna tareda dafe kansa yana fitar da numfashi da sauri sauri
"Ina wayata?" yafaÉ—a yana kallon Sumayya data koma can gefe ta tsugunna har sannan tana rike da wuyanta, mika masa wayan tayi ta koma nesa da shi ta tsaya tana kallon sa, lambar Ammi ya loda sannan ya danna call, bugun farko Ammi ta É—aga wayan gabanta na faÉ—uwa ganin kira da wata lamba ta wani kasa
"Ammi kiyafemin" abinda Mustapha yafara faÉ—a kenan bayan Ammi tai picking call É—in
"Mustapha kaine Alhamdulillah Allah na gode maka" Ammi tafaÉ—a da muryar kuka
"Ammi ina Aimah"
"Tana nan kalau"
"Ammi gida zan tawo"
"Mustapha ka zauna ka karasa abinda yakaika India kwanki fa suka rage maka"
"Ammi Aimah fa bazan iya zama anan ba Aimah ba" hmmm Ammi taja numfashi tana goge hawayan tausayin É—anta dasuka zubo mata
"Karka dawo Mai babban suna ka zauna kamar yanda nace maka Aimanah tana nan har kadawo"
"Shikenan Ammi zan zauna ki turomin lambar Aimah na kira naji muryarta" Ammi ta katse kiran ta É—ora kanta saman kujera ta fashe da kukan tausayin Mustapha, "Mustapha kadawo hayyacinka a kurarran lokaci yamzu Aimanah tazama ta wani" kuka tayi sosai sannan ta mike ta fita daga É—akinta zuwa na Momy, Mustapha yamaida kansa ya kwanta saman bed na asibitin yanajin zuciyarsa kamar zata fasa kirjinsa ta fito, wata iriyar soyayyar AIMANA ce ketasowa tun daga kasan zuciyarsa
"Ammi bazan iya ba, bazan iya jure zama anan ba Aimah ba, mikewa yayi yana kallon Sumayya data haÉ—a kai da gwiwa ta zafga tagumi
"Ke kisa a sallameni gida zan koma" asanyaye tamike ta fita shi kuma ya koma ya zauna yana tinanin irin hukuncin da zai yankewa Sumayya, saki shine babban abinda zuciyarsa ta amince dashi

A can gida kano kuwa gaba É—aya hankalin Amarya yatashi da kyar ta lalubi hijab É—inta ta saka tana kokarin fita daga É—akin Murjana ta shigo É—akin, kallo É—aya Amarya tayiwa Murjana ta É—auke kai tana tsaki
"Mama ina zaki?"
"Wajan boka Tsito zani komai ya warware"
"Mama dama kin zauna basai kinje ko ina ba ni na tone komai"
"Na shiga uku" Amarya tafaÉ—a tana É—ora hannu aka "Murjani ke kika mana wannan É—anyan aikin, na shiga uku ni naja'atu Allah ya wadaranki Murja" Amarya ta fice fuu daga gidan gaba É—aya.

Aimanah da Abas soyayya suke sosai da sosai ko yaushe suna manne a waya ayyuka sun masa yawa sosai sakamakon karin girma daya samu a wajan aiki hakan yasa bai zuwa kano sosai sai da waya, tuni Aimanah tafara aiki a ɗaya daga cikin gidan redion dake cikin garin kano, sosai tamaida hankali wajan aikinta, yau agajiye ta dawo daga wajan aiki gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta kamar mai zazzaɓi haka takejin jikinta wanka kurum tayi ko abincin dare bata tsaya taci ba ta wuce ɗakinta zata kwanta barci, harta gama addu'ar kwanciya barci ta lulluɓa da blanket taji alamar shigowar sako wayarta, da sauri ta ɗauki wayar tana murmushi "Abas farin Masoyi" tafaɗa afili tana kokarin cire key na wayar
_"Fatan alkhairi tareda fatan kina cikin aminci ina mai neman afuwa bisa tarin ɗimbin zunubin dana aikata a soyayyarki_ mamaki tayi ganin bakuwar lamba da bama ta wannan kasar ba goge massages ɗin tayi taja tsaki ta koma ta kwanta tana mai cewa kilama saɓanin number aka samu, Abas ne ya kurata suka sha soyayyarsu har tayi barci sannan ya kashe wayarsa ya kwanta.

Mustapha gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa gaba ɗaya hankalinsa yayo gida kano nageria, sam yafita harkar Sumayya ayanda yaso tun acan zai yanke igiyar auransu gaba ɗaya amma yakasa saboda tausayinta da yaji ya jinkirta sai yadawo gida,yau cike yake da murna da ɗokin gobe zai bar india zaiyi ido huɗu da sarauniyarsa Aimanah murmushi yayi sanda ya tuna Aimah ya tina tilin tex masaages daya ke aika mata amma bata taɓa dawo masa da reply ba, shi duk azatonsa fiahi tayi baisan cewa batama san shi bane, ita kuwa Aimanah ko sau ɗaya bata taɓa kawowa wai Mustapha nw ke aiko mata da sakonni ba waɗanda tana ganin shigowarsu wasu ta karanta wani ma ko buɗewa batayi zatayi delate ɗinsa, dan yanzu ba kowa a gabanda da zuciyarta sama da Abas wanda takewa wani irin so, sosai take son Abas a yanzu a cewar Aimanah yanzune tai soyayya, soyayyar Mustapha datayi a baya ba soyayya bace idan ta haɗata da ta Abas,
Abas É—an soyayya ne ya iya soyayya da tattalin mace kusan ko yaushe suna jone a waya motsi kaÉ—an ya kirata ya ce yayi kewarta, yau Aimanah ba inda taje kasancewar lahadi ce tana gida bata fita, azaune suke a falo itada Mahh suna kallon Arewa 24 Aimanah na tsotsar alawa ahankali kamar wata karamar yarinya Mahh ta kalli Aimanah tai murmushi
"Hmm Abas zai sha yarinta dan Allah jibi yanda kike ta tsotsar alawa mai tsinke kamar wata yarinya" Aimanah ta ɓata fuska kamar mai shirin kuka
"Mahh nifa yarinya dika shekaru na basufi goma sha bafa"
"Kice ma baki shekara ba" Mah tafaÉ—a tana maida hankalinta kan shirin da ake haskawa a arewa, wayar Aimanah tayi kara alamar shugowar kira kallo Mah tay taga hankakinta ba akanta yake ba hakan yasa tai pickin call É—in
"Hello Masoyi" Aimanah ta faÉ—a a hankali tana satar kallon Mahh
"Masoyiya ya kike, kawau naji kewarki na kiraki"
"Kewa niko bana kewarka saboda ko yaushe kana maƙale a zuciyata"
"Nima haka, gabana faɗuwa yake Masoyiya yanzu Kanol ya kurani zamu shiga daji, tsoro nakeji gabana faɗuwa yake Aimanah ji nake kamar wani abu zai sameni nifa gani ma nake kamar mutuwa zanyi....😰
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Goma Sha É—aya*

"Mutuwa kuma? haba masoyi tabbas mutuwa wajibi ce akan dukkan mutum bawa mai numfashi amma bazaka mutu yanzu ba, masoyi bansan ka da sarewa ba kaida kake karfafawa wasu gwiwa kuma yau kazo da wannan maganar insha Allah nasara ke tare da kai, katashi kai shiri ka haÉ—a rundunarka ku tafi Allah yana tare dakai Masoyi"
"Na gode masoyiya kin karfafa mun gwiwa, duk na sare inda zamuje ba sarvice kwana uku zamuyi ki kularmin da kanki, ki adanamin soyayyata can kasan zuciyarki, kiyi barci sosai banda tunani mai yawa, Ina fatan duk sanda kika tina ni kimin addu'ar samun nasara"
"Insha Allah nasara na tare damu" kashe wayar yayi naja ajjiyar zuciya ina É—ago kaina muka haÉ—a ido da Mah wacce bansan tsawon lokacin data shafe tana kallona ba
"Masoya, in anyi magana kice ke yarinya ce gashi har kin iya kalaman soyayya"
"Mahh" Aimanah ta faÉ—a cike da kunya, mikewa Aimanah tayi tabar wajan tana dariya, Mah tabi Aimanah da kallo tana mamaki, ada in wani yagaya mata Aimanah zata so wani bayan Mustapha zata karyata amma hukunci na ubangiji yau ga Aimanah nason wani mutum fiyeda son datayiwa Mustapha.
Chapter 12 · 0% Book details