← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 62

Sashe 10

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ok Sir" messages ne yashigo wayarsa hannunsa na rawa ya buÉ—e tex É—in
_Kalbie ka kwanta kayi barcin, bazan É—aga kiranka ba sai safiya, fi Amanillah_ yaji daÉ—in tex É—in nan sosai ya karanta sa ba adadi kwanciya yayi kan gadon kafafunsa a kasa, Idanunsa na kallon P o p É—in É—akin, ya lankwasa hannayansa ya É—ora kansa akai, wani irin bugawa Numfashinsa keyi, da sauri ya É—auki wayarsa ya dannawa Hajiyarsa kira, Hajiya wacce ke kwance jikin mijinta gabanta har faÉ—uwa yayi jin ring na waya ahankali ta mike zata bar jikin mujinta, hannu yasa yadawo da ita jikinsa ya rungumeta yasa É—aya hannun ya É—akko mata wayar,
"Abas" Hajiya tafaÉ—a hankalinta tashe ta É—aga wayar "Hajiya Aimanah ta amince dani yanzun nan ta kirani"
"Abas shine zaka kirani da daran nan da nayi barci fa"
"Hajiya bani da wanda zan raba farin cikin nan da shi kin sani sai ke, da inada kanwa ko kani tabbas su zan kira a daran nan" tausayin Abas ya rufe ta ta kakalo murmushi tareda kokarin ɓoye halinda take ciki ta ce
"Nayi farin ciki Abas Allah yasa albarka ka turomin lambar ta zan kirata da safe, amma kadaina kirana a irin wannan lokacin kasan dai lokacin Abbanka ne" dariya Abas yayi ya katse kiran, tareda sake kiran lambar Aimanah, Aimanah wacce barci ya fara É—aukarta firgigit ta farka jin karar wayarta
"Wo Abas" Aimanah ta faÉ—a tana lumshe idanu, ta maida kanta ta kwanta karar shigowar tex bayan kiran ya katse yasa ta É—auki wayar tasan ba tantama Abas ne _Hayatie ki É—agamin kira inaso naji muryarki nayi barci mai daÉ—i Inba haka ba zan tawo kano yanzu_
"Hmmm Abas" tafaÉ—a ta kashe wayar gaba É—aya ta maida kanta ta kwanta.

Ammi cikin barci taji wayarta na kara alamar kira, buÉ—e idanunta tayi ta janyo wayar bata tsaya duba ko waye ba ta É—aga kiran
"Ammi barci kike ki tashi mu raya daran nan kinsan matsalar da muke ciki"
"To Mah nagode" Mah bata sake magana ba ta ajje wayar kan daddumar data ke kai taci gaba da jan carbinta Istingifari tayi guda É—ari ra É—ora da salatin annabi kana ta fara jero addu'a wacce gaba É—aya kan Mustapha Allah ya fitar dashi daga halin dayake ciki, acan gidan Ammi ma alwalan tayi ta tada salllah haka mahaifiyarsu Ana itama sosai ta raya daran da sallah haÉ—eda addu'o'i, Aimanah washe gari bayan tayi sallar asuba barci ta koma bata tashi ba sai bakwai da rabi, cikin mintuna da basufi talatin ba tayi wanka, yau kasancewar garin antashi da sanyi yasa ta sanya riga ja da bakin wando ta É—ora doguwar rigar sanyi wacce tazo mata har gwiwarta tasa hula da karamin hijab daya sakko ya rufe kirjinta, da sauri ta fito ganin har takwas ta gota al'adar gidance karfe takwas ake zaman breakfast, kamar jiya yau ma kowa ya rigata zuwa wajan banda Daddy da jiya ya tafi legos sai Mah da taga bata fito ba, gaba É—aya tayi masu jam'i da ina kwananku, tare suka amsa tamaida hankali wajan cin abincin saboda yau da yunwa ta tashi, Yah Mus'af na lura da ita na yanda yau ta zage tana cin abinci sosai abinda suka daÉ—e basu gani ba tun sanda ta shiga kuncin rabuwa da Mustapha, wayarta ta kunna kamar jira ake kira ya shigo, dafe kai tayi ganin Abas ne mai kiran, kamar bazata É—aga ba sai kuma ta É—aga batace komai ba

"Barka da safiya abincin ruhi na"
"Hmmm Barka dai! ya kake" Aimanah mikewa tayi zata bar wajan ganin gaba É—aya yayun nata sun zuba mata idanu suna kallonta musamman ma Mas'ud wanda yakasa jurewa sai da yabiyo ta har É—akinta lokacin ta gama wayada Abas
"Ke dawa kike waya?" Mas'ud ya watso mata tambaya yana tsareta da idanu
"Uhmmm ummm Abas ne"
"Waye Abas?"koma wane ki gaya masa an maki miji" da sauri ta É—ago ta kallesa batace komai ba saboda maganar Mus'af da taji daga bayan yaya Mas'ud wanda bata sanma yana É—akin ba, yana tsaye jikin kofa ya É—ora hannunsa É—aya saman kofa É—ayan kuma ya rike kugunsa dashi
"Yah Mas'ud waye yayi mata miji?"
"Kai mai kake anan?"
"Yaya ba wannan ba tambayya nayi"
"Ni nayi mata" Mas'ud yafaÉ—a a zafafe, Mus'af yayi dariya har ya juya zai fita daga É—akin sai kuma ya dawo yana kallon Mas'ud ya ce
"Yaya nasani kana taya abokinka kishi ne, amma kasani yanzu ba Mustapha a zuciyar Aimanah, haka ba wanda zai mata dole anan dan haka ka zuba idanu kawai Aimanah ta sami mijin aure wanda yafi Mustapha" Mus'af yana gama faÉ—a yasa kai ya fice daga É—akin Mas'ud yabi bayansa a zafafe, hayaniya suka fara yi wanda yasa Mahh ta fito daga É—akinta tana kallonsu
"Yau kuma yarinta za'amin a gidan nan" Mah tafaÉ—a tana kallon yaran nata da basu san ta fito ba daga É—akinta,
"Mah ni yaron nan zai tsaya yana gayawa magana, na lura yaron nan shiyake so ya cusawa Aimanah soyayyar wani ba Mustapha"
"To Mas'ud ina Mustaphan yake yanzu zama zamuyi tayi da ita muna kallonta har Mustapha yadawo, ba wannan maganar kabar Aimanah ta so wanda zuciyarya ke so, koda Aimanah har yanzu Mustapha take so bazan yadda ba na kaita gidansa wanda bazata tsinci komai ba a gidan sai tarin wahala kishi da Sumayya ka zaɓa mata, kana kallon halin da ake ciki amma kake kokarin kare soyayyar Mustapha karna sake jin hayaniya a tsakaninku kan wannan maganar, kai Mus'af bawa Mas'ud hakuri kuma karna sake jin sa'insa a tsakaninku koba akan wannan maganar ba" Mus'af yabawa Mas'ud hakuri yai gaba abinsa
"Kayi hakuri bawai na goyi bayan Mus'af bane kasan dalili na"
"Na fahimta" Mas'ud yafaɗa yana mai wucewa ɓangaran su ransa ba daɗi tabbas da yana da dama saiya ɗaurawa Mustapha aure da Aimanah saboda yasan duk randa Musty yadawo Mustaphansa akwai matsala in Aimanah taƙi sa, Mah ta kalli Mus'af daya koma wajan daya tashi yaci gaba da cin abincin sa
"Karage zafin zuciyar nan taka Mus'af"
"Insha Allah zan rage" Mus'af yafaÉ—i haka yana cigaba da cin abincinsa,
"Gobe ka shirya zaka kaini ÆŠanbatta"
"Mah inada tiyata fa"
"Kullum tiyanta bata tashi sai anyi maganar zuwa ƙauye, Mus'af bafa a raina asali"
"Mah bana gudun ƙauye kawai banaso ne naje ayita kallona kamar sunga sabuwar halitta" Ma'aruf yayi dariya sosai wacce tasa har Mah dake tsaye saida ta dara ya ce "Mah Yaya fa bazai kaiki ba kibari ni zan kaiki gobe sunday bazan shiga kasuwa ba, inama Gwaggo Rakiyya zata birgeni data haɗa auranka da Ummita"
"Allah ya isa tsakani na dakai" Mus'af yafaÉ—a tareda ture plate É—in abincin dake gabansa, Mah dariya take sosai, yanda Mus'af yawani zazzaro idanu shi yafi bata dariya
"Ai kuwa ka kawo shawara haka za'ayi bari Daddy yadawo" Mus'af cak ya tsaya daga tafiyar daya fara yi zai bar wajan Mahh dan Allah kar muyi haka dake karma maganar nan taje wajan Daddy shifa É—aukar maganar zaiyi da gaske ina ni ina wata Ummita mai zanyi da kazamar yarinyar nan"
"Kai dai kake mata kallon kazama" Ma'aruf yafaÉ—a yana cigaba da dariya
"A'a Yah Ma'aruf kodai kodai"
"Kodai mai karma ki karasa bar maganarki anan kafin na faÉ—o maki sunan naki masoyin Amadu" Aimanah dariya tayi sosai kamar zata faÉ—o kasa daga saman kujera "Kasan Allah banakin Yaya Amadu kawai banason kaunar sa ne da ace ina kaunarsa zan iya auransa maye a cikin zaman kauyan wani bin fa sun fimu kwanciyar hankali, kuma ma ai birninka aljihunka" Mah bata sake ce masu komai ba taci gaba da dariyar Mus'af wanda tini yabar wajan,wayar Aimanah ce tayi kara ta kalli screen na wayar tana murmushi ganin Abas ne.

Akwana atashi yau Aimanah da Abas sun kwashe watanni tare da Abas soyayya suke sosai kamat baza'a mutu ba😂kusan ko yaushe suna jone a waya duk karshan sati yana kano, tun Hajiyarsa na mita harta zuba masa idanu,

Yauma kamar ko yaushe suna tare ta masa rakiya zai wuce Jigawa, Aimana ta gyara tsawarta jikin motar Abas tana kallon yanda yake tsara mata kalamai wanda take jinsu kamar a film, ba shine saurayinta na farko ba amma yanzu kam zata iya cewa ba kowa a zuciyarta samada Abbas, lumshe idanu tayi tareda buɗe su akan kyakyawar fuskar Abbas wanda yai kuri yana kallonta, "Abbas ina sonka sosai, zuciyata bugawa take akowanne bugu tana bugawa ne tareda kaunarka , Abas naroke ka karka yaudare kar..." Saurin katseta Abbas yayi tahanyar faɗin "Aimanah ki manta da wata yaudara banzo nan danna yaudareki ba naroke ki kimanta da *Mustapha* da yaudarar dayai maki ki ɗauki abin a matsayin kaddara da kuma dama can ba rabon aure a tsakaninku, bantaɓa soyayya ba sai akanki kece first love ɗina, uwar ya'yana insha Allah murmusa mana uhmm"

Dariya Aimanah tayi tareda saka hannu tarufe fuskarta tana dariya sosai, Abbas ya kalli agogon dake sanye a tsintsiyar hannunsa yaÉ—ago yana kallon Aimana wacce yanayin fuskarta ya canza, idanunwansa yabuÉ—e sosai yana kallonta tareda É—aga gira "Aimanah tafiya zanyi kinsan yau zan koma koma Abuja bana son tafiyar dare Hajiya faÉ—a takeyi, kwara na tafi da wuri, nabaki amanar zuciyarki, ki kularmin da kanki please"

"Kema haka My Abas ka kularmin da kanka ka tsare idanunka, karka kalli ko wacce mace"

"Kallo?" kallofa love ai daga kanki nagama kallon wata ɗiya mace kema kin sani nafaɗa maki ba sau ɗaya ba biyu ba" sallama sukayi Aimanah ta wuce cikin gida shi kuma yahau motarsa yatafi, ahankali yake tuki cikin zallar nishaɗi shi kansa yakasa gane shin wanne irin so yakewa Aimanah wani iri yakeji idan yana tareda ita jinsa yake kamar nan duniya babu kowa su kaɗai suka rage lumshe idanu yayi yana murmushi tareda tuna ranar farko daya fara gani Aimanah, da wani yammaci da bazai taɓa mantawa ba.
Chapter 10 · 0% Book details