← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 62

Sashe 44

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumayya yau baki tayi kawanta ne wanda suke karatu tare suka kawo mata ziyara suna zaune nan falo suna hira, Aimanah tadawo daga wajan aikinta yau bataje makaranta ba, gwaggo fulani da suke É—akinsu itada yara suka fito tun sanda sukaji tsayawar motar ta, Salman É—an gwaggo fulani ya shigo falon da sallama ya mikawa Aimanah car key É—inta yana faÉ—in
"Hajiya ga keys É—in nan"
"Yanzu dai bazaka daina kirana da Hajiya ba, nace in bazaka faÉ—i suna na ba kace min Anty mana"
"Da dai yafi sauki kam" gwaggo fulani ta faÉ—a tana dariya
"Yawwa salman bari na É—akko maka kuÉ—i kasiyo mana hanta yau miyar alaiyahu nakeson yi a gidan nan naga kuma bama da hanta" Aimah tafaÉ—i haka tana tafiya zuwa É—akin Al'Mustapha dake can karshan falo cikin wani lungu, gaba É—aya kawayan Sumayya suka bi Aimanah da kallo wacce ita sam bata lura da suba, mintina kaÉ—an da dawo hannunta rike da kuÉ—i ta mikawa Salman, ya juya ya fita
"Amma" Islam ta faÉ—a tana shigewa jikin Aimanah, É—aga ta tayi sama tana mata wasa
"Maman Hanif ta shigo É—azu bakya nan"
"Allah sarki bari na gama aiki zan dai shiga mu gaisa" Aimanah sai sannan taga bakin Sumayya ta karasa wajansu fuska a sake tana gaida su, suma faram faram suka amsawa Aimanah gaisuwarta taja yaran suka shiga bedroom É—inta, Gwaggo Fulani ta koma É—akinsu, Feenah ta kalli Sumayya ta buÉ—i baki zatai magana sai Leena ta ce
"A'A kar ce komai mu shiga daga ciki" Feena hannun Sumayya taja suka shiga Bedroom É—inta suka kullo harda saka key, zama sukayi gefan gado fina ta rike baki tana kallon Sumayya da mamaki
"Wai yanzu Sumy wannan ce kishiyar taki daman?"
"Ita ce" Sumayya ta faÉ—a a san yaye
"Cab tabbas zaki ga takaici jibi yarinya sai iyayi kalli uban kuÉ—in da ta fito dasu daga É—akin mijinta"
"Mijinta kuma" Sumy ta kuma faÉ—a cikin sanyinta
"To mijinta mana Sumayya ke kina zaune anan bazar kin saki jiki kina zaune da kishiya lafiya waya gaya maki ana zama da kishiya nifa nan da kika ganni sanda zan auri Alhaji na shiga malamai nayi na rabasa da matarsa da yayansa ya kaÉ—a ta can aka koma gida akaci gaba da cin tuwon dawa, na kama abina ram na rike yanzu in gaya maki daga ni sai É—ana muke abinda ranmu yake so mota sai wacce naso nake hawa, yanzu ki duba misali ace yau Mustapha ya mutu mai zaki samu a dukiyar sa sai dai fa aÉ—an tsakurar maki É—an kaÉ—an, kizo muje inda za'a maidaki tauraruwa a idanun mijinki ya zama sai abinda kika ce shi za'ayi a gidan nan"
"Bazan bi malamai ba, inkai zunubin ina" raÉ—a Lima tayi mata a kunne komai suka cewa Sumayya oho tadaiyi murmushi tai shuru tsawon lokaci kana ta ce
"Ina son Musty tabbas nima zan so na haihu da shi zanyi abinda kuka ce yau she zamuje wajan malam É—in?"
"Basai munje dake ba can enugu ne wajan da nisa sosai indai zamuje kwana biyu muke yi, Mustapha zai barki kiyi tafiyar kwana?"
"Zai bari mana, zan masa karya zani Kaduna gidan yayar babanmu nasan zai amince, ban taɓa ce masa zani wani waje ba ya hanani"
"Yawwa yar gari toki tanadi kuÉ—i, Malam yana aiki kamar yankan wuka amma fa sai yaji dumus" Lina tafaÉ—a tana dariya
"Banda matsala da kuÉ—i Mustapha nasamin kuÉ—i a acount É—ina duk wata bana amfani dasu tarawa kawai nake yanzu zasumin rana" nana suka rabu akan jibi zasu tafi enugu, koda Al'Mustapha yadawo ta gaya masa baiyi musu ba sai fatan sauka lafiya da yayi mata, sanda yace zai sai mata ticket anan ne tace bata son zuwa a jirgi mota zata bi, washe gari ta kira yar uwar babansu tafala mata tafiya zatayi ne bikin kawarta a enugu tasan in Mustapha yasan ga inda zata bazai bari ba tace masa nan zata zo, koda wata magana ta taso tace nan ta zo, jiki na rawa Matar ta amsa mata da to sukayi sallama Sumy ta tura mata dubu hamsin, randa sukai alkawari ranar suka tafi gaba É—ayansu ukun, Sumayyya tun tana tafiyar marmari harta fara galabaita sabida a enugun ma inda sukaje can wani kungurmin daji ne ba gida gaba ba gida baya, sai wata bukka saman tsauni haka su Sumayya suka hau tsaunin nan kafin suka rufe idanunsu lina na karanto masu wasu É—alasimai wata guguwa ta É—ebe su, tai kamar zata buÉ—e idanunta taji anan faÉ—in
"Karki soma kada ki sake ki buÉ—e mana idanunki anan, kina buÉ—e su sun zama banaki ba mallakin aljani tsunju" ai kara damke idanunta tayi har zuwa sanda taji guguwar ta tsaya taji wata murya mai kamar ana busa usur tana masu magana, Feena ta zungureta ta buÉ—e idanunta tai tozali da wani ramamman mutum dogo sosai ga rankwameman kai zaune saman fatar damisa" shekewa yayi da dariya yana kallon Sumayya
"Yarinya burinki ya gama cika tunda kika zo nan ungo wannan" yafaÉ—a yana wullo mata wani kullin magani kulle cikin kyallan atamfa
"Kimasa lemu ki tabbatar kinsa garin maganin nan to daga ranar sai abinda kika cewa mijinki duk abinda kika ce masa shi zaiyi zai manta da kowa da komai sai ke, hakama kishiyarki kowa nata zai manta da ita sannan zamu kafe ta a gidan komai zakiyi mata bazata iya barin gidan ba, gaba ɗaya dukiyar Mustapha ta zama taki sai abinda kika ga dama kika ce yayi shi zai yi" ranta ne yayi wasai taji gaba ɗaya kamar an yaye mata damuwar dake ranta, saidai jikinta ne yayi sanyi sanda taga Malam na saduwa da Lina ta bayanta anan ne hankalinta yata shi taga lina bata ko damu ba, agabanta ya kuma biyan bukatarsa da Feena, jikinta ne ya hau ɓari ganin malam na kallonta yana lashe baki
"Ki nutsu bazanyi komai dake ba, bama bukatar irinki akwai sauranki sai nan gaba kema zakiyi abinda suka yi juye mana kuÉ—in jakarki" gaba É—aya ta zazZzage masa kuÉ—in cikin jakar suka fita da baya da baya"
"Lina mai naga kunayi da mutumin nan"
"Wannan ba huruminki bane Sumayya kiyi kallo kawai kuma karki sake ki bawa kowa labarin abinda kika gani mun aikata da boka, wannan wata bukatar ce daban" hotal suka kama suka kwana...✍🏻
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin*

Musty ke zagaya falon da gudu, yara da Aimanah na biye da shi suna dariya, kallo É—aya zaka masu su matukar baka sha'awa Gwaggo Fulani na can karshan falon tana kallon ahalin dake cikin zallar nishaÉ—i, dukan su ba wanda ya iya kama Mustapha, zilliya yake masu kamar a filin kwallo, sai da yagaji dan kansa kana ya zube kan kujera Aimanah da yaran gaba É—aya suka faÉ—a kansa suna faÉ—in

"Yee mun kama Abbie mun kama abie"
"Abie ni coculate zaka bani" Islam tafaɗa tana taɓe fuska kamar zatayi kuka
"Abi mu kuma sweett muke so ko Aslam" Tasnim yafaÉ—a yana kalllon Aslam

"Ba wanda zan bawa komai, sabida ba wanda ya iya kama ni"

"Harni?" Aimanah ta faɗa tana taɓe fuska kamar wata karamar yarinya

"Ni na'isa nace har ke, in ban baki sweet ba yaya zanyi da ita" yafaÉ—i haka yana shafa mararta, bakinsa kan kunnanta yake mata raÉ—a
"reina inajin kishi fa, kizo muje ki bani ruwa" yafaÉ—a da wata irin murya da sauri ta É—ago kai ta kalli cikin idanunsa waÉ—anda suka tabbatar mata da abinda yafaÉ—a

"Baby yara na nan fa?"
"Ni ba ruwana da wasu yara" yafaÉ—a yana mikewa tsaye, kallonta yayi da runan nun idanunsa da suka fara canza launi, lumshe su yake a hankali yana buÉ—e su akanta, bayansa tabi ganin ya nufi É—akinsa, yaran ma suka bi su, cak suka tsaya daga bakin kofar É—akin Mustyn sanda Mustapha ya shiga

"Amma, Abie ya shige bai bamu sweet É—in ba, kuma kin hanamu shiga É—akin sa" haÉ—a yaran tayi gaba É—aya ta rungume su, dai dai nan Musty yafito da alawa da coculate yabawa kowa
"Mungode Abie Allah yakara arziki" yaran suka haÉ—a baki suka faÉ—a gaba É—aya

"Amin maza ku wuce wajan Gwaggo ta ɓare maku sweet ɗin" da gudu mazan suka tafi, Islam ta makale jikin Aimanah tana yamutsa fuska
"Ammi na wuce kije kinji bazan jima ba, Abie zan sa yayi barci ya huta yanzu zan zo wajanki" sakin Amman tata tayi ta tafi tana waigenta, Mustapha jawo Aimanah yayi suka faÉ—a É—akin
"Baby ka fiye rigima fisabilillahi da tsakar ranar nan"
"Aimah bazaki gane ba" yafaɗa sanda suka faɗa gado, ta buɗi baki zatai magana ya haɗe bakinsa da nata yafara aika mata da zafafan sakonni masu wuyar karɓa🚶‍♀️

Sumayya basu shigo Abuja ba sai dare hakan yasa bata sami damar aiwatar da aikinta ba ta bari sai washe gari, ai kuwa washe gari sai dare kana Mustapha yadawo yariga da yafaÉ—a mata, tun yamma ta gama haÉ—a komai har lemun daya sha maganin da malam yabata ta jere komai bisa danning jiran dawowarsa kawai take, bai shigo gidanba sai bayan sallar insha yana shigowa É—akin yara yafara shiga ya duba su kamar yanda ya saba, cake ya basu sunata murna sannan ya fito Aimanah na zaune a falon tana aiki a systam É—inta, ya tsaya É—an nesa da ita kaÉ—an
Chapter 44 · 0% Book details