← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 62

Sashe 20

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Prop cikeda damuwa ganin yanda idanun mutane yadawo kansu ya ce
"Habu abinda yafaru ya rigada ya wuce iyayanmu ne sukayi mu bazamu biya bashin gabar dasukayi ba"
Alhaji Abubakar daya É—auka da zafi huci kawai yake ya kalli Amininsa Habu ya ce
"Alhaji Habu auran nan bazai yuwu ba zoka É—aura ma Abas aure da Æ´arka Habiba yanzu"
"Alhaji in rai yaɓaci hankali fa baya gushewa komai yafaru a manta baya mun riga mun tara mutane kuma ni bazan ɗaurawa Habiba aure ba rana tsaka batare da saninta ba"
"Haka kace" Alhaji Abubakar yasaɓa malum malum ɗinsa ya fice daga masallacin mutane suka bisa da kallo a dai dai sanda Abas da tawagar abokansa suka karaso anan Babansa ke gaya masa ba wannan ɗaurin auran yaje ya nemi wata, nan take Abas ya faɗi kasa akayi hospital da shi
Prop tsabar bakin ciki kasa cewa komai yayi sai bin kofa da yayi da kallo baya ma jin abinda ke faruwa a wajan shidai kawai yaji sanda Akace fatiha aure yaÉ—auru tsakanin Al'Mustapha Kamal sareena da Aimanah Faruk mai nera, kokarin faÉ—uwa Alhaji Faruk yake da sauri amininsa Alhaji Kamal ya rukosa shida Ya Muneeer suka saka sa a mota Muneeer yaja zuwa gida, tuni labari yakai gida kan abinda yafaru Ma'aruf ne yakai labarin hankali yatashi sosai musamman Aimanah sanda taji labarin bada Abas aka É—aura aure ba faÉ—uwa tayi sumammiya Anty Hasana ta zuba mata ruwa ta tashi tunda ta tashi take kuka taki cewa komai ta kira wayar Abas yafi sau talatin ba'a É—aga ba,Mus'af kamar ya kaiwa Ya Mansur duka haka yaji dan shine silar wannan É—aurin auran, Mah hankali tashe ta sami Prop a É—akinsa tana kuka
"Prop kasan abinda kayi kuwa yaya zaku É—aura mata aure da Mustapha ya zaku jefa yarinya a masifa"
"Dan Allah Aisha ki sarara min nima bansan da auran ba kinsan halin masifar dana shiga lokacin da Alhaji Habu ya wulakanta ni a gaban mutane, Mansur ne ya É—aura auran Aimanah da Mustapha bani ba kije kiyi masa faÉ—a ni ki kyaleni da abinda yadaman" a fusace Mah ta fita daga É—akin zuwa Compound inda Mansur ke tsaye shida sauran mazan da basu gama watsewa ba hannunsa kawai taja zuwa ciki har É—akinta ta shiga da shi ta zaunar dashi gefan gadonta ta zauna a kasa
"Mansur maiyasa kamin haka mai yasa da kayi fushi bakai tunanin mazai faru ba ina Aimanah ya Aimanah zata iya kishi da wannan yar matsafan kana fa ganin halin da ake ciki yauahe ma aka samu Musty ya farfaÉ—o"
"Mah kiyi hakuri kaina ya kulle ne narasa mafita mahaifin Abas yayi fushi bansan maiya taɓa haɗasa da Daddy ba, kuma jiya naga Mustapha da Aimanah na kuka da daddare bayan mundawo daga dinner nayi zaton ko har yanzu tana sonsa"
"Ni ba zancan so nake ba abinda zaije yadawo nake dubawa"
"Mah muyi addu'a da fatan alkhairi sannan kisa ma auran nan albarka, ki goge fuskarki kar Ammi taga kukan nan naki bazata ji daÉ—i ba zata zaci bakison Æ´arki ta auri É—anta ne" da sauri Mah ta goge fuskarta sabida abinda Mansur É—in yafaÉ—a gaskiyya ne, Ammi ta shigo É—akin hankalinta tashe sai yanzu taji labarin abinda yafaru sabida bata gidan anan ta kwana gafda za'a tafi É—aurin auran ta tafi gida sabida ta kira wayar Mustapha sau ba adadi bai É—aga ba shiyasa taje ta gano lafiya, kuka take sosai tareda yiwa Mansur faÉ—an abinda yayi.
Chapter 20 · 0% Book details