← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 62

Sashe 46

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sumayya malam waya yayi mata akan tazo ga aikinta ya gama ta karɓa, hakan yasa washe gari ta ɗauki hanyar enugu, a jirgi taje shiyasa bata wani ɓata lokaci ba tana zuwa tsaunin da malam yake tahau kamar yanda sukayi wancan zuwa wannan karan ma hakan tayi malam wata koshashshiyar mage ya wullo mata ta cafe
"Kishiyarki nada hatsari sosai, indai wani abu zamiyi mata bazai taɓa kamata ba, sai dai na biyo mata ta bayan gidan, wannan magen da kike gani kisata a karkashin gadonki kar ki bata abinci ba ruwanki da ita, ga wannan" yasake wulla mata garin magani a cikin kwalba
"Ki jika shi ki sha, sanda zaki sha ki ambaci sunan kishiyar taki zata rinka jin tsoronki kuma duk umarnin da kika bata zata bi, hhhhhhh gida ya zama naki yarinya sai dai mumada sharaÉ—i zaki daina sallar asuba da la'asar a maimakom sallah biyar uku zaki nayi kina jinmu" jikinta na rawa hannunta na kankame da magen da ke É—an kuka kasa kasa ta É—aga kanta dan bakinta yakasa furta komai sabida tsoro da firgi cin daina salloli biyu da aka sata, ta fita da baya baya
Shatar mota ta ɗauka a tasha zuwa abuja sassafe ta isa gidan ta dake abuja, tayi nasarar tarar da Mustapha baya nan ya fita aiki, hakan yabata damar saka magen kasan gado ta kuma zuba ruwa a kwalba mai magani da malam yabata ta shanye...✍🏻
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da É—aya*

Aimanah dake kwance a É—aki gaba É—aya taji jikinta kamar wacce ake É—aurewa da igiya duka jikinta yayi sanyi kalau, lamo tayi tana kallon yaranta dake barcin safe, banko kofar da akayi da karfi ita ta farkar da Islam dake rigima daman barcin nata ba wani nisa yayi ba, Aimanah ta É—aga kai ta kalli Sumayya dake girgiza tana wani fari da idanu
"Ki fito ki gyaramin gida malama" Aimanah ta ɗago da niyya maida marta ni amma wani abu mai kyalli ya fito daga idanun Sumayya ya faɗa idanunta da sauri tayi kasa tareda runtse idanun nata, dariya Sumayya taci gababdayi tana kallon Aimanah data sun kuya tana murza idanunta, da sauri ta ɗago bayan taji idanun nata sun daina zafin amma kallon da Sumayya ta mata yasa gabanta ya faɗi ba musu tabi Sumayya zuwa compound ta soma aikin data saka ta, daga wannan ranar saiya zamana komai na gidan Aimanah keyi ta koma kamar mai aikin gidan, ko abinci ita keyi amma wanda Sumayya ke bata ko yaran baya isa, Aimana na cikin damuwa sosai nan da nan ta rame tai baki sau biyu tana kwada son futa ta gudu daga gidan sabida azabar da Sumayya ke gana mata amma getman ya hanata fita, Maman Hanif makociyar su Aimanah ce tasu tazo ɗaya sosai lokaci bayan lokaci suna zagaya juna su gaisa, Maman Hanif ganin kwana biyu Aimanah bata shigo mata ba hakan yasa yau ita ta shiga gidan, abinda ta gani ya ɗaga mata hankali ganin Aimanah kamar mata yarinyar gida tana rike da moper tana goge compound na gidan da sauri maman Hanif ta taɓa Aimanah, Aimanah ta juyo tana kallon ta, sharr sai hawaye daga idanun Aimanah, gefe Maman Hanif taja Aimanah suka zauna
"Maman Hanif ina cikin masifa kalli yanda rayuwa ta juyamin baya, Mustapha yadaina kulani komai na gidan nan ya canza jibi yanda nadawo yar aiki a cikin gidan mijina nakasa taɓuka komai ko na ɗaga waya zan kira makusanta na saina kasa nayi yunkurin barin gidan nan na tafi namu gidan an hanani fita ina zan saka kaina ban saba da wahala bazan iya wannan bautar ba" Maman Hanif goge hawayan idanunta tayi ta ruko hannayan Aimanah
"Aimanah kina addu'a kuwa kina azkhair yanda yakamata"
"Inayi Maman Hanif ina komai har karatun kur'ani ina yi"
"Aimanah na rantse da Allah asiri aka maku aka farraka tsakaninki da Mustapha, ki tsananta addu'a ki daina barcin dare kina ta shi cikin dare kina addu'a Allah zai fiddaki daga wannan jarabawar daya maki, sannan karki gayawa kowa wannan maganar ki rike sirrin cikin gidanki"
"Maman Hanifa nabar maganar nan fa kika ce karna faÉ—awa kowa na zauna cikin uku ba da azabar aikin nan harta motocin gidan nan ni nake wankewa"
"Aimanah kiyi hakuri" maman hanif ta faɗa bayan ta mike tun daga wannan ranar Maman Hanif ke kawowa Aimanah abinci a ɓoye wanda zai ishe su, Sumayya duniya ta mata yanda takeso sai facaka take da kuɗi tana abinda take so, tsadaddiyar motar Aimanah yanzu ta zama mallakinta da kanta tasa Al'Mustapha ya karɓar mata key ɗin daga hannun Aimanah yabata, a cikin wannan halin da suke Rumana ta haifi yaranta twince masu matukar kama da Abbas mace da namiji, Hajiyar Abbas jigawa ta wuce da yaran da mai jego acan zasuyi zaman wanka Abbas ma kwana huɗu da haihuwa yabi matarsa wai tare zasuyu zaman wankan, Hajiya Hafsatu mace mai kirki da son mutane ita tayi ta kula da Rumana Ammi da taje ma bata barinta tayi komao harta ɗora ruwa yiwa mai jego da jarirai wanka duk ita takeyi, Aimanah taji labarin haihuwar tayita ɗoki da zumuɗin zuwa suna amma Mustapha yasawa idanunsa toka yace ba inda zata, wannan duk huɗubar Sumayya ce, Aimanah tayi kuka ranar kamar ranta zai fita, ta duba duka account ɗinta gaba ɗaya bata da komai a ciki duka ta cinye su lokacin da Sumayya ta ɗebe kayan abincin gidan, sai da dare yayi kana ta kira lambar Yaya Mus'af bayan sun gaisa ta ce
"Yaya dan Allah kuÉ—i nakeso"
"Kina matar accounter kike neman kuÉ—i, ko bashin banki basai yabaki ba" Mus'af yafaÉ—a yana dariya
"Yaya banaso yasani fa, shiyasa nabari sai yanzu na kiraka, wasu kaya zanyi ordar nake neman kari"
"kamar nawa"
"Ko É—ari da hamsin nasamu"
"Bama masu yawa kike bukata ba, ba damuwa zansa maki yanzu"
"Nagode yaya" Aimanah tafaÉ—a tana share hawayan idanunta
"Ba godiya a tsakanimu ina mutanan"
"Sunyi barci tafaÉ—a tana kallon yaran dake barci" basu jima da sallama ba taji alart tana dubawa taga dubu É—ari biyu, murmushi tayi nan take ta yiwa Rumana transfer na dubu É—ari tareda mata messages _kiyi hakuri Rumana bazan sami damar zuwa suna ba anma zan zo daga baya naga babys ga kuÉ—i nan ba yawa asaiwa yarana riga_ Rumana murmushi tayi bayan ta gama karanta messages É—in

Hankali tashe Mustapha ke kallon Sumayya
"Ina kika saka min jakar da jiya na shigo da ita,"
"Jaka kuma na rantse ni banga ka shigo da jaka ba gidan nan" Sumayya tafaÉ—a tana zare idanu, a haukace Mustapha ke bincikar É—akin ko ina lekawa take ko zau gano jakar, rasa wannan jakar kamar rasa aikin sa ne, ga zargin cin amana da za'a masa kilama takaisa ga birsin hakan ya kuma tasar hankalinsa
"Sumayya ki fito min da jakata nan fa na ajjeta"
"Na rantse ban É—aukar maka jaka ba, in baka yarda ba muje É—akina ka bincika daga nan sai a duba na Aimanah" sak yayi yana kallonta jin ta ambaci Aimanah sunan da a yanzu bayajin akwai wani suna daya tsana ko son ji bayayi sama da sunan, É—akinta aka bincike tas babu jaka ba dalilinta, haka ta tisa Mustapha a gaba aka shiga É—akin Aimanah, ita tsorama taji daga gansu sun ahigo mata bako sallama mikewa tayi tsaye tana kallonsu
Chapter 46 · 0% Book details