← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 62

Sashe 53

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aimana tana turasu wajan get ɗin ta zauna wajan tareda fashewa da kuka wasu halittu ke mata gizo a idanunta kamar zararriya ta kwasa a guje ta shige gidan dan zamanta a wajan jitake kamar ana ɗaureta da igiya ɗakinta ta shige ta kwanta ta lulluɓa cikin blanket rufe idanu tayi har sannan tana hango haluttun nan na mata yawo cikin idanu buɗe idonta tayi tar wai tana karanto suratul bakara da karfin gaske, batayi nisa tana karantawa ba barci yayi awon gaba da ita tsawon awanni tana barci mai daɗi wanda ta jima batayi irin saba sai yamma sosai ta farka, durowa tayi daga gadon ta shiga bayi tai alwala ta tada sallah tai azahar kana tai la'asar tana nan zaune tana azkhair wanda ta jima sosai batayi ba taji an buɗe kofar ɗakinta, kallon kofar tayi Mustapha ne da Sumayya Musty na gaba rikeda takarda a hannunsa Aimanah ta kallesu kallo ɗaya ta ɗauke kanta har sanda taji Mustapha ya ajje mata takarda a gabanta
"Ga shi Na sake ki saki É—aya" lumshe idanu Aimanah tayi a zuciyarta take faÉ—in alhamdulillah, juyawa Musty yayi ya fita daga É—akin, Sumayya ta kece da dariyar mugunta tana kallon Aimana
"Yau dai mun yarda kwallon mangwaro mun huta da kuda, kici gaba da zama anan ke da yayanki nasan yunwa ce zatayi ajalinku, kina nan ba iya fita zakiyi a gidan nan ba sai sanda naso naga dama, kasar ma zamu bari zamu zaga duniya kafin mudawo nasan kin rigada kin zama ba matar Mustapha ba daga nan zan fitar dake daga wannan gidan" Sumayya ta fice tabar Aimanah saman darduma tana ambaton Allah da rokonsa akan yafitar da ita daga wannan ukubar da take ciki, zurawa takardar idanu tayi ta warwareta rubutun Mustapha raÉ—au saman farar takardar ninke ta tayi ta ajje ta saman gado, tana nan zaune ta jiyo futar su a mota bayan mintina taji an kuma shigowa É—akin nata wannan karon Lina ce ta shigo É—akin jikinta ne ya É—auki mazari sam bata kauna ko san ganin wannan matar, wani kallo take bin Aimanah da shi kafin kuma ta ce
"Zo muje," Aimanah ba musu ta mike tabi bayanta suka fito daga É—akinta, É—akin Sumayya taga sun shiga maida kofa lina tayi ta rufe batare data saka key ba, É—aga katifar dake shimfiÉ—e saman katakon gadon Sumayya Lina tayi wata mage ta bayyana ramammiya da ita idanunta ja jawur da su ko kyan gani bata da
"Kinason fita daga wannan halin da kike ciki, kinga wannan itace akayi asiri aka haɗa da ruhinki indai har magen nan na kulle anan bazaki taɓa iya barin gidan nan ba, ki bani dama da ƴan mintina na kashe kishi na dake ni kuma na maki alkawarin saina karya duk wani asiri da Sumayya ta maki," Aimanah baya taja ganin Lina na kokarin cire kayan jikinta, sai da lina tai tik ta ɗago tana kallon Aimanah dake makure jikin bango, jikinta gaba ɗaya karkarwa yake ambaton Allah kawai take a fili da zuciya, Lina ta tsugunna tana karkaɗa jiki a tunaninta zata ja hankalin Aimanah, kunce magen Lina tayi, cak Aimanah ta tsaya daga karkarwar da jikinta keyi, yanayin yanda take ji a jikinta taji gaba ɗaya ta sauya ta dawo Aimanar ta da, lokaci ɗaya taji kamar ana kunce ta daga ɗauri, juya idanunta kawai take a ɗaki tana neman abin dazata kare kanta daga Lina wacce ke kusanto ta, kan wata yar tukunya idanun Aimanah ya sauka batayi wata wata ba tasa hannu ta fusko tukunyar kasar ta bugawa Lina a fuskarta Lina ta saki wata karar azaba ta sheme anan, da gudu Aimanah ta fito daga ɗakin batayi wata wata ba ta fice daga gidan gaba ɗaya, gudu take sosai har batasan inda take jefa kafafunta ba sai ji tayi anyi sama da ita...✍🏻

07039793439
[2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da HuÉ—u*

ji kake keeeeeeeeeee matar dake jan motar tai saurin taka burki, Aimanah da motar tayi sama da ita ta dawo kasa kanta ya bugu da kwalta take yanke kan yafashe jini yafara zuba, nan da nan yan sanda dake kusa da wajan suka karaso ba'ayi wata wata ba akayi hospital da Aimanah wacce ko motsi batayi, matar data bige Aimanah kuka take sosai tana addu'ar Allah yatashi kafaÉ—un yarinyar data bige, hankali tashe ta kira babban É—anta ta sanar da shi halin datake ciki, cikin kankanin lokaci sai ga shi a Hospital É—in shiya rinka kwantar mata da hankali har zuwa sanda aka turo gadon da Aimanah ke kai daga emargency zuwa word, ruko hannun mahaifiyar tasa yayi suka bi gadon
"Dr ya ake ciki"
"Hajiya muje office na maki bayani" juyowa sukayi suka bisa zuwa office Muhd ya zaunar da mahaifiyarsa saman kujera ya tsaya jikin kujerar hannunsa cikin na maman nasa
"Hajiya gaskiyya yarinyar nan na a cikin wani yanayi mara daɗi, ta bugu sosai a kanta a yanda muke tunani koda ta farka to zata manta komai nata, sai dai lamari na ubangiji komai na iya canzawa tsaɓanin binciken mu, a karshe dai muyi addu'a"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku ni Zainabu yau kuma haka Allah yai dani kaico"
"Mom please ki daina kiran shiga ukun nan komai zai zo da sauki insha Allah muyi addu'a kamar yanda Dr ya ce, Muje a kira Azinatu tazo ta kula da ita ke ki koma gida, mu kula da komai"
"Muhd bazan iya komawa gida ba hankalina bazai kwanta ba tsoro nakeji karta mutu na shiga uku"
"Mom zan kira Dr Fawas ya maki allurar barci fa kinsan yanayin ciwonki dan Allah ki cire damuwa, muje na taya ki kiyi alwala ki sallah kiyi addu'a Mom"jiki sanyaye ta mike tabi bayan É—an nata

Mustapha kwantar da kansa yayi jikin kujera, haka kurum yake jin jikinsa ba daɗi har wani zazzaɓi zazzaɓi yake jin na shirin kamasa
"Sumy mu koma gida bazan iya tafiyar nan ba banida lafiya" harara ta wurga masa
"Sabida kawai bakada lafiya zamu fasa tafiya holewarmu" mikewa yayi ya ajje mata takardunta a kan cinyarta ya mike zai bar wajan ganin da gaske tafiyar zaiyi yasa ta ji gabanta na bugawa tabbas wani abu na faruwa a gida, wayarta ce tayi kara alamar kira ne ya shigo zaro idanu tayi tana kallon Mustapha da har ya fita daga recepsion, hannunta na karkarwa ta É—aga kiran Malam daya shugo wayarta
"Kinyi sake, Lina ta ruguza komai harta tukunyar ki ta fasata" hannu Sumayya ta É—ora aka zata saki ihu ta tina a inda take cike da damuwa ta ce
"Ran Malam yadaÉ—e yanzu yaya zanyi nasan dai tunda ina da kai banida sauran damuwa"
"Komai ya rushe Sumayya, mijinki na gafda dawowa hankalinsa hakan dai dai yake da barinki gidan sa"
"Shikenan na shiga uku ni Sumayya kayi wani abu dan Allah malam"
"Zanyi akan mijinki Aljani shinzu zai shiga tunaninsa bazai dawo hankalinsa ba kafin muga mai zamuyi amma dai kisani komai ya rushe kishiyarki ta bar gidan, gobe ki shirin karɓar baki daga kano" yana gama faɗar haka ya katse kiran wayar, a mota ta tarar da Mustapha yana zaune da alama ita yake jira, tana shiga yaja motar suka bar aiport ɗin suna shiga gida ya kwanta barci ba sallah bare salati, zuciyar Sumayya tai sanyi ganin Mustapha baice komai ba ta daɗa kiran malam sukai waya ya gaya mata lalle jibi tazo a sake wani aikin akan Mijinta, gyara ɗakin nata tayi ta kwashe komai sama ko kasa ta duba magen nan bata ganta ba, rai ɓace ta nufi gidan Lina a motar Aimanah wacce yanzu tazama ta hawan Sumayya, Lina na kwance saman doguwar kujera da kumburarran goshi zuciyarta fal takaicin abinda Aimanah ta mata ga ba biyan bukata ga ciwo ga kuma ɓarnar datayiwa Sumayya na ruguza mata komai, ga bakin cikin shikenan ba ita ba zuwa taron gobe da zasuyi a kaduna to ina zata da wannan katon goshi, gabanta ne yafaɗi dataji sallamar Sumayya, tsaye kam Sumayya tayi a kanta tana aika mata banzan kallo
"Kin kyauta akan wata bukata taki shine kika so ki ruguzamin rayuwa to ta Allah ba taki ba, yar akuya mai bin mata" dariya Lina tayi tana tashi zaune da kyar
"Gara ma ni nice yar akuyar ba uwata ba tsohuwar najadu"
"Lina ya isheki fa dani kike bada mahaifiyata ba ki tsaya a ni ɗin idan kika sake taɓo min mahaifiya inada makamin da sai na girgiɗe maki wannan auran wallahi"
"Kin daÉ—e baki kashe min aure ba, anan anan É—ina kike" Lina tafaÉ—a tana nuna tafin hannunta
"Ok haka kika ce to muzuba mu gani" Sumayya ta faÉ—a tana ficewa daga É—akin, kai tsaye data fita wajan mai gadin gidan ta tsaya suka gaisa ta basa kuÉ—i masu yawa akan yabata lambar mai gidan, get man baiyi wani tunani ba ya bata lambar tasa a wayarta tai save ta fito ta shiga motar ta taja, kai tsaye gidan Feenah ta nufa a mutumce suka gaisa sun jima suna hira kana Sumayya ta faÉ—o kan zancan daya kawota,
"Ni kuwa Feena ina vidio É—in nan da kikaiwa su Lina itada malam randa mukaje É—in nan?" Feena na dariya ta ce
"Yana cikin wayata duk sanda naso nishaÉ—i kun nawa nake na kalla nayita dariya ni kaÉ—ai"
"Ki turo min ta whatsapp"
"Ok bari na turo maki yanzu" ta kunna data ta tura mata, tana ganin ya shigo tai dariya bata jima sosai ba ta tafi.
Chapter 53 · 0% Book details