← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 62

Sashe 24

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Anty Halima sun haÉ—o kayan lefe na kece raini itada Anty Hasana koda suka kawosa gidan É—akin Momy suka ajje Anty Hasana bata zauna a gidan ba ta wuce gidan Ana sabida ta gaji sosai, Alhaji Kamal yaga kaya yasa albarka yace akai Momy da Ahmad da Shaheed sukai kayan har zasu tafi Ammi tace
"Alhaji Amarya bataga kayan nan ba amata magana" Momy ta leka ta gaya mata tazo taga kaya, ta leko daga bakin kofar sashinta ta tsaya tana karewa akwatinan da takasa kirga yawansu ta taɓe baki ta koma cikin ɗakinta batare da ta ce komai ba, su Momy suka wuce da kayan, Alhaji Kamal yabi Ammi ɗakinta, jiyowa tayi ta kallesa taja ta tsaya tana kallonsa
"Madam wai maiya canza minke ne?"
"Maizai canza ni kuwa kaine dai naga ka nufi wani waje daban" ajje hular kansa yayi ya zauna saman kujera yana murmushi,
"Alhaji daka futa na sameka a É—akinka bana son rigima kasan dai yau Amarya ce ke dakai"
"Sabida itace dani kuma sai akace bazan shiga inda raina yakeso ba, ko wacce acikinku ta sani nakan shiga É—akin da naso koda ba acan nake ba indai inada magana da ita kema dan rigima kike ji shiyasa kika kasa fahimta"
"Au rigima, ni karamar yarinya ce kenan?"
" E mana ni a wajena kinfi Raudah yarinta" dariya Ammi tayi ta zauna kusada Alhajin
"Bani ruwa na sha" Alhaji Kamal yafaÉ—a yana kallonta
"Nifa Alhaji bazan baka ruwa ba, nama tina banma da shi a É—akin nan É—azu nake gayawa Ahmad inya fita ya tawomin da shi"
"Babu a story ne?"
"E haka Shaheed yace dana ce ya É—akko yasamin a firij"
"Kinga yanda abu yakasance ba zato ba tsammani na tausayawa Aimanah na kuma taya Mustapha murna Allah ya taya sa ruko yabasu zaman lafiya da zuri'a É—ayyiba"
"Ameen" Ammi tafaÉ—a tana kwantar da kai jikin kujerar datake kai
"Da sonayi nabasa gidana dake Kabuga ya zauna acan sai kuma Halima take gayamin sun gama magana saman gidan dayake ciki zai gyara ta zauna acan"
"Haka nima É—azu take gayamin hakan yafi amma ya za'ayi ace Aimanah na sama Sumayya na kasa hakan kamar ba tsari"
"Haka Allah ya tsara, yace Sai Juma'a zata tare mai kuke shiryawa koba zakuyi taro ba"
"Naji Mas'ud É—azu yana cemin zasuyi Party ranar asabar abar tarewan sai asabar saboda Mustaphan bazai shigo kano da wuriba ranar juma'an jirgin dare zai biyo"
"Shikenan na tura masa gudun mawata ta bikin ban samu na masa komai ba"
"To yana godiya Allah yakara arziki mai albarka"
"Amin" Alhaji Kamal yace bayan ya mike, da sauri Amarya dake laɓe jikin window ta salallaɓa ta koma sashinta tana hucin takaici,
Anty Halima ta turawa Musty hotuna da vidion kayan da suka haɗo, Anty Halima ta tsaya kan komai ganin yatafi dai dai itada Ahmad suke komai, tsab aka gyara saman benan inda Aimanah zata zauna Anty Hasana da Anty Ummi sukaje suka gano wajan yayi kyau sosai, Prop yabawa Mah card ɗinsa yace suje da Aimanah ta zaɓi kalar kayan ɗakin datake so, duk yanda sukaso Aimanah taje ta zaɓa ki tayi sai Anty Hasana ce ta zaɓi komai, sukayi komai suka gyara saman inda Aimanah zata zauna yayi kyau sosai, gaba ɗaya Aimanah batada walwala tunda Musty yatafi legos ta kashe wayarta ko yaya Mas'ud yakawo mata wayarsa yace zasuyi magana da Mustapha bata musu kai tsaye zata karɓa daga ya fita zata saka wayar a airplane mode ta ajjeta gefe taci gaba da sha'aninta, daga farko kullum tana cikin kuka da damuwa saida Mah da Daddy suka zauna suka mata nasiha sosai sannan ta hakura ta rungumi kaddararta Mustapha, sau tari takan ɓuya tayi kuka sosai musamman inta tina Abas tanaso tasan halin dayake ciki amma tasan haramcin hakan bata taɓa kwada kiransa a wayaba kamar yanda bai taɓa kiran nataba tun bayan abinda yafaru lambarsa ma bloking ɗinta tayi a wayarta.
Sumayya gaba É—aya ta shiga damuwa musamman sanda taga an kawo kayan Aimanah an jera ta shiga É—aki tayi kuka sosai har saida idanunta suka kumbura
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na goma sha Takwas*
Chapter 24 · 0% Book details