← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 62

Sashe 59

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Rumy maiye haka dan Allah ki tsaya ki fahimce ni mana, wallahi bako ɗigon son Aimanah a zuciyata ina jinta kamar yar uwata wacce muka fito ciki ɗaya, wani ɓangaran kuma ina mata kallon yayar matata"
"Haka zakace min mana zaka min daɗin baki, inka ɓoye sirrin zuciyarka ai fuskarka ta fallasa asirin zuciyar" kusa da Rumanan ya karasa ya jawota jikinsa yana shinshinar wuyanta
"Ba wata mace a wannan xuciyar ta Abbas saike Rumy, kece dai ke kaɗai zaki mulkin wannan zuciyar yanzu ko gaba har zuwa karshan rayuwata Abbas bashida wata mace bayanke bazance na maki alkawarin bazan maki kishiya sabida komai mukaddari ne amma dai ina da tabbacin bazan iya son wata macan bayan ke ba, kece komai nawa" Sosai kalaman Abbas sukai tasiri a xuciyar Rumana anan dai suka raya sunna daga rigima aka ɓige da soyewa, tare sukai wanka yana shirin fita tace
"Yaushe to zanje kanon" dafe kansa yayi yana kallon cikin idanunta
"Ke dai kam Maman twince kin fiye rigima yanzu dai so kike mu kara wani faÉ—an, ko inaga dai so kike mu koma scound round" yafaÉ—a yana kashe mata ido É—aya
"Nidai ba daÉ—in bakin da zaka min wallahi sai naje kano naga Yaya Aimanah kuma tare zamuje da kai" zaro idanu yayi tareda haÉ—e fuska
"Ke dan Allah yaushe rabon da ki ganni a kano inaga tun randa aka É—aura mana aure da ke, bana jin nan kusa zan iya zuwa kano" yafaÉ—a yana lumshe idanu tareda kwantar da kansa a fuskar gado, alamun damuwa suka bayyana karara a fuskarsa, Rumana kallon mijin nata tayi tana murmishi tareda kudurce wani abu a ranta hakan yasa ta zauna kusa da shi tasa hanunta cikin nasa tana mirzawa a hankali tsawon lokaci suna a haka kafin tayi magana
"A wannan karon fa sai kaje kano, mai kake tsoro a kanon badai karka fama mikin son Amanah bane to itama tana kano kuma a yanzu kanada damar da zaka mallaki Aimanah, Abbas nabaka dama idan har Yaya Aimanah ta amince da kai ka aure ta" buɗe idanu Abbas yayi yana kallon Rumana daya soma tinanin ko kishi yaɗan taɓa mata kai ne,
"Ke!!! Rumana dawo hankalinki please"
"Ahankali na nake Abbas da gaske har cikin zuciyata gaskiyya nake faÉ—a maka inma bazaka iya yakin ba ni zan zama sarkin yakin neman auran Aimanah gimbiyar Abbas" Rumanah tafaÉ—a tana dariya
"Rumana abin nan bamai yiyuwa bane ki bar faÉ—a dan Allah, Aimanah fa yayarki ce"
"Dan tana yayata aiba haramun bane addini bai halatta haka ba"
"Amma al'adarmu ma bata aminta da hakan ba"
"To addini ko al'ada wanne ka zaɓa"
"Mubar maganar nan please tana samin ciwon kai, ki shirya zamubi jirgi zuwa kano, amma hotal zamu sauka"
"Ni bazan kwana hotal ba kamar wata.."Dan Allah bana son musu a wannan yana yin kiji abinda nace kawai" batace masa komai ba tabisa da kallon tausayi har ya fice daga É—akin

MUSTAPHA
Jirgin karfe huÉ—u na yamma Mustapha yabi zuwa kano, Ahmad yaiwa waya suka haÉ—u a airport na kanon shiya É—akko sa zuwa gida acikin mota suna tafe ba wanda kewa wani magana can dai Mustapha da shirun Ahmad ya damesa ya É—ago ya kallesa suka haÉ—a idanu, Ahmad kauda idanunsa yayi yana kallon kwalta batare daya ce komai ba
"Duk haushi na kuke ji ko?" Mustapha ya tambayi Ahmad yana kallon sa, Ahmad dake tuki da hannun daman shi yayinda É—ayan hannun ke tallafe da kansa batare da ya kalli inda Mustapha yake ba yayi kamar baiji abinda ya ce ba can dai yamaida masa da
"Rayuwarka ce fa Yayanmu kayi duk yanda kaga dama kawai dai inajin haushin ka ne daka saki Aimanah inda ace iyayanmu basuda fahimta mai kake tunanin zai faru da tuni zumunchi ya ɓaci"
"Na rantse da Allah Ahmad ban saki Aimanah ba, hauka nayi da zan rabu da farin cikina" wani kallo Ahmad yaiwa Mustapha kafin ya furta
"Ga takarda nan raÉ—au da rubutunka ai baza'a maka karya ba"
"Ahmad inma na saki Aimanah ai ba da sani na nayi ba, kariga da kasan komai kasan asiri gaskiyya ne ni kaina yau dana dawo mutum nai mamakin abinda naiwa Aimanah ganin abin nayi kamar a mafarki ni ban san ma da wanne ido zan kalli Mah da Aimanah ba"
"Da idanun da kake ganin kowa ka azabtar da yaran nan baka ga Mamana Islam yanda ta koma ba, olsa typoid maleria duk ita kaɗai Allah ne yayi tanada nisan kwana Allah yakai Shaheed gidan yatawo da su watanta guda a hospital sannan ta warware har yanzu batada wata cikakkiyar lafiya olsa tariga da ta taɓa mata zuciya" zaro idanu Mustapha yayi yana kallon Ahmad,
"Ahmad kaini school É—in su naganta dan Allah wayyo ni kaico"
"Shaheed yatafi É—akko su mu karasa gidan kawai" shuru motar tayi ba wanda ya kuma magana har suka karasa gidan, sun tarar Ammi ta dawo faÉ—a sosai taiwa Mustapha kan abinda yafaru ta nuna masa mihimmancin addu'a da azkhair taku ce lalle ya je har gida ya bawa Mah da Daddy hakuri, harya mike zai futa zuwa gidansa sai kuma ya koma ya zauna yana kallon Ammi idanunsa suka kawo hawaye
"Ammi ya aure na da Aimanah?"
"Aure ya rigada ya mutu Mustapha, Aimanah yanzu ta zama ba matarka ba, ban kuma lamince ka koma mata ba ka barta ta sami wani ta aura kaima ka nemi wata Mustapha yara dai Allah ya raya zan rike su a waje na"
"Ammi shikenan na hakura da Aimanah, Ammi zuciya ta bazata iya jure wannan hukuncin naki ba"
"Nariga na zartar da hukunci bakai ba Aimanah bazaka ɓata mana zumunci ba nida yayata muzo muna jin haushin juna, auran zumunchi ma an daina sa a family gaba ɗaya kowa ya nemo a waje" tana gama faɗar haka ta mike tabar wajan, Mustapha damuwa kunci gaba ɗaya suka mamaye zuciyarsa ya wuce gidansa ya buɗe ɗakin Aimanah ya kwanta ya saki wani kuka mai sauti, kirjinsa yaji ya masa nauyi shikenan shikenan shida Aimanah har abada yanaji yana gani zata auri wani ba shi ba
"No wallahi bazai yuwu ba, zuciyata bazata ɗauka ba, wayyo Aimanah Rayuwata Farin cikina Kaunata" ya jima nan kwance shuru yakasa taɓuka komai.

SUMAYYA
Sosai take kuka a mota har suka karasa katsina Allah yasa da kuÉ—i a jakarta harma da ATM card É—inta duka a ciki, sosai hankalinta ya kuma tashi dataga halin da Amarya ke ciki ta rame tai baki sosai daga ka shiga gidan kasancewar É—akinta ne farko inka shigo zaka fara jiyo wari da É—oyin da take, matar dake kula da Amarya daman ta gaji neman hanyar barin aikin take tana ganin Sumayya tazo ta gudu aka bar Sumayya da aikin kashi da fitsarin Amarya idan tana gyarata haka zata toshe bakinta da face mask inta gama tayita kwara amai dama ga cikin jikinta kafin wani lokaci itama Sumayyan ta kwanta ciwon laulayi,
Chapter 59 · 0% Book details