← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 62

Sashe 57

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Kazo ka zauna kaci abinci sai kaje ka kwanta ka huta" Mom tafaÉ—a tana kallon Yasar daya kafe Aimanah da kallo,shafa kansa yayi kana yaja kujera ya zauna,
"Ummu kinci abinci" Aimanah tayi murmushi batare data ce komai ba, Anty Ramla da Moha suka kalli juna suka fashe da dariya, Aimanah gaba É—aya ta kasa sakewa idanun Yasar take ji a ko ina na jikinta, bata wani ci dayawa ba ta mike zuwa É—aki
"Ummu ki tsaya na baki habbatus sauda ki turara, sannan ki maida hankali sosai wajan yin azkhar na safiya da maraice ki yawaita karanta kur'ani kina kuma yawan saurara a wayarki"
"Batada waya ai" Anty Ramla ta faÉ—a tana kallon Yasar
"Bari inna fita anjima gaida gwaggo mariya zan taho mata da waya"
"Da wuri haka" Moha yafaÉ—a yana dariya
"Kasanmu a lamarinmu ba ɓoye ɓoye, sak muke tafiya ba kwana kwana"
"Yanzu dai so kake kace kaga mata"
"Ta aure ma insha Allah" ya maidawa Anty Ramla martanin maganarta
"Tana dai da mijinta, kajira kaga yanda zata kaya" Mom tafaÉ—a tana kai lomar abinci bakinta
"Mom tariga tayi idda fa, ba wata uku tai a gidan nan ba"
"Hakane tayi idda yau kwana biyu kenan datai wanka, amma dai kabi a sannu karka zurma
"Mom nafa riga na shiga irin sosai É—in nan" yafaÉ—a yana dariya, Barci Yasar yayi na awanni sai yamma yatashi ya sake wanka ya fita ya zaga su gaisa da yan uwa, sai bayan sallar insha yadawo a hanyarsa ta dawo wa ya tsaya babban shagon sai da wayoyi ya saiwa Aimanah waya Infinix hot 50 pro, da sabon layin da yayi regester da kansa, lokacin daya dawo gaba É—aya suna zauna a danning ana cin abincin dare
"Mom shine ba'a jira ni ba"
"Ina kuwa zamu jira ka Yasar, ka sani dai dokar Mom ce in lokacin cin abinci yayi ba a jiran wanda baya nan inya dawo ya ci shi kaÉ—ai"
"Ok naji, Ummu zubamin abinci kamar wanda zaki iya cinyewa" Dariya Aimanah tayi ta soma zuba masa abincin cikin sanyi jiki,
"Yawwa barshi haka ina zan kai wannan abincin in da ina cinye kamar wannan aida tuni nafi haka kiba, Mom dafa sai dai a kara girman kofar shugowa"
"Yasar ka barni naci abincina karna kware kai wai dole in kana waje sai kasa mutum dariya"
"Mom nafison kullum na rinka ganin fuskarku wasai ba damuwa" Mom dai batace masa kanzil ba harta gama cin abin cinta tsawon mintina suna nan zaune a wajan, Aimanah ita ta fara mikewa zata bar wajan, Yasar ya jawo ledar daya ajje kasan kujera ya mikewa Aimanah
"Ummu ga wayarki kamar yanda na faɗa maki, ki buɗe ta ki saita komai zamuyi waya cikin dare" hannu Aimanah tasa ta karɓa tareda masa godiya,mikewa Mom tayi
"Mom gashi"
"Na gani Aimanah Allah yasa albarka"
"Ya Moh kaga yabani waya a tayani godiya"
"Dai dai Allah yasanya alkhairi
"Anty Ramla kinga" Aimanah ta faɗa tana mika mata ledar, Antyn ce ta zaro wayar daga kwalinta ta buɗe ita tasa mata screen gard ɗin da wayar tazo da shi, tasa sim ta kunna wayar kana tace taje ta sata a caji, Aimanah ta karɓa ta juya zata bar wajan Azinatu taja tsaki tareda bangaje ta tabar wajan, Aimanah murmushi tayi kawai ta wuce ɗakin Mom, Aimanah cikin barci taji wayar na kara, cikin magagi ta ɗaga kiran
"Ummu bakiyi barci ba" taji muryar Yasar ta doki kun nan ta, cikin magagin barci ta ce
"Barcin fa nake" dariya sosai Yasar yayi
"A barcin kike magana kenan? wastsake dan magana zamuyi dake ta fahimta"
"Yasar barci nake ji sosai mubar maganar sai da safe"
"Bazan iya ba Ummu, Kaunarki ta shige ni sosai tsoro nake kar nayi jinkiri wani ya rigani samun fili a zuciyarki"
"Filin zuciyata babu kowa a ciki Yasar sa Yasar, ba yanzu ba banan kusaba bance bazan kuma bawa wani fili a zuciyata ba amma dai ba yanzu ba" É—if ta katse kiran tareda saka wayar a jirgi ta maida kai ta kwanta, Ahankali ta furta
"MUSTY" share hawaye tayu tareda runtse idanunta hawaye naci gaba da fita,
Yasar naushin fulon daya ke kai yayi da karfi yana faÉ—in
"Ya Allah" haÉ—e da sakin numfashi, Moha gyara kwanciya yayi tareda buga tsaki
"Ka takuramin fa Yasar kazo kana waya murya kasa kasa kamar munafiki, yanzu kuma ka fara kai naushi," filon sa ya É—auka ya sauka daga gadon ya koma saman doguwar kujera yasa fulon ya kwanta yana mita
"Gara nayi nesa da kai kafin ka kai min duka" Yasar dariya kawai yayi baice komai ba shima ya mike ya shiga bathroom ya ɗauro alwala yazo ya tada sallar nafila, bayan ya gama jero nafilfili daya saba yi duk dare yai addu'a, sannan ya mike ya sake kawo wata raka'a biyun yai addu'ar istikhara na neman zaɓin Allah" yasake addu'o'i ya kalli agogo yaga huɗu da kwata hakan yasa ya fita zuwa masallaci, can ya zauna yana karatun kur'ani har akayi sallar asuba yadawo gida shida Moha wanda yabisa masallacin bayan anyi kiran sallar asuba, yana ganin Muhd ya shiga ɗakin Mom su gaisa shi kuma ya wuce zai kwanta yana cewa Moha
"Agaida min Mom sai nayi barcin safe zan zo mu gaisa kafin ku wuce kano"
"Ai dama ka zo kun gaisa É—in a mota zamu tafi karfe bakwai zamu fita kaga sai kayi barcin sosai" juyowa Yasar yayi suka shiga É—akin tareda Muhd, Mom na bathroom Aimanah na zaune saman dadduma tana azkhair, sallamar da sukayi ta amsa ta É—ago kai ta kallesu
"Yaya Moha barka da safiya anta shi lafiya"
"Lafiya kalau Aysha ya kika tashi"
"Aysha kuma yaya Aimanah dai, wannan babban sunane sunan mamata"
"Ummu ina kwana tunda ni baza'a gaida ni ba" Yasar yafaÉ—a yana zama É—an nesa da ita kaÉ—an,
"Ni na isa na ki gaida yayana, barka da tashi ya gajiyar hanya"
"Gajiya tabi lafiya Ummu," yaÉ—an matsa kusa da ita ka É—an yana magana kasa kasa yayin da kan Aimanah ke cikin kafafuwanta fuskarta É—auke da murmushi har Mom ta fito daga bayi kallo É—aya taiwa Yasar É—in ta fita daga É—akin tana jin tausayin É—an nata yanda so yai masa mummunan kamu, a kicin ta tarar da Anty Ramla nata kokarin haÉ—a abin kari dan ganin sun fita da wuri
"Sannu Ramla, Allah ya maki albarka yabaki yaran da zasu faranta maki fiye da yanda kike min Ramla"
"Amin Mom" Ramla ta faÉ—a tana murmushi, kafin bakwai sun gama shiryawa zaman break kawai akai shima a gurguje akai dan ganin an fita da wuri, Ramla ta fito da jakar kayan Aimanah suka fita compound inda Moha ke cikin mota yana jiran fitowarsu, ahankali yake takowa har zuwa inda su Aimanah ke tsaye itada Mom
"Mom yanzu da ban fito ba tafiya zakuyi" Mom mota ta shiga bakinta É—auke da addu'ar abin hawa bata tankawa Yasar ba,
"Ummu dan Allah ki rike min alkawari insha Allah gobe zan zo kano muyi magana ta gaske"
"Sai kazo amma zaka iya auran bazawara mai Æ´aÆ´a uku" zaro idanu Yasar yayi yana kallon Aimanah cikeda mamaki
"Wai dan Allah da gaske, nayi farin ciki daya kasance munada yara zan aureki a haka zan kuma haÉ—a da yaranmu na rike ina maku fatan sauka lafiya"
"MOM Allah ya tsare hanya" yafaÉ—a sanda ya leka kansa cikin motar"
"Yasar kana ɓata mana lokaci fa, ance kazo a tafi da kai kace ba yau ba amma ka tsare mu da zance"
"Lafafa min Ya Moha a sauka lafiya" yafaÉ—a yana rufe murfin motar yaja baya yana kallon Moha yaja motar suka fita daga gidan, gwauron numfashi yaja ya jima nan tsaye a wajan kana ya koma ciki ya koma barci, Tafiyar awanni biyar da wani abu yakawo su Aimanah garin kano ita ke nunawa Moha hanya bayan sun shigo kano har suka karasa gidansu dake gadon kaya,
Chapter 57 · 0% Book details