← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 62

Sashe 47

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin wani zuba mana idanu kamar na mujiya jaka ake nema a gidan nan ba'a ganta ba, shine nace a bincika ɗakin kowa dan a fitar da ɓarawo, nagodewa Allah an bincika ɗakina bata nan shuyasa na rako sa a bincika nan"
"Ok bisimillah" Aimanah tafaÉ—a tana matsawa suka shiga É—akin sosai, bin ciken farko saiga katuwar jakar mai shake da manyan kuÉ—aÉ—e a cikin wardrove É—in Aimanah, wacce tayi tsuru tsuru tsoro duk yakamata ganin abinda bata zata ba
"Ka gani ko kaga gaskiyya ta fito ko, shiyasa nace a bincika ko ina, oh ana zaune da katuwar ɓarauniya bamu sani ba," Mustapha baice komai ba ya rungumi jakar kuɗi zai fita da ita
"Wai kana nufin baza kace komai ba, kana ganin wannan babban zunubin da ta aikata sata fa"
"Maizan ce Sumy tunda sun fito ai shikenan"
"Au haka zakace ai wallahi bazan zauna da ɓarauniya anan ba wataran ni ta sace ni yau yau ɗin nan zata bar wajan nan daga ita har ƴaƴanta amaidata can ɓangaran bayan nan ta karata acan"
"Duk yanda kikai dai dai ne" Mustapha yafaÉ—i haka yasa kai yafita daga É—akin, watsi Sumayya tafara yiwa Aimanah da kayan sawarta dana yara tana watso su waje
"A fita afita a koma can aci gaba da sata" Aimanah na hawaye ta fara tsintar kayanta ta É—ago ta kalli Sumayya zuciyar Aimanah ta rauni kawai ta fashe da kuka, kafafun Sumayya ta rike
"Sumy na roke ki da girman Allah da azabar da kike gana mana gara kisa Mustapha ya sakeni na koma gaban iyaye" Sumayya ta kece da mahaukaciyar dariya tana kallon Aimanah
"Saurin me kike ai ana gab da yin hakan zan saka ya baki takarda mai É—auke da saki uku ta yanda ke da zama da shi har abada amma sai bayan na gama shayar da ke zumar azaba a gidan nan" Sumayya na gama faÉ—ar haka ta juya ta wuce ciki ta rufo kofa, Aimanah kayanta ta É—iba zuwa bayan wajan yayi datti sosai sabida da Salman É—an gwaggo ke zaune a wajan babban falo ne sai É—aki É—aya mai É—auke da toleit a ciki, kayanta ta jera a wardrove ta zauna gefan karamin gadon taja tagumi tana hawaye Tasnim na goge mata, Islam da Aslam na kwance lamo a jikinta,
Aimanah duk yanda taso ta gayawa wani halin datake ciki saita kasa kamar wacce aka rufewa baki, hakan yasa ta tsananta ibadarta barcin daranta ya koma rabi cikin dare take ta shi tayi sallah tai kuka ta roki ubangiji ya fitar dasu daga halin da suka shiga, ko kaÉ—an batajin haushin Mustapha sai ma tausayinsa datake ji daman can tasansa da rauni musamman wajan azkhair sau tari ko addu'ar kwanciya barci ita ke masa ta shafa masa a jikinsa bare kuma azkhair da ada intayi magana sai yace aikine ya masa yawa zai yi, tasani wasa da azkhair da karatun kur'ani da yake shiya jawo masu komai, sabida ta tabbata Sumayya asiri tayiwa Mustapha kamar yanda tayi a baya sanda zata aure sa,

Sumayya shewa sukayi da kawayanta suka tafa
"Gaskiyya lina ina godiya da kuka É—orani a hanya kuga yanda nadawo wata big girl da na tsaya kaina zai kulle, ai ingaya maku a gidanna mulkina nake yanda naga dama komai na Muatapha yanzu yadawo nawa harta motar Aimanah yanzu ni nake hawa da kaina na koma wajan malam kibauu nasa ya hana waÉ—an can mutanan dawowa nace a janyw masu hankali daga nan bare su dawo suga abinda ke faruwa atafi a lalatamin aikina yanzu ba gashi ba inata shan sharafi na, boka ya tabbatar min da Aimanah bazata iya barin gidan nan ba inhar ma magen karkashin gado na kunce ba," tafawa suka daÉ—a yi tareda shewa, Aimanah komawa tayi ta jingina da bango tana hawaye
"Mage mage a karkashin gado ya ilahi" komawa Aimanah tayi da baya daman Islam ke kukan tana jin yunwa ta zo ta roki Sumayya ta taimaka ta bata abinci ashe rabon zata jiyowa kanta ne, wayar maman hanif ta kira mintina kaÉ—an tsakani Hanifa babban É—iyarta ta kawowa su Aslam abinci, Aimanah zuru tayi tana kallon yaran ganin yanda suke cin abincin hannu baka hannu kwarya, share hawayanta tayi tausayin yaran suka kamata tamike tana jin zuciyarta na mata wani irin zafi

zagayan neman mafuta a rayuwarsu tafara yi, kakarin aman data jiyo daga bayanta yasa ta juyowa taga islam ce keta amai da sauri ta rungomo yarinyar jikinta tana mata sannu, wajan datai aman Aimanah ta gyara, kafin wani lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufe islam sai surutai take,
"Wayyo Ammi zan mutu afaÉ—awa abie banda lafiya a kaini asibiti wayyo Ammi cikina" islam ke faÉ—a da muryar yara
"Yi shuru islam bazaki mutu ba, zakiji sauki Aslam ne ya mike da gudu ya fita ya zagayawa wajansu Sumayya bako sallama yafaÉ—a É—akin kai tsaye wajan Abie É—insa yaje ya ruko hannunsa
"Abie islam bata da lafiya zo kaje ka ganta" Mustapha saroro yayi da idanu yana kallon yaran yana son tina inda yasan sa
"Kai maye baza shi ba, futa ka bamu waje É—an iska mara tarbiyya" Sumayya ta faÉ—a a zafafe kamar tana magana da sa'anta, Aslam baya yayi ya fita daga sashin yana legen Mustapha wanda shima yaron yake kallo wanda yake hango fuskarsa a fuskar yaran
Islam tasha wahala matuka maman Hanif ta kawo mata magani harta sami sauki, yau Murja garin abuja suka sauka dawowar su kenan daga dubai jirgi ya sauke su nan abuja, hakan yasa ta cewa Alhaji Jamil ya kama masu ɗaki a hotal su kwana zataje gidan yayarta su gaisa, texz ya ta shiga zuwa Yaya Mustaphan cikeda ɗokin ganin yayar tata da yayanta harma da yaya Aimah, hannu biyu Sumayya ta karɓeta suna hira kan mahaifiyarsu
"Anty Sumy yanzu wai ba wanda mama take jin tsoro yamata magana ta daina harkar datakeyin nan"
"Babu Murjana iyayanta ne to suma sun zuba mata idanu duk da na tabbata basu san mai take aikatawa ba, duk da daman can bata É—auke su da mihimmanci ba, addu'a kawai zamuyi mata" kai kurum Murjana ta gyaÉ—a can ta ce
"Yanaji gidan shuru ko Yaya Aimah bata dawo daga aiki ba" dariya Sumayya tayi ta ruko hannun Murjana suka fito can baya karshan gidan Sumayya ta tura kofa suka shiga Aimanah ce zaune saman carfet itada yaran data rungumo su duka a jikinta, Murjana kallon Aimana tayi ta juya ta kalli Sumayya dake ta murmushi
"Murja yaushe kika zo?" Aimanah ta tambayeta a sanyaye
"Yanzu" Murja tabata amsa tana bin É—akin da kallon mamaki, ta juya ta kalli Sumayya da har sannan fuskarta ke shimfiÉ—e da murmushi
"Anty Sumy ban gane bafa mai Aimanah take anan wajan da ya dace ace yan aikinku ke wajan"
"Itama yanzu ai batada maraba da yar aikin" Sumayya ta faÉ—a tana jan hanun Murjana dake kallon Aimanah wacce ke goge hawaye suka fita
"Sakar min hannu Sumy ki sake ni, mai abinda na gani yake nufi"
"Kin rigada kinsan komai Murjana wani malami na samu mai zafi ina gaya maki hmmm ba'acewa komai, aiki yayimin yanda nakeso, kema in kinason kama mijinki kizo na rakaki kiga yanda ake aiki kamar yankan wuka"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, la'ilaha illa anta subahanaka inni kuntu minal zalimin, maine haka wai Sumayya kinyi hauka ne, ina zaki kai wannan zunubin mai girma haka"
"Istigifari ai bai bar komai ba murjana inaka aikata ba dai dai ba saika tuba ka koma ga Allah"
"Sumayya banso ba banso kika komawa harkar asiri ba duk karyan banza ce da É—aukarwa kai zunubi kisani Allah baya yafe laifin wani daka cuta, Anty Sumy kin cutar da masoya Allah bazai barki ba, kuma da ikon Allah saina tarwatsa komai" Murjana na gama faÉ—ar haka tayi baya ta koma wajan Aimanah da har sannan ta sameta tana hawaye
"Yaya Aimanh bar hawayan nan insha Allah komai zai wuce yanda na tarwatsa wancan asirin haka yanzuma insha Allah saina tarwatsa komai, nasanki ada kinada ibada kici gaba karki daina tabbas nasan ibadarki tasa kika tsaya iya wannan halin, kaico kaicon yaya Mustapha da bai É—auki azkhair da mihimmanci ba shiyasa daga an masa abu yake saurin kama sa kici gaba da addu'a Yaya Aimaah, ko zaki bini mu gudu na maida ke kano"
"Bazan iya nayita yunkurin yin haka amma sai naji na kasa barin gidan zan so ace zan iya fita daga gidan nan da tuni bana cikinsa" mikewa Murjana tayi tana gyara zaman jakarta dake saɓe a kafaɗarta
"Gobe zan dawo Yaya Aimah da ikon Allah saina fiddaki daga wannan gidan" ɗagowar da Murjana tayi taga Sumayya na tsaye jikin kofa tana kallon su, sa kai Murjana tayi ta raɓa ta gefanta ta wuce tana gafda fita daga gidan taji Sumy ta kira sunanta ta juyo tana kallonta
"Zaki fitar da ita ko? to gara ma kiyiwa gidan nan kallon karshe keda sake shigo sa har abada" juyawa Sumy tayi ta koma ciki, Murjana jikinta yayi sanyi tana mamakin Sumy,
Sumy na komawa É—akinta malam ta kira ta sanar mata yanda sukayi da Murjana sannan tace tana so yakara mata aiki sosai kan Mustapha taga yafara mata musu kwanan nan
"Dole zai maki masu kishiyarki na tsaye kan addu'a bamuda wani abu da zaiyi tasiri a kanta, kici gaba da rikon magen nan ruhin haÉ—e take da ruhin Aimanah daga randa kika yi sake magen nan tabar cikin gidan daga ranar Aimanah bazata sake kwana a gidan nan ba, fitar Aimanah daga cikin wannan gida dai dai yake da tarwatsewar komai da kikayi, ga tukunya nan mun saka aljani dundurusu ya ajje maki a kofar É—akinki ki fito ki É—auka ki mata ma ajjiya mai kyau karta fashe inta fashe akwai matsala maganar kanwarki kuma yanzu zan mantar da ita komai" sallama sukayi da boka Sumayya ta fita ta É—auki tukunyar a hankali tasa can wani É—an lungu dake cikin É—akinta ta adanata
Kamar yanda malam yafaÉ—a hakance ta faru Murjana kafin ta karasa hotal É—in da suka sauka ta manta da wata Aimanah bare kuma alkawarin komawa datayi mata
Chapter 47 · 0% Book details