← Book details Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 62

Sashe 51

Aimana Mami Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

GIDAN MURJA
Alhaji Jamil da yaransa uku Jannart Labiba da Ansar zaune bisa danning, yayinda Murjana keta zuruftu daga kicin zuwa danning area É—in sai da ta gama ajje komai kana ta zauna, kallon yaran tayi da murmushi a fuskarta ta ce
"Baza kumin sannu ba" lokaci É—aya suka haÉ—a baki suna faÉ—in
"Momy sannu da aiki" dariya tayi tana kallon Alhajin daya ke ɓata fuska kamar wani karamin yaro
"Kaifa Man wani bin in kana abu sai kace Ansar" ta faÉ—a da murya kasa kasa,
"Inajin yunwa sosai, yau banci abinci a kasuwa ba" da sauri taja plate ta soma zuba masa abincin farar shinkafa ce sai farar doya da miya, sai haÉ—in salad gabansa ta ajje plate tana faÉ—in
"Bisimillah" kansa ya É—ora saman kafaÉ—arta murya kasa kasa ya ce
"Nifa ke zaki bani"
"Yara na nan fa" itama ta faÉ—a a hankali
"Ki basu nasu su wuce wajan mamansu suci acan"
"Kasandai ba sakewa zasuyi a can ba ga nanny bata nan kawai dai ka daure kici da kanka" mikewa yayi zai bar wajan tasa hannu ta ruko sa
"Jannart zubawa kowa abinci a plate kuci" ga lemu nan kowa ya ɗau wanda yake so amma Ansar kar abasa mai sanyi" taɓe fuska Ansar yayi kamar zaiyi kuka murja taja kumatunsa tana murmushi ta ɗauki plate ɗin data zubawa Alhaji abinci suka zauna can falo ahankali take basa abinci a baki yanata zuba mata shagwaɓa kamar wani karamin yaro, saida ta tabbatar ya ishe sa sannan taci kaɗan, ta koma wajan yaran data soma jiyo hayaniyar su
"To yaya ne, zaku fara faÉ—an ko?"
"Momy Ansar ne fa wai sai ya sha lemu mai sanyi kuma kin hana abasa sabida yana mura"
"Naji ku wuce to Jannart ki tabbatar kin tayasu sunyi homework ke kinga munyi naki É—azu in kun gama ku kwanta barci zan shigo É—akin kowa yayi addu'a ku kuma kunna karatu a mp na É—akin ku kisa bakara" kai Jannart ta É—aga alamar to har sun soma tafiya suka jiyo suna mata bye bye Ansar da gudu yadawo ya rungumeta ya sumbaci kuncinta ya ce
"Goodnight Mom" Murmushi Murjana tayi tana kallon yaron da yayi gaba da gudu, hawayan dake zuba a kuncinta taji ana share mata ko tantama batayi ba tasan Alhaji Jamil ne hakan yasa ta faÉ—a jikinsa ta fashe da kuka
"Shikenan banda rabon ganin ɗana a duniya shi kenan bazan sami soyayyar da yara ke wa uwarsu ba? shikenan bazan taɓa haihuwa ba har abada? bazan sami ɗan da zai kula dani ba bayan na tsufa, kaicona kaicona nayi nadama Allah na tuba ka yafemin, Allah kabani hakuri da juriyar cin wannan jarabawar da kamin ya Allah" sosai take kuka mai taɓa zuciya, Alhaji Jamil ma hawaye ya share yana buga bayanta a hankali alamar lallashi
"Yi shuru Wife dan Allah ki daina kukan nan gasu Ansar nan insha Allah zasu maki dukkan wani abu da É—a kewa uwa" bata tsaya sauraron saba taci kukanta ta koshi yanata aikin lallashi, sai da tai shuru suka wuce É—akinsa har sunyi shirin kwanciya ya ce
"Mako guda ya rage fa tafiyarmu India"
"Bazani ba, ka tina yanda akayi a tafiyarmu indunusia irin tashin hankalin da akayi da matarka dan haka wannan karon ka tafi da ita ni ina nan zan kula da yara" wani kallo yamata kana ya ce
"Bazani da itan ba, dake naga damar tafiya kuma da ke zan tafi" jiki sanyaye Murjana ta kalli Alhaji daya kwanta ya juya mata baya agogo ta kalla taga tara saura minti biyar na dare
"Gaskiyya Abban Ansar ba haka ake ba, yanda na sani in anyi tafiya da wannan in wata tafiyar tazo da waccan za'a tafi sai dai in ita tace ta yafe a tafi da wata" afusace ya mike yaja hannun Murjana zuwa sashin Rahila, kofar ya buÉ—e a fusace falon shuru ba kowa hakan yabasa damar buÉ—e kofar bedroom É—inta, abinda yagani ya masifar É—aga masa hankali bama shi kaÉ—ai ba har Murjana wacce ta zaro idanu tana salati, salatin da Murjana tayi shiya dawo da Rahila da Hanne hayyacinsu da sauri suka ja bargo suka rufa, Rahila na zare idanu ganin Alhaji Jamil tsaye kamar wani sakago ya saki baki yana kallon su da kyar ya iya saita kansa ya ce
"Daman abinda kike aikatawa kenan shiyasa kike tara mata a gidana, kike kin bina wani waje ina can na saki baki ashe ke ga abinda kike aikatawa, kin cuci kanki Rahila keda Allah kin aikata babban zunubi Rahila kije dan kanki na sake ki saki uku bake ba yarana na haramta miki su har abada ki nesa da gidan nan ki nemi inda zaki" juyawa yayi ya fita yanajin sa wani saroro kamar iska zata É—aga sa sama, kuka ya sha sosai daran ranar, Murjana ko É—akinsa bata koma ba É—akinta ta koma itama ta sha nata kukan takaicin wannan zamanin da mata suka lalace,
Rahila sanda Alhaji Jamil ya furta mata kalmar saki ba karamin tashin hankali ta shiga ba fiye dana ganinta da yayi kwance da wata hakan yasa ta fashe da kuka, shikenan ta kare mata ina zata iyayanta gaba É—aya sun rusu da gidan Alhaji jamil ta dogara sai kuma aikin datake wanda bata wani tara abin arziki ba
"Ki daina kukan nan dama ma yabaki yanda zaki sakata ki wala kiyi harka yanda ranki ya ke so munada kungiya ta mata yan less zamu saka ki a ciki zaki samu kuÉ—aÉ—e sosai zaki fantama mota sai wacce ranki yakeso akwai alhazan birni zaki iya auran É—aya daga ciki wanda shi ba mace bace a gabansa shima yanada tasa harkar a gabansa ma zaki iya yin duk abinda ranki yaso da mace bazai ce maki komai ba si dai kawai yayi aure ne dan kada a zargesa in anga yana zaune ba aure, gobe ne ma zamuyi taronmu na shekara a kaduna ki zo mu tafi gidana inada mata kala kala acan da suke zaune" Rahila mikewa tayi ta sitirta jikinta ko wanka ba wanda yayi haka suka bursuna kaya suka fita a gidan a motar Rahilan,
Amarya rai ta ɓata ganin Hajiya Hanne data ce mata taje jigawa sai gobe zata dawo, amma sai gata yanzu da tsohon daran nan harda guzurin wata matar
"Daman wai ba jigawar kika tafi ba?"
"Naje daga can ma nasamo mana wannan"
"Ko dai kikaje wajanta ba, waton ni kin barni a nan kika ajje ni kin hanani holewa da kowa kince ni taki ce ke kuma kina bin wasu, nan haka da mukaje habuja gidan Sumayya daga ganin wata sai da kika bita kika kwana da ita, to gaskiyya nima fita zan na hole yanda raina ke so"
"zaki iya yin hakan ai" Hanne tafaÉ—a tareda jan hannun Rahila sukai sama, saroro amarya tabisu da kallon mamaki can kuma tayi kwafa ta koma É—akinta,
Chapter 51 · 0% Book details