← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 32

Sashe 32

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Mamy ta kama yaro tarike sosai tanajin soyayyar yaran har cikin ranta, Take taji soyayyar Moopy mai girma tana ratsa ko ina najikin ta

Tsohuwa sai murna take tayi DA.

Ammi na gefe batace komiba sai murmushi take.

Kwanan su d'aya aka sallameta ,Mai jego da Baby na cikin koshin lafiya.

Gidan ta akawuto da ita dan tasamu kulawa daga mahaifiyar ta.

Tsohuwa tama Ammi magana da hudu ba akan ta cire kunya ta kula da yar ta tinda dai babu mai tsayawa wurin.

Ammi tace mata bamatsala insha alylah.

Irfam ranshi ya b'aci sosai da aka rabashi da matarshi, Washe gari yazo gidan Ammi ya isketa tanama yaro wanka.

Bayan sungaisa ya shige d'akin Moopy ya isketa tana d'aura towel za ai'mata wanka .

Rungumeta yayi" yace shine kika bari akarabamu ko?

Tace aa muna tare har abada.

Wake maki wanka yasake jefe mata tambaya?

Moopy tace inna Asibi ce.

Ido ya Zaro yace aikuwa bata isaba daga yau zandinga miki.

Tintana ganin abun kamar wasa har daga baya ta gane dagaske yake, DA kanshi yakamata yamata wanka yagasata sosai kana ya fiddota.

Haka suketa rayuwa harta iya da kanta.

Ranar suna Baby yaci sunan mahaifin Moopy inda suka samishi suna(ABUL KHAIRI)littafina na gaba insha allah.

Anci ansha inda yam.uwan irfam suka musu kara sosai .

Ammi ta sha kukan tinowa da danginta da batason inda sukeba. Da yanzu dasu za asha hidima.

Bayan taro ya watse Amaryar jego tasamu kyaututuka da dama daga dangin mijinta.

Ammi ta zage tana bama yarinyar ta kulawa, Mamy ma ba abarta abayaba tana basu guduncmuwa tinda tason basu da kowa

Aranar dasuka gama wanka Irfan yakwashesu sai gida.

Inda suka bude sabuwar rayuwa mai cike da in'ganci.

Bayam shekara biyar.

Aka sanya bikin Ammar da Amina, inda su Moopy suka taka rawar gani sosai komi sune kan gaba.

Shekara na zagayowa meenah ta haifo yarta.mai kyau inda taci suna Ummul KHAIRI suna cemata.khairi

Kullum rigimar ABUL KHAIRI akaishi wurin KHAIRI ya ganta.

Irafan yace miyasa ka keso a'kaika wurin ta.?

Cike da yarinta yace b6aby nace.

Dariya sukasanya suduka Moopy" tace abunda kake cewa shine yace shima".

Dariya sukayi suka shirya suka tafi gidan Amina su duka.

Acen suka wuni da zasu taho Abul khairi kuka yasan ya sai an'barshi wurin Baby shi.

Dole suka barshi suka musu Sallama suka tafi...

Suna shigowa Irfan yace Baby nah muje sama musamo wani Baby tinda wannan ya gujemu.

Harara shi Moopy tayi tace bazanjeba ,Bakace nagama haihuwa ba.

Kanta an'kare yasureta sukayi sama suna dariya.....

TAMMAT BI HAMDULILLAH.....

I miss you mutanena 🥰🥰
Chapter 32 · 0% Book details