← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 32

Sashe 26

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sati biyu Amina ta falfafo ta samu lafiya tayi fress ita da Aminu, sunyi mugun kyau dan sosai Irfan ke kula dasu, dan haka yau suka yanke shawarar kaisu gidan moopy da daddare....✍️
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘💘💘💘💘💘💘💘
ZAMAN TASHA
54&55

Kwanon shi ya sake juyo masu yayce ku kallah Ammi ce zaune tagama sallah sai kuka take tana rokon Allah ya yafemata akan kuntatawar da tayiwa yar cikin ta,cikin kukan tace yau gashi duniya ta juya man baya, way'anda na fifita akan ta gashi bako d'aya gabana, Allah ka yafeni kasanya in had'u da ita badan halina ba.

Tsohon nan yayi murmushi tare da cewa ku ya kuke gani a'mayar mata tinaninta yanzu ko abari sai yar fulanin ta gane kuran ta?

Ammar ya'ce gaskiya kawai a'barta sai gaba, ni yanzu nafiso inji miye a'lakar Daddy da Moopy.

Tsohon yayi dariya ya'ce" karka wani damu zakaji, amma kason ubanka badai yanzu zai isoba ko, in kuma kanaso ya bayyana a'tsakiyar palon shida kakar ku yanzu zakuganshi..
Ammar ya bud'e baki zai magana Irfan cikin k'agara ya'ce" su bayyana dan Allah Malam.

Kansuce komi sukaga Moopy ta tashi a'hargitse tana bin jikinta da kallo, Ammar ya duba ba tsoho ba alamun shi Irfan ma haka, gogicewa sukai suduka ya suna magana zasuga ya b'acce! kansuce komi sukaji tsohuwa ta turo k'ofar da karfi hankalinta tashe ta'ce" kai dan ubanku ina ne band'aki ? Wallahi yau Musa drive ba kuga tukin da yayi da niba .

Cikin mamaki Ammar ya fara k'ok'arin magana sai ga Daddy da gashi sai yar jallabiya yar guntuwa, a'dimauce shima yashigo Moopy sai binshi da kallo take ta'ce" Alhaji kaine haka da daddare? ta fara k'ok'arin tashi, da sauri Irfan ya kamata ya d'auki dan kwalinta yana k'okarin dauramata, ido ta zumai shima idon ya zubamata duk wata tsanarshi da take- take taji ta yaye a'zuciyar ta, saima sha'awa da yabata, amma kasancewarta miskila cikin lokaci ta juya kanta kamar batason mike faruwa.

Haka ya kunduma mata d'aurin tare da kamo hannunta suje falon, su kafarajin karfin zawon da Tsohuwa keyi kamar na sabon jariricikin rawar jiki Daddy ya'ce" muje Palo naga akwai ma mutane a'gidan, haka suka mika sukayi palon saiga Tsohuwa har wanka tayi tafito kan nan nata kamar ciyawa rigarta sakale a kafad'a, Ammar ya'ce" kisa kaya mana.

Tsohuwa ta'ce" kayan uwarka! yan iskan yara k'agare kuke kuga mutum tsirara kibishi da kallo, gwaurayen banza, nason zuwa yanzu duk kunyi tsami sai an'tusamaku sabuwar a
Shayi..

Subhanallahi suka furta sudukua wata irin matsananciyar kunya takama Irfan, shikaum Ammar saurin ficcewa yayi yana Allah wadaran da halin Tsohuwa, haka tabiyosu suka fito tasamu kason carfet ta zauna tana wash shege bukar gobe sai na koresh .

Moopy idonta ya sauka akan kan nanta ido ta zaro tare da mutsutsikesu tace me? yau kuma idona gizau yakeman,wanike gani haka kamar Amina da Aminu?

Amina ta rugo ta rungumeta Aminu kuma yayi tsaye gefenta yana kallon yar uwar tashi cikin shauki, ya'ce" aunty Moopy ashe zamu sake ganinki dama?

Moooy ta fashe da kuka ta had'asu ta rungume tace ya akai kuka Zo nan?..

Daddy da ake mintsinin makoshinshi kota ina ya'ce" dan Allah Mufeeda zoki zauna gobe kwayi maganar.

MOOPY taje ta zauna tare da k'urama k'annanta ido.

Alhaji ya fara cewa to Alhamdulillah Allah abun godiya,na tafka wani baban kuskure a'rayuwata, amma ina rokon Allah da ya yafeman .

Shekara ukku data wuce.

Mahaifinki yazo wurina mukaje muka sake ganin gidan gonarki, yaceman kyanshi a'kirawo mai zanen wurin nan ya zanamaki, nace ba matsala wanda ya maku gidaje zaimaki, mahaifinki da yake mutum ne mai kula ya fuskanci ina cikin damuwa matuk'a yanemi jin ba'asi,nikuma na cemai gaskiya ina cikin damuwa matuk'a,ban boyemai ba nafara mai bayanin kamar haka.
Na'ce" malam kason fa Imran mun mai Aure, amma matarshi na k'asar waje inda yayi karatu sanadinshi yanada karfin sha'awa tin yana shekara ashirin nai mai aure, na had'asu da matar suka tafi dan matsanancin ciwon ciki yake,likitoci suka bamu shawarar AURAN dashi, to kuma É—iyar dan uwana ce wato lawal munacemai balele ma ana mahaifin Ammar, dan mu biyu Inna ta haifa dagani sai shi,sai Hajara Allah ya mata rasuwa wajen haihuwa , to bayan auranmu nida kanene shi sojane kuma a'bodar jibiya yake aiki shiyasa zamanshi ya koma cen,ya auri É—iyar abokin aikinshi mahaifiyar Ammar kenan, tinda yammar sati d'aya ke tsakanin Ammar da Irfan, shiyasa tin suna yara na an'sheshi mukaba Inna su, suna zaune a'gidanta wannashine.

Bayan Imran yakoma Sudan ya cema matarshi zai k'ara aure, ta tada hankalinta suka fara rikici har taman waya nikuma nace abun duk baikai na hakaba, ya hakura da Moopy kawai zan had'ata da Irfan tinda ya kammala karatunshi, baiwani jadaniba kasancewarshi mai biyayya, ya masu fatan ALKHAIRI daganan yanemi shawarata akan suna bukatar d'aukarshi aiki nace bakomi yayi zuwa wani lokaci yadawo kasarshi , Baban ki yayi dariya yace bakomi wallahi,yace man ina Imran din?nace dama ya jene dan ya sanar matar sakwon auranku, Babanki yace zaidawo ko shikenan ? na'ce" aa yana hanya. ya ceman ba damuwa haka Imran ya dawo bai nunamaki ba ya maku cuku-cuku kukayi tafiya dan hutum wata biyu ya d'auka har Allah yasa kuka dawo mahaifinki ya kwanta jiya duk yana kasa,r baifi saura kwanaki ba Allah yama Babanki cikawa ba, yakoma bakin aikinshi Babanki na cikin halin jinya ya roki al'farmar in aurar dake ga wanda ya dace, mafarin na hada auranki da Irfan, a'ranar mahaifinki yaji dadi sosai mafarin duk naseehar dayamaki akan kikasance mai yimin biyayya,to atakaice dai Moopy Irfan mijinki ne,ga Tsohuwa nan itace tai jinyarki bayan tafiyar wadda a'kabarmaki Inna laure, kuma gaban Tsohuwa akai komi gatanan tamaki bayani fatana ku yafeni bansanar dakuba saboda naga moopy nason aikita shiyasa kaikuma nasonka sarai Abubukar shiyaaa nashare har sai yau da dare nasamu tinatarwa..
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘💘💘💘💘💘💘💘
ZAMAN TASHA
💘💘💘💘💘💘💘💘
NA UMMY AYSHA
🅿�5️⃣2️⃣&5️⃣3️⃣

"" Da daddare Moopy na zaune cikin palonta tana ta rubutu tana lumshe ido, basai an'fad'amaba wakarta take rubuta wa! ""Su Ammar sukai Sallama shida Irfan suka shiga tare da samun wuri suka zauna.

Oyoyo yah Ammar sannu da zuwa.

Ammar ya'ce" yawwa sannu mu zakice, bakiga bani kadai bane?

Moopy tace au hakane fa! sannunku,ina wuninku, ta juya kai..

Irfan ma baiko kalleta ba ya zauna tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana bim falon dake shige da nashi da kallo .

Ammar ya amsa Tare da tambayar ba kowane...?

Moopy ta'ce" bakowa ni kad'aice, Inna Asibi ta tafi k'auye, sai gobe zata dawo...

Ammar ya'ce" da kyau" in tambaye ki mana?

Moooy ta'ce" inajinka.."

Ammar ya'ce" wani abune kikeso da muradin gani? kuma in'kin ganshi zakiyi farin ciki.?..

Moopy tai shuru zuwa cen tayi murmushi ta kad'a kai! ta'ce " Wallahi bakomi..

Ammar ya'ce koda ammi ce..?

Take jikinta ya fara rawa idanuwanta suka fara juyewa,ta fara k'ok'arin sulalowa daga saman kujera,kan Ammar yayi wani yunk'uri Irfan ya isa kanta jikinshi na rawa yafara tab'a kumatun ta, Amma ina cikin rawar murya ya'ce Ammar minai mata ?

Ammar yace yo mimukamata dai.irfan ya'ce Wallahi bakomi ko dai maganar dakamata ne,ta b'atamata rai ne?

Ammar ya'ce" mahafiyarta fa aka kirawo, sai abun yab'atamata rai,bayan shekara nawa tana neman ta ...

Dukkansu kansu ya kulle" Irfan ya sungumeta yayi d'akin dake nan palon ya a'jeta akan katifa, ya fara kwararo karatun Al'kur'ani cikin surutul Bak'ara, yi yake ba kakkautawa zuwacen ya farajin kururuwa cikin d'akin, karcet ya tashi yayi falo jikinshi na rawa, ya'ce" Ammar zo kaji suka dawo d'akin,jikinsu na rawa! kamar wasa daga bayan su sukaji murya tsohon! kasa juyawa sukai sai Ammar da yakusa yin fitsari ya'ce Baba ina kwana ina wuni...

Tsohon ya'ce wato harkun samu kusanci da ita da zaku rabani da yarinyar kirki ko.?

To ni nan ta taba d'aukar mutane ciki harda kaka ku, a'hanyar jibiya ta tsaya ta taimakaman ta tsallakar dani titi,tindaga ranar yarinyar tashiga raina dan na fahimci rayuwarta cike take da damuwa, mahaifiyar ta Azzalumar macace, ayhiyasa na shafe mata tinaninta a'kwalwa ta manta da ita baki daya, kai kanka da kazo da suffa zalinci Abubukar shiyasanya na horaka iya horo, Ammar ya zaro ido jin ya am'baci sunan irfan na gaskiya.
Tsohon yaci gaba da cewa bakason a'lakarka da itaba shiyasa ada tazamema abar wulakantawa, amma ba laifin kowa bane sai na ubanka da baida ilimin sauke hakkin dan adam, sama da shekaru biyu yabar matar Aure tana yawo a'gantale da igiyar Aure akanta, ku kallo nan ya dakamasu tsawa da sauri suka juya sosai jikinsu yakama rawa da sukaga Tsohon mutum tuguf cikin suffar mutane lafiya lau harda sanda da kwano.
Yace ku kalli cikin kwano nan kugani.

Idon su kamar ya fad'o suka zubama kwanan ido! Irfan ya zaro ido yace wanna ai Daddy nane a kwance.

Tsohon yace na fika sani, kuma zakaga hukuncin da zanmai,saboda wasa da amana da yayi da kuma raya sunna, ya buga yatsun shi biyu a kwanab saiga Daddy an nuno ya wartsake yana zunduma salati, tsohon yasake zabgama kwanan yatsu, Daddy ya mike yan kururuwa .

CIKIN karaji tsohon nan ya fara fad'in ya amanar da aka baka ?ka gaggauta zuwa ka had'a abunda Allah ya halasta kaji na fad'ama, inba hakaba zancimaka mutunci..

A idon su sukaga Daddy ya tashi da gashi sai singlet yayo waje, ya hau mota ko driver bai tsaya jira ba ,a'gaggauce ya d'auki wayarshi saiga kiran shi ya shigo a wayar Irfan.

Tsohin ya'ce" maza ka d'auka.

Irfan ya d'auka!Daddy yace maza kaje nan opposite da gidanka gidan wata budurwa ina zuwa.

Irfan ya'ce ok.

Daddy ya sake cewa ka cema Ammar nace yayi sauri ya d'akko Tsohuwa mu had'u a'gidan yanzu! ya kashe wayar."

Tsohon nan ya kwashe da dariya tare da Ce'wa d'an nema taya zaka fifita neman kud'i akan Sunna .

Ammar yace ya Allah munbaro yaran nan waje fa.

Tsohon ya'ce" karka damu suna zaune a palo, naji dadin taimakon da kukai masu matuk'a. ku tsaya kugani kamin kaje ka dakko tsohuwar....✍️
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘💘💘💘💘💘💘💘
ZAMAN TASHA
5️⃣6️⃣&5️⃣7️⃣
Chapter 26 · 0% Book details