← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 32

Sashe 25

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Irfan yace Dan Allah kadaina minacema ni kuwa.

Suna shiga mota kiran Mamy na shigowa wayar Irfan ya d'aga tace kai maza ka k'araso ga Yusra ta iso......✍️
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘❤️💘💘❤️❤️💘❤️
ZAMAN TASHA
💘💘💘💘💘💘💘💘
NA UMMY AYSHA
🅿�4️⃣9️⃣

""" Cikin Kasa da murya Irfan ya'ce" to".

Haka suka tada motar ba mai cewa kowa wani wabu, ko wannan su da irin tinanin da yake yi harsuka kusa karasa G.R.A kana Ammar ya'ce" ko kason Moopy marainiyace shiyasa bataso ka zagi mahaifinta?
Irfan ya zaro ido ya'ce" to duk wannan dukiyar da take fantamawa da ita waya bata?

Ammar ya'ce" kasamu cikakken lokaci zan baka tarihinta Insha Allah.

Cike da zakuwa Irfan ya'ce ina jinka yanzu?

Ammar ya'ce" ba Mamy ke kiran kaba?

IRFAN ya'ce share wannan kiran, wai ita dole sai na auri wannan karuwar yarinyar diyar kawarta Yusra.

Ammar ya'ce" a'a kadaije zaifi kawai ,an'jima muhaÉ—e gidan Tsohuwa ko nan zaka kwana?

IRFAN ya'ce" a'a ba nan zan kwana ba, sai nashigo din, daganan sukai sallama suka rabu Irfan ya faďa gidansu Ammar ya juya motar shi zuwa masallaci yayi Sallah, yana gamawa ya tada motar zuwa JIFATU ya lafto siyayya ta gani ta faďa, ya biya ya fito yayi gidan Moopy.

Yana zuwa ya iske Moopy da su Rafel zazzaune cike da farin ciki kowanne a'fuskar shi, fuskar Moopy fayau ba alamun damuwa ko wani bacin rai, dan zuciyarta fayau take .

Ammar yashiga suka gaggaisa ya ajema Moopy sayayyar da ya yomata ya'ce" gashi inji masoyinki na hakika.

Mamaki sosai yakama Moopy tace waye shi yah Ammar?

Ammar ya'ce nima haka kawai yace man .

Fahad yace kai aboki ko kaine?

Ammar yazaro ido yace aa gaskiya ni ai k'anwata ce ko Moopy?

Moopy ta'ce" eh Wallahi hakane.

Ammar ya'ce yan uwana naji daďin haduwar mu Wallahi, inaso kutayani ba Moopy Hakuri akan laifin da abokina D'an uwana yamata, ya kwashe komi ya fada masu tare da irin tsantsan so da Irfan yake mata, tin bai son ko wacece ba.

Sosai Moopy ta shiga tashin hankaliba cikin kuka tace karmuyi haka da kai Yaya na karkai am'fanin da matsayinka awajena kasani tirsasani yin a'bunda ba shibane.

Ammar ya'ce" ba tilasti Moopy kana bazan taba nunamaki kiyi abunda baki soba sai dai ina neman alfarma a'wajenki zaki iya ganina da Irfan akoda yaushe gidan ki kozaki yarda da hakan kasancewar baya zuwa ko ina kuma bazaiji dadi infita in barshiba.

Moopy ta'ce banda case da wannan bakuma zanso ya zarce daga hakan ba.

Ammar yayi dariya ya'ce" hakan ma nagode.

Irfan na shiga palon su yayi sallama fuskarshi a daure cikin k'asaita yasa kai zai shige kamar daga sama yaji an'rungumoshi ta baya,tare da Ce'wa shine bazaka kula da niba bayan tin dazu nike jiranka.

Rai amatuk'ar bace ya juyo a'fusace tare da dauke Yusra da wani wawan mari dayasata kwalla ihu aguje su Mamy suka fara sakkowa suka yo kan yusra data fadi tana burgima rai bace Mamy ta'ce mi kaimata?

Ba tsoro ko kaďan afuskar Irfan ya'ce" marinta nayi saboda ta...

Kan ya k'arasa yaji an'kifamai mari har biyu...✍️
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘❤️💘💘❤️❤️💘💘
ZAMAN TASHA
💘💘💘💘💘💘💘💘
NA UMMY AYSHA
5️⃣0️⃣

""" Agigice Irfan ya juyo jin bak'on lamari! Mahaifiyar Yusrah ce sai huci take kamar zakanya, cikin matsanancin fushi ta'ce" kai d'an ubanwa ye da zaka mari yata? Uwarkama tayi kad'an balle kai Dan
Tsohonka...

Tashin hankali da ba a'samasa rana inji IRFAN! ke ni kika mara akan wannan kod'ad'd'ar yar taki ?

Tasssss! tasss!! tasss!! ya saukema Hajiyar Yusra mari ! Mamy jikinta yayi mugun sanyi,su da keso a lallab'ashi amma shine abun yake neman zama fitina.

Cikin mamaki Hajiya ta'ce" ni kamara"?

Irfan ya'ce an mareki ko zaki ramane?

Aiko Hajiya ta juya ta d'ad'ama Mamy marin da yasa ta fadawa akan kayan kallo, dan ta maru .

Fad'a ya kaule tsakanin IRFAN dake a'fusace! ya fara jibgar Hajiya da Yusra da belt saida ya masu rudu-rudu kana ya korasu Kamar karnuka.

Cikin takunshi na k'asaita ya karasa wajen Mamy dake kwance magashiya! a'hankali yasa hannu ya'ce sannu Mamy.

Afurgice Mamy ta tashi ta haura saman bene da mugun gudu dan ta d'auka k'awartace ta dawo.

Ko ajikin Irfan saima sama da yayi da gudu yayi wanka yayi Sallah, ya fito a'gaggauce ko d'akin Mamy bai kallaba ya fice tare da tada motarshi yayi gidan Tsohuwa, yana zuwa ya duba Ammar baya nan, ya zaro waya yakirashi Ammar yace bana nan ina gidan Moopy ka k'araso mana.

Irfan yayi jim yace kana ganin ba matsala ne?

Ammar yace eh mana ka k'araso.

IRFAN ya'ce to tare da tada motarshi yayi gidan Moopy! sosai gabanshi ke faduwa haka ya daure ya aje motar bakin get ya fara ta kawo kamar mai ciwon k'afa harya shuga cikin palon da yakejin hayani yarsu, zaune suke sunbaje kaji ko wannasu a plat sai shagali suke, Moopy na zaune k'asa tana danna waya Inna Asibi ma k'asan take zaune su Ammar na saman kujera sai fira suke.

Irfan yayi sallama yashiga palon.

Su Duka suka zubamai ido kamar abun had'in baki,sai yaji duk hakan bai mai Dad'iba, ya basu hannu suka gaisa tare da gaida Inna Asibi ta amsa yayi shuru..

Ammar yace k'anwata baki gaida D'an uwaba ko dai ba a'yafemana bane?..

Moopy tai murmushi mai kyau ta'ce" aa Wallahi ina wuni?

Tace da Irfan tana kauda kai.

Agajarce ya'ce lafiya.

Fira suke sosai su Rafel sai janshi da labari suke amma yayi shuru yaki cewa komi, dan mugun haushi suke bashi ganin sunwaniyi fako-fako a'd'akin budurwa tsaki yayi mai sauti tare da tashi yaficce. Moopy ta rakashi da harara. Ammar ma yamasu sallama yafito suka hau mota .

Irfan ya fara maseefa ta inda yake shiga batanan yake fitaba, danmi kuke zuwa kuyi zaune danmi bazatabar mu a'mmullah da kuba ?yi yake ba k'ak'k'autawa.

Ammar yayi murmushi tare da cewa kashirya jin labarin nata yanzu ko maseefa zakai?

Irfan ya'ce" ina jinka".

Ammar yayi parking din motar tare da zayyanema Irfan Tarihin Moopy tindaga farko har karshe ,da alakar dake tsakaninsu da Alhaji shi da ita bata sani ba..

Ido jajur irfan ya'ce"Imran! Imran!!
Kuka mai karfi ya kwacemai.

Dakyal Ammar yasha kanshi ya Hak'ura...

Cikin kuka IRFAN yace inaso in'son gidan Ammi ta..

Washe gari tin da safe su Ammar suka fara bincikar gidan Ammi cikin ikon Allah suka gane da taimakon Moopy da Ammar yamata tambaya asace tabasu amsa....

Suna isa inda aka kwatan tamasu sukaga samari mutum biyar sun fito da gawa daga cikin gidan..
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘💘💘💘💘💘💘💘
ZAMAN TASHA
💘💘💘💘💘💘💘💘
NA UMMY AYSHA
🅿�5️⃣1️⃣
""""Salati su Ammar suka saki suka k'arasa da sauri wajen, tare da tambayar mutum biyar din nan dasuke tsaye da gawa, Irfan ya'ce" waye ya rassu agidan nan?

Kan ya rufe baki yaji kururuwar na fitowa daga gidan.

Arikice suka juya !Ammi ta fito a'haukace tana Wallahi ba zaku fitarman da D'iyaba, kubarman ita bugun numfashina ce .

Afusace Aminu da keta kuka yace ku ajemata ita, kubarmata tashiga da ita tinda yarso din tace, Wallahi Ammi nayi danasanin fitowa daga tsatsanki Allah ya rufamana a'siri bayan ya karb'i ran mahaifinmu yabamu jajartatta yar uwa mai son mu da kula damu, kikai am'fani da matsayinki na uwa kika wulakantata, tayi zuciya tabarmu bari na har abada, bayan kinsan bakida wata sana'a, bamu da komi ga lalurar Amina, to gashinan ta mutu ta barki, kuma Wallahi kinada alhakin mutuwarta, saboda tana da hanyar daza a'mata kika hana nima bazaki k'ara gani Nana zantai inyi aiki karfi ina kula da kaina Amina Allah yajikanki ya juya da sauri yatafi.

Cikin matsananci kuka Ammi ta bishi tana kiranahi! amma ina cikin lokaci Aminu ya b'acce mata ko sawunshi bata gani ba, hankalinta yasake tashi gashi duk samarin sun watse sai gawar Amina, dasu Ammar tsaye.

Sosai Irfan yaji haushin Ammi! yaja Ammar gefe yace mu wuce mu kyaleta bayan kwana biyu madawo.

Ammar yace aa mutaimaka mata ko gawar a'kawar, ai baza abar gawa haka ba a tozarce.

Ammi ta kula dasu tayo wurinsu tana kuka tana sutaimaketa dan Allah, y'ayanta duk sunk'are shikenan bani da kowa saini d'aya, ina Mufeedah? Dan Allah ki bayyana gareni a'dai-dai wannan lokacin da bani da kowa.

Irfan ya juyo afusace yace sukad'ai kika haifane ina sauran?

Ammi cikin kuka tace babu !sai yar uwarsu itama bani da labarinta, sama da watanni na fara nemanta ido rufe amma bangantaba. tafashe da kuka.

Ammar ya'ce yanxu to yazakiyi da gawar nan? ko barmaki zamuyi...

Ammi ta'ce" aa ku suturtata dan Allah kutaimakan...

Irfan ya'ce zamuje da ita masallaci acen amata Sallah a binneta.

Ammi ta fashe da kuka tace Allah ya yafemaki diyata allah yadawoman da Aminu da Mufeedah, na yarfa kuje Amina na yafemaki ki yafeni y'ata, nason na cutar dake dana kasa nemar maki abinda zaki sanya bakinki.

Tana kallo su Irfan suka fiddo gawar Amina daga cikin makara suka sanyata a'bayan motarsu sukayi gaba.
kuka sosai Ammi ta sanya ba mai lallashi, saida tagaji ta koma gida rayuwar duniya baki daya ta juyamata baya, batada komi nata dazata kalla tace kudi sunanshi, Allah Allah kakawoman Mufeedah in nemi a'fuwarta, nason sakayya abunda namaki kad'ai bazai barniba ....

Bayan suntafi su Ammar sukai shawarar zuwa Asibitin ayi gwajin daya kamata, haka sukeje aka fara gwaje-gwaje cikin ikon allah saiga lumfashin Amina ya fara dawowa, sosai sukai farin ciki Irfan ya'ce Ammar ya kake ganin zamuyi da matar cen taban tausai fa...

Ammar yace bari inje gidan in'bata wani abu ta d'anci abinci.

Haka yaje har unguwar su Ammi tana ganinshi ta'ce" har an rufeta ko?

Ammar ya'ce" eh saikibita da addu'a ba, ya ajemata abunda zai bata yayi gaba.
Ammi kamar taci babu yaushe rabo tin moopy na bata kuďin.

A'hanyar dawowar Ammar yayi karo da Aminu yana tafiya akan hanya yanata share hawaye, Ammar ya tsaya yamashi bayani tare da d'aukarshi yayi Asibitin su da aka kwantar da Amina, farin ciki sosai yakama Ameenu, nan yafara masu godiya sukace bakomi, yaďan zauna ya kula da ita kamin kwana biyu.
Aminu yace to insha Allah..
Chapter 25 · 0% Book details