← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 32

Sashe 2

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsohuwa tace wlh karkaga laifina kama ka keman da shanuwa da akai layya bana makwaftana gidansu irfanu ga hula kakifa kamar kasamu bokitin roba amma namaka alkawari bazan sake kallonkaba tafada tana maida hankalinta ga titi suna zuwa kwanar gidan balele tace asauketa.

Yar Cara's tace bari inkaiki kofar gida kinji inna?

Tsohuwa tace ke kinsan dalilin daya hananine ne? haba banso saukeni mana yar cara'f.

Yar Cara's tace bafa haka akecemanba inbazaki iyaba kikirani da mufeeda kawae.

Tsohuwa tace ai dama ba zakara aka yankamakiba kikasa akasamaki yar cakwal ? Gasunanki na mutunci ganin za awuce da ita yasata cewa ke saukeni yayi nan.

Yar Cara's tai parking tasauketa tare da sauka ta,daukarma tsohuwa jikkata ta ajemata tace inna yaushe zaki koma in,mayar da kene?

Tsohuwa tace ke yar nan inkinganni lahira maza suka kaini ba mataba kinji tsaya inkawomaki ruwa tinda kinada kirki.

Tafada wani tafkeken gida tare da rufe kofar.

Yar Cara's natsaye tana juya hannuwanta sai jitayi anbude kofar anfito wani zanka deden sojane tsohuwa nagaba yana bayanta tana zuwa tabude bayan motar da karfi inda makashi ya jingina da kyaure yana kwasar bacci sai jinshi yayi kasa sharaf agigice yatashi yana fadin la'ilaha illallahu muhammadu rasulillahi (S.A.W) dan duk tinaninshi accident sukayi .

Tsohuwa takwashe da dariya tare da fadin shege ashe kason Allah to kwantar da hankalinka nakawoka amaka hukuncij daya dace a musulunci ga dana nan zai cima uwa dai dai gwargwado tafada tana nunama sojannan dayayi tsaye yana karema yar Cara's kallo.

Tsohuwa ta dage takaimai bugu ga kirjinshi tare dafadin kai dan ubanka bacema nai kacimai uwa ba kayi tsaye kamar gunki.

Yace innamu bazaifa yiyuba inkamashi hakanan amma kibarshi inkere na yawo zabo nayawo watarana zamu hade.

Tsohuwa tasanya kuka tace shikenan balele. tadauki wata yar karamar tsoka tacema yar Cara's anshi ga alkawarin danaimaki .

Yar Caras tai murmushi tare da dukawa har kasa tace ngd inna Allah ya amfana tafada tana fadawa cikin mota, dasauri makashi yashiga ciki dan hakanan tsohuwa naneman tajamai bala'i daga wasa Allah yarufamai asiri sojan nan baikamashiba suna hawan bakin titi suka sauka suka biyata tajuyo katsina aguje cikin kankanin lokaci tashigo cikin tashar KSTA tana shiga ta ajiye mota su BIG sai sannu sukemata ta amsa tare da cemasu batajin dadi zataje gida sai gobe insha Allah yau fita daya zatayi kowa yasha mamakinta dan shekara ukku da,fara aiki amma ko bata lfy saitayi jigila so biyu .

Tana barin TASHA ta hau napep tare da sauka wani karamin gida sosai dayake a'matse sosai tana shiga ta iske mahaifiyarta da kannanta su biyu zazzaune sunyi uba uban tagumi da alama yunwa kekaimasu karo tana shigowa kannanta biyu mace da namiji suka mike suna faddin oyoyo adda sannu da xuwa mikika samomana ne?

Yar Caras tace ga kudin dana samo yau banajin dadi gasu saikusai wani abu ko ? Tafada tana juyemasu baki dayan kudaden hannunta, takalli ammy su dake zaune gefe ta kauda kanta cen gefe tace ammy nadawo ga kudin nan nasamo amma bayawa.
Ko kallonta wadda akakira da ammy bataiba. ko kadan yar Cara's batadamuba dan inda sabo yakamata tasaba tana zaune suka samo taliyar muri dafaffa suka zauna sukaci babu wanda yacemata komi har suka gama ta dauki bokiti ta debo masu ruwa makwafta ta ajiye tare dacema kannanta nawuce sai allah yakaimu, ammy natafi kamar yanda tayi tsammani bazata amsaba hakance tafaru ko kallonta bataiba.

Tana fitowa ta,tsallaka gefen titin gidansu ta doshi wata bishiyar bedi dake gefe inda wata zabgegiyar motar mai maseefar kyau kirar zamani take tafada cikin motar tare da sauke numfashi mai karfi tace ya rabbi ka warwareman matsalata Allah kasan dai dai Allah kabayyanar da gaskiya lamarinka akan baiwarka tafada hawaye nazubomata. ta kunna motar tare dabata wuta tahau titi sosai take gudu da motar cikin kankanan lokaci ta iso goruba rood, wani tafkeken gida da duk yafi sauran gidajen unguwar baki dayanta kyau naga tayi hon da gudu wani buzun mutum dayasha rawani yarugo yabudemata tare da fadin haj sannu da zuwa ya aiki Allah yatsareki yakaremanake yabaki lfy sannu hajjaju yafada cikin muryarsu ta buzaye.

Yar Caras tace yawwa baba sannu ya aikin fatan banyi bakiba ko?

Yace eh amma alh fahad yashigo dazu bansan miyayiba yafita.

Tace ok badamuwa tafada tana karasawa wajen parking lot inda wasu mahaukatan motoci sunkai hudu suke lullube cikin tampal tana gama parking tafito tare da cilla key dinta, ta chabe tai hanyar cikin gidan masha Allah nace dan wani mahaukacin gidane mai maseefar kyau (tsayawa tsara kyan gidan zai iya cinye baki daya littafinnan amma ku hararo abun)

Tana shiga tafada saman makaken gadonta tare dafafin wash. Tatashi tacire hijjob dinta nan wani yalwataccen gashin ta ma aboci tsawo da sheki bakikirin dashi yazubomata har bisa gadon baya tacire gabaki dayan kayanta tai tsaye bakin mirro ta,fashe da wani irin mahaukacin kuka tare da fadin ni ni niiiii.......🖊�
25/03/2022, 22:11 - Khadeejaht Salisu Fari: ❤️💘❤️❤️💘❤️💘❤️
*ZAMAN TASHA*
❤️💘❤️💘❤️💘❤️💘
WRITER UMMY AYSHA
❤️💘❤️💘❤️💘❤️💘

🅿�-5️⃣&6️⃣

*Elegant online writers*

Niii rayuwa, zataima haka.

Wace irin mahaifiya, Allah, ya bani da bata, É—aukar kaddara.

Dan ummy, zata kasa É—aukar kaddara da Allah ya É—ora?, bayan komi yafaru dani sana din tane.

Duk duniya bata da abunda ta tsana a rayuwarta sama dani, ta faÉ—a tana fashewa da wani mahaukacin kuka mai cin rai.

Saida tai kuka mai isarta bata da wanda zai rarrasheta, kana ta faɗa haɗaɗɗan toilet ɗinta, da keta ƙamshi, komi nacikinshi fari sol ne.

Sosai gabanshi ke wani irin mugun faÉ—uwa, ga wata matsananciyar kunya data rufeshi, yau shine wata yar ZAMAN TASHA, zata wulakanta a gaban bainar nasi innalillahi wa inna ilaihirraji un!

Driver da fuskarshi tacika da kwatamin, da "YAR CARA'S" tawatsamai, yakalli ,IRFAN dako idonshi baka gani dan baki daya fuskarshi, da jikinshi ya lalace da kwatami.

Kayi hkr yallabai, muje gida kadan dauraye kayan naka saimuje inda zaka ko?

"IRFAN" da bakin ciki ya hanashi motsi, yadago jajayen idonshi, dasaida sukasanya driver ya daka tsalle, yakoma gefe, yace yallabai wlh wuta ke haramar tashi, daga idonka, dan allah kayi hkr bari inkira ado yayi maza yakawomaka, sabuwar mota yanzu, yafada yana laluben wayar shi.

Bayan yakira, yacema ado kakawomana mota, gamunan dai dai TASHA kofar guga kayi sauri yallabai najiranka.

Baifi 20mint ba saiga wata zabgegiyar mota, tayi parkin gabansu, "Ado yafito dasauri tare da kalle kallen inda zai gansu.

"IRFAN" nakallanshi amma bazai iya cemai komiba, kamar ancema driver yajuya, yana juyawa sai yaga Ado, cikin daka tsawa yace gamunan gabanka shine kaketa kalle kallen iskanci, kamar bajiranka akeba.
Ado yazaro ido yakara kallon driver tare da fashewa da wata mahaukaciyar dariya yace yau gyaran 'kwata kayi? ko-ko gyaran rijiya? yafada yana dukawa saboda dariya.

Bakinciki, yasanya IRFAN dauke Ado da'wani mahaukacin marin, dayasanya Ado, watsawa da gudu bala'i cikin motar, dayakawo, tare dajan motar aguje, yayi gaba, dan duk daukarshi mahaukacine yagamu dashi.

IRFAN baison sadda yawatsa, da'gudu ba yana kiran Ado, amma ina Ado ya gigice yayi gaba, dole tasasu tsayawa suna nishi.

Driver yakara daukar wayarshi dan yakira Ado yana kira saijin wayar yayi kusa da kafarshi, alamun tsoro yasashi barinta. cikin bacin rai yace yallabai, bamu da wani solution yanzu, abu daya yarage shine muhau kurkura mutafi gida, dan wanda muke sanya ran zai taimakamana, yazama mahaukaci, cikin yan mintina.
dan,haka muhau kawae mutafi, yafi tsayuwar, nan damuke mutane duk sunzuba mamu ido suna kallonmu tin dazu.

Wata r'azananniyar tsawa IRFAN yadakamai, tare dafadin Allah yakiyaye hawan keke napep nii IRFAN, bazan taba hawan wancen matsiyacin abun, da duk dattin duwawun talakawane akaiba, badaini IRFAN ba. yafada yana zaro zabgegiyar wayarshi tare da lallatsawa, yakara akunne, yadan jima kana naji cikin daddadan muryarshi dayakasance mai sauri saurin magana yafara magana yana fadin Ammar kana ina ?yafada yanasanya wayar speaker dan inya kaita akunne zata iya baci da dattin fuskarshi, daga cen bangaran Ammar yace "Maza" inanan cikin gari nazo gaida tsohuwa kuma na iske batanan tayi tafiya.

IRFAN yace kakaraso kadaukeni, ina nan, cikin gari amma bansan sunan unguwarba, ga bala zai fadama.

Daga inda yake bala yakai bakinshi dan babban kuskuran dazayayi arayuwarshi yatabama IRFAN abunshi yace muna kofar guga wajen TASHA jibiya.

Basu dade, tsayeba saiga motar Ammar tayi parking dai dai wajen motarsu, yafiddo waya zaikira IRFAN kenan yaji an bude site din mai zaman banza anzauna.

Cike da bala'i Ammar yajuyo zai magana idonshi yasauka akan fuskar abokinshi datasha penti cikin yatsina fuska yace kai lfy kuwa "Maza" kaji warin kwatamin dakake kuwa?

IRFAN yazubamai jajayen idanuwanshi, tare dafadin kakaini gida nace.

Ammar yace wlh dama ka koma gidan baya, tsakanina da Allah tsami kake haba, dan bala'i danka kwasa kowama saiya kwasa waima tsaya faduwa kai ko-ko?

Karaf cikin kunnan driver,jikinshi har rawa yake yace wata yar budurwace tawatsamamu, kwatamincen! na bakin tasha, wlh nima kaga fuskata yafada yana nuna fuskarshi datakoma wata kala dan duk kwatamin, yabushe ajikinta saiti secuising.

Ammar yasaki wata mahaukaciyar dariya, tare da fadin mace? macace taima Maza haka ?kuttt dan Allah tana inah?

Bala driver yace wlh yallabai yar ZAMAN TASHA ce bamuson inda takeba yanzu, da alama mota takeja dan lodi akamata tazo taimana wanna iskancin .

Dariya kawae Ammar yake, tare da tada motar yace kasamu mai gyara saiku dawo da wannan.driver yace toshikenan.
Chapter 2 · 0% Book details