← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 32

Sashe 1

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💘
ZAMAN TASHA
❤️💘❤️💘❤️💘❤️💘
BY YMMY AYSHA
❤️💘❤️💘❤️💘❤️💘
🅿�1️⃣&2️⃣

BISSIMILLAH RAHMANI RAHIM yanda nafara littafinnan lfy da raina da lfy ta ya Allah kagwadaman karshenshi daraina da lfy ta inasonku masoyana so mai tsananin girma, fatan alkhairi ga dukkan masoyan ummy aysha 💅

Zaune take abakin TASHA hannunta rike dawata katuwar rake saisha take hankalinta kwance sanye take da riga da wando na Pakistan wandon fari sol riga orange sai wata hijjob mai saukin kudi fara sol yar karama mai hula data dace da kyakyawar fuskarta dabazata wuce yadi d'ayaba tsakiyar kanta tayi acuci bawata kwalliya taiba bayan kwalli dake idonta amma saboda farinta bazaka ce batashafa powder ba kafarta sanye dawasu orange din takalma dabazasufi dari ukkuba cikin daga sauti irinna yan TASHA tace yane
BIG har yanzu baka kammalaba? wani dan tulaki na hango yayo wajenta dadan gudunshi yace yar Cara's wlh mutum daya yayi saura tace ok zankarasa shanye rake nah inban samuba zan wulla da wayanda suka samu tafada tana lumshe idonta BIG yace angama yanda kikace haka za'ayi tana zaune taga wata hadadiyar mota mai maseefar kyau tayanko da gudu tagefen datake zaune akan wani dan karamin table cikin daga sauti take fadi wait wait!!!

Ganin motar bazai tsayaba cike da kwarewa tasaita raken hannunta tajefi bayan motar dasauri aka parker motar wani yafito dasauri da alama driver ne ,

Cikin wata tafiya mai cike da kasaita kasancewarta doguwa mai jikin kiba amma basosaiba sai tafiyar tamata mugun kyau tafara tafiya tare da jefa hannuwanta acikin ajjihunta takaraso wajen da driver yake tacemai bakason aikinkaba ko?
Indai kason aikina ai yakamata inkana tuki kaji wani canji amotarka katsaya kakula wannan taurin ran naka zai iya jamaka matsala watarana..

Afusace driver yace baza akulanba ke harkin isa kigayaman aikina shekara goma ina tuka mota ko keke bantaba bigewaba shikenan yau zaki koyaman aikina mtss

Ta lumshe idonta dana lura dabi'artace tace ok tare da dukawa kason motar saiga zungureriyar 'kusa ajikin tayar da gab take da fashewa tace wannan yakake ganin zaku kaya aduk sadda tafashe? .

Cikin rashin gaskiya da kame kame driver yafara kallon cikin motar yace to to!! Naji jeki.

Tamikomai hannu tare da fadin bani zan wuce .
Driver yace mizanbaki tace kudi nasanya nasai rake inasha ganin zakuyi accident yasani jefamaka raketa ka,kauga bazanyi asaraba tafada tana juya ido
Cikin takaici yace to ubanwa yasaki kika jefa? kikaki barina inma mutuwace in ....
Baikarasaba yaji an daukeshi da mahaukacin mari tadago idonta da,cikin "kankanin" lokaci suka koma jajawur tacemai mafi girman kuskuran dazakai shine kazagi mahaifina duk ranar da tsautsayi yasaka sake zagin mahaifina wlh anan zan gwadama ni cikakkiyar yar ZAMAN TASHA ce wlh banza kawae kaban kudina inwuce nacema

Sosai yarike kuncinshi yana kallon yarinyar dabazata wuce shekara ashirin da biyarba tadaukeshi da marin daya nemi gigita tinaninshi yace nikika mara?

Tace eh karama mana yadaga hannu zai kifamata mari aka zuge glass din motar tare dacemai kull cikin wata tattausar murya.

Bahaka yasoba yaso yanunamata shima yayi ZAMAN TASHA bawai ita kadaiba.

Bude motar akai tare daziro wata kyakyawar farar kafa dake sanye cikin bakaken cover sai kyalli suke ahankali jikinshi ya ida fitowa bansan sadda nace masha Allah tubarakhallah lallai Allah yayi halitta kyakyawan namijine farine kyakyawan gaske ajin farko yasha wata danyar gizna fara sol yasanya hular zanna mai ratsin fari da'baki sajenshi kwance lub lub bakikirin,bakinshi pink color yan kananu dasuka dace da fuskarshi hancinshi dogo sosai har baka yanada yalwar gira da manyan idanuwa da kallo guda saiya ladaftar da mai laifi.

Cikin kasaitacciyar muryarshi yacema driver bukar bakada hankali ko?
Kai wawan inane danmi zaka biyo dani tacikin gari bayan kason duk yan TASHA ne kezazzaune suna ZAMAN banza suna jiran azo abasu dagangan zasu sama motarnan wani abu dan sunganni aciki ke ubanmi za abaki harkina daga,hannu kina marin wanda yagirmeki banza yar ZAMAN TASHA kawae.

Cikin bacin rai tace ubanka nike zaman jira kasake zagarman uba wlh zansanya amaka dan banzan duka awajannan dawata banzar fuskarka kamar kosai mtss dallah bani hamsin dina inwuce.

Cike da mamaki yake kallonta tinda yake baitaba ganin macen data tsinkashiba arayuwarshiba kamar yarinyar nan wato batama tsoranshi bata shakkarshi bata ganin shidin ko wayeba kenan?

Yace aikuwa zakison kintabo IRFAN KHABIR HAIFAN ,yafada yana cije bakinshi .

Cikin zaromai idonta tace kai dallah cen dawani shegen sunanka kamar atini niban kudina inwuce kaji ganin,zata taramai mutane yaxaro makudan kudade yajefamata tace kai harkana da kudin dazakaban wlh baka dasu kuma bak ajeba ta duka tadauki dubu daya tasiyo rakenta ta nera hamsin takawomai canjin tare da watsamai su afuska .

Azabure driver yace laaa kai wannan akwae yar banzar yarinya datsayi kamar daran tsalla mai gida jibi tsohuwar goma talike ahancinka yafada yana nuna naira gomar datai tsaye bisa zufar dake zuboma IRFAN ahanci suna tsaye kunya duk tacika IRFAN ganin yanda mutane suka zagayesu suna,kallo basu ankaraba saiga yar Cara's tadawo da wata katuwar kusa mai maseefar tsini tadagata tacakama tayar motar jikake suttt duk iskan yafita.
Takalli irfan tace jan kosai hukuncin duk wanda yazagi mahaifina kenan tana cikin magana BIG yace yar Cara's ansamu cikon daya, cikin sauri takarasa cikin tashar nan akafara fadin Cara's Cara's ko kallonsu bataiba tashiga wata jar mota kirar gowp tayi addu'a tare da daukar wani bakin glass tasama fuskarta wani mahaukacin kyau yamata dukda fuskar tata adaure take tamau babu alamun annuri afusace taja motar tafita daga cikin TASHA tana zuwa dai dai inda IRFAN yake tsaye har lokacin kamar andasashi yakasa komi ga naira goma ahancinshi baidaujkeba bata kuma fadiba. Wasu ruwan dake kwance bakin inda yake tsaye tamurza tayar motar cike da kwarewa ruwannan sukai tsalle suka watso jikin farar shaddar IRFAN da driver dake tsaye yanata magana azabure IRFAN yadago jajayen idanuwanshi yazubama motar dataimai wannan aika aikar tasauke glass tare da cemai hukuncin duk wanda yaraina mahaifina kenan mtsss taja motar damahaukacin gudu kamar ba maceba tadauki hanyar jibiya sai gudu take shararawa wata tsohuwa dake xaune gaba tace haba yar nan kibimu ahankali mana inbanda lalacewa zamani kina mace kina tukin mota. Tafiya mai nisa irin wannan wlh danason maca xata kaini gidan balele da bazan shigaba yar Cara's tai parking gefen titi tare da fitowa tasamu sit belt tadaure tsohuwar nan tare da fadin kisanya wannan kawae gudun karki watsar da hakoran gaba kinyi expired amma har gobe son duniya kike .

Cikin sauke numfashi tsohuwa tace ke dan ubanki kicereman igiyar nan tinda ba goro bace ni saiki daureman ciki dan kinsan safara'u matar balele tayankaman kaji bakin ciki kike inci ko?
Tinda kinsan babaki zanba .

Sosai tai murmushin daya fiddo da zankadediyar wushiryarta dake tsakankanun fararen jerarrun kananun hakoranta masu maseefar kyau ga mamakina hadda hakorin makka gareta dan asali mai maseefar kyau sosai yakarama hakoranta kyau tace karki damu mama bama TASHA zankaikiba har kofar gidan dakikeso insha Allah.

Tsohuwar tace wlh yar karama zan yanmaki kazar inbakibar guduba yar Cara's tace aini burina inkaimu inkwaso wasu inkuma kara komawa dan 'ka idata so biyu nike jigila wannan hanya duk kuma inda shidda tayi na yamma ZAMAN TASHA yakare sai Allah yakaimu kanan.
Tsohuwa tacema wasu samari biyu dake baya kai anshinan kasha wata shegiyar hularka har bisa ido kamar kakifa po kiraman dana ingayamai ankusa kasheni.

Wanda taima magana cikin muryar yan daba yace waiya tsohuwa wlh karkija bara tadawo bana wannn hular sata sirrine dan bansaba sawabane amma inkika sake magana zancireta saiki son dawa kike magana atakaice dai sunana makashi...🖊️😳�
25/03/2022, 22:06 - Khadeejaht Salisu Fari: ❤️💘❤️💘❤️💘❤️💘
ZAMAN TASHA
❤️💘❤️💘❤️💘❤️💘
UMMY AYSHA
❤️💘❤️💘❤️💘❤️💘
🅿� 3️⃣&4️⃣

FREE NOVEL

gabaki daya tsohuwa tafiddo idanuwanta waje tare da fadin yallabai dama kaine? aimundade munajin labarunku kullum sainaima addu'a Allah yahadamu ko bisa hanyane, inacikin masoyanka tafada jikinta na rawa baki daya.

Cikin muryar yan daba yace to gdy nike kakus.

Tace karkaji komi masoyina bari mukarasa gidan d'ana in sammaka kaji da safara'u tadafaman kaji ko?

Yace yawwa kakus dama sai nasha wahala kamin inkarasa inda zani dan haka sai mufasa kawae muje mushanshareta aha.

Kasa kasa tsohuwa tace jibarshi shege b'akinshi kamar zunibi ya ajiye wani gemen banza kamar tabarmar kaba.

Makashi yayi ka sake yanajinta yace kikace me tsohe?

Cikin rawar murya tace gafarar Allah nike nemamaka nason dole walakiri ya cima uwa tinda kai hamshakin dan dabane ka kauga haduwarku babu kyau ko dan jikallena mai kan kwakwa.

Yace wlh tsohuwa kika sakeman sharri saina kifar da motarnan kowa yagane kuranshi yafada yana zaromata jajayen idonshi. jijinta na rawa tajuya tare da fara lazimi.

Yar Cara's tuki take cike da kwarewa bata um bata um um amma bakinta yana motsawa ahankali itakadai tason mitake fada suna karasawa bakin gadar jibiya taja wani wawan burki tsohuwa da tasha dauri saida tai gaba tadawo baya jikake kumm.

Tasaki wani mahaukacin kuka tama fadin Allah ya isa tsakanina dake yar cakwal kike ko yar firit?

Yar Cara's tafita daga motar tare dakama hannun wani dattijo da tagani zai tsallaka titi, mafari tsaida motar kenan saida ta tsallakar dashi tana kokarin juyowa, yace yanda kika taimakeni Allah ya ya'yemaki duk damuwar dake ranki yata ngd da kokari.

Yar Cara's tabishi da kallo tare da fadin bakomi baba karba wannan kasai ruwa. tafada tana mikamai naira dari biyu bata jira cewarshiba ta tsallaka tabude motarta takara gaba sosai tsohon nan yabita da kallo har ta baccema ganinshi.

Suna cikin tafiya tsohuwa tace dan ubanki "yar Cakwal" ga kwanar gidan d'ana balele cen kin zalinceni kin cireman hakoran danikema jikokina dariya,tafada tana bude katon wawulo din ta.

"Yar Cara's" tace kai tsohuwa wannan dasashin naki aibana yau bane kijifa babu alamun jini awurin amma in ni namaki kiyi hkr kakata kinji?

Tsohuwa tace nayi amma bazan baki ko sisiba dan balele nah bamai kudi bane kashin talauci garai duk abunda yataba baya albarka. yauma nazo inbashi shawara yafara sana'ar kidmashins dan duk yayi maganin wani dan iska dawani tsohon dan ta adda dayake ganin yakai wani shege da masu hula bisa geme tafada tana satar kallon makashi.

Makashi yace idan kika sake kallona inba sai na ciremaki hanciba dan kwal uba nike haba kaji maseefa.
Chapter 1 · 0% Book details