← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 32

Sashe 24

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Moopy ta saki Dariya da taja hankalin mutane da yawa ciki harda IRFAN da mamaki ya ke neman sanya numfashinshi d'aukewa ta ware idonta tare da juyasa tace umm D'an wake ko Tuwo.

Nan ma akasake tafawa

Tambaya ta ukku MIKIKAFI SO DA TSANA A RAYUWARKI ?

Take fuskar Ta ta canza cikin siririyar muryarta ta'ce azagarman MAHAIFI ko a"wulakantani akan abunda bansani ba shinafi tsana.
Abunda nakuma fi so shime tai makon wanda bashi da shi. da Son mai sona ko ya kau mutum yake

Tambaya ta ukku waye MASOYINKI NA FARKO?

Ahankaki tace BABANA, Inna ta, kaka ,yah Rafel yah Fahad, Baba Alhaji, yah Ammar, sune masoyan daban da kamarsu duk duniya.

Fahad yace Masha Allahi ko zan iya sanin abunda ya faru dake da bazaki tab'a mantawa ba?

Moopy tace Karyani da wani yayi, da kuma Marukan da ya dinga saukeman akan abunda bani da hakki, shiya fara man na rama..

Take wajen ya kaule da hayaniya wani mai kama da D'an daba yafito yana wallahi ba dan kaniyar da ya isa ya maki haka ya zauna lafiya, fadamana inda yake d'an kwal ubar gobe sai dai uwarshi ta haifi wani, dan yau inba sai nai mai sabuwar shayi ba dan kundun uba nike, dan bazamu bari ba.

Take cikin Irfan ya d'uri ruwa dan gani yake kamar mutane zasu fahimci ko waye...

Moooy ta karb'i Speaker tace ayi hakuri a'zauna mukarasa lokacin Sallah ya kusa ba, kubarshi dan kanshi....

Nan suka natsu wajen yayi tsit.

Ammar ya karbi speaker hannun Fahad yace k'anwata idan wanda ya kasance mak'iyin ki yafito maki asigar masoyi shin zaki iya yafemai?

Moopy tace tabbas kuwa, amma fa banda mutum d'aya koda mutuwa zayyi bazan taba ya femai ba, dan ya zalinceni matuka daga taimako tafada idonta na zubar da kwallah, afusace tace zan yafema kowa banda wannan azzalimin bazan kara tankamaiba amma zan dinga kai kararshi wurin mahaliccina yasakaman ...

IRFAN da kuka yake muraran kamar karamin yaro, jin yanda take ai'bantashi acikin baina nas,i ahankali ya taso kirjinshi na bugawa yayi Al'kawarin koda mutane zasu kasheshi awajen nan sai ya bayyana ma duniya shine Moopy ke nufi. haka yafara tafiya yana layi harya iso gab da ita.

Moopy ta jiyo zatai magana kenan idonta ya fada a'nashi,nan suka shiga yiwa juna kallon-kallon kamar wasu Zakuna, afusace dan tama manta Speaker ce hannunta tace kazo nan diynma cikin taron masoyana ka mareni ka sake karyani ne? minaimaka da duk sadda zan kasance cikin farin ciki saika do so inda nike, waye kai mika keso in'maka?

Kamar daga sama sukaga mutane bila adadin suna yo kan irfan da gudu bala'i suna fad'in shine shine Wallahi..

Cikin tashin hankali Ammar yafara sakkowa wajen aguje yayo kan Irfan yana fadin mubar wajan na. Dan Allah.

Irfan da zuciyarshi ta riga ta dake "y'ace ba zanje ko inaba indai ganin gawata gabanta zaisanya ta yafeman to bandamu da rayuwata ba a'dai-dai wannan lokacin, da rayuwar take juyaman baya, ashe duk azabar danike mata itace masoyiyata, kaicona-kaicona dana kasance mai zafin rai da zuciya.Ammar inaso ka nemaman gafarar iyayena ko bayan Raina.

Ammar yavdakamai tsawa ganin mutanan sunkusa cinmasu yace mu gudu Irfan." Amma Irfan ya dage kan kace mii mutanan nan sun'masu zobe suna fad'in sai sunkwatarma masoyiyarsu yancinta, daga cen gefe wanda yatashi d'azu ya ruga cen kusa da wata bishiya sai gashi da iccen faskare babba yace Wallahi saina kar'yaka in'yaso akaini kotu, aguje yayi kan Irfan yana zuwa ya ture Ammar damugun karfi har saida Ammar yakai kasa ya daga iccen nan tare da.....✍️
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘❤️💘❤️💘💘💘❤️
ZAMAN TASHA
💘❤️💘❤️💘❤️💘❤️
NA UMMY AYSHA
💘❤️💘❤️💘❤️💘❤️
🅿� 4️⃣7️⃣&4️⃣8️⃣

""""Ya D'aga iccen nan tare da yin kan Irfan zai saukemai kenan yaji ya bugi iska, cike da mamaki k'auran nan ya juyo yaga mike faruwa idonshi yafada akan Moopy dake tsaye tana huce. a'fusace ta'ce" ni nasaka? dan mi bazaku bari in'barshi da wanda ya halicceshi ya haliccemu ba ,sai kuce sai kun d'aukar man fansa? ban son da Yan Sanda da yan jagaliya irinka ba amma som ban neni ko d'aya ba nace Allah shi zai isar man, karka k'ara kwatan ta yiman wannan shishigin ta fad'a a'fusace, tare da komawa inda take d'azu ta dauki speaker ta fara magana kuyi Hakuri Masoyana, banaso ya zamana ranar farin ciki ta zama ranar damuwa ta ,a'yau duk wanda ya raunata d'an uwanshi musulmi ta dalilina nason dole a'samu masu tir da bayyanata akaro na farko a'wajenku, dan haka kuyi Hakuri ku barshi da halinshi nagode da kulawa Allah yabamu ALKHAIRI. ta aje tare da sakkowa daga kan step din sosai wurin ya kacame da hayaniya ta mutane daban-daban, anan kowane ke fadi albarkacin bakinshi wani yace tana da mutunci wani yace ta wulaknta masoyanta dasuka so daukar mata fansa, kowa da kalar abunda zai fada .
Manyan Alhazawa suka dunga bama Fahad kyaututuka na ban girma a'bama Moopy, kud'ad'e kam ta samesu kamar ta fasa ihu, ko motocin hawa saida ta samu guda shidda manya masu numfashi uwa uba Waseeku na so da k'aunarta da suka shigi zuciyar Al'hazawan birni,tin fahad na tar ba hannu yana sawa Aljuhu har ya cire babbar rigarshi ya bazata k'asa duk wanda yaba Moopy kyauta zaice sashi a'nan, ahaka har akayi Magriba, d'ayar motar da a'bokin Rafel ya tukota suka bud'e anan itama ta fara raba sabon kaset dinta na wakokin datayi masu maseefar dad'i, kowa yayi murna yayi godiya taro ya watse cikin farin ciki har myoopy zata shiga mota ta tino da Ammar, da sauri ta fito zata k'arasa wajen da yake ta dingajin sheshshekar kuka natashi, ta D'an saurara kad'an har'zata wuce Sai kuma ta dawo baya, anan ta leka bayan Bishiyar dan daga nan takejin kukan, ganin mutum ya bada baya bazata iya kallon fuskarshiba ga duhun mangariba yasa a'hankali cikin siririyar muryarta ta'ce" duk wani tsanani yana tare da sauki, ya waita LA HAULA WALA KUWATI ILLAH BILLAH, SHINE ZAI MAGANIN DAMUWARKA CIKIN SAUKI,KA LUZAMCI HASBUNALLAHI WANI IMAL WAKIM ADUK SADDA KASAMU TUNKUSHEWAR ZUCIYA, ALLAH YA WAR'WAREMAKA MATSALARKA AMEEN.

Ta juya zata tafi Irfan da duk a'bunda ta fada ya'jita sarai amma yana tsoron ya juyo baison wace matsala zai fuskan ta da ita ba, tinanima yake yamata maganar a'nan ko-ko ya isketa gida? To kuma ko yaje bata'nan, karfa yabari damar data sameshi ta kauce. cikin sassarfa ya cimmata tare da Shan gabanta idonshi fall hawaye kamar yaro ya dukar da kanshi k'asa tare da fad'in dan girman Allah dan zatin Allah kiyiwa Allah Moopy ki yafeman ko nasamu sawaba, ni d'an adam ne zuciyata da ruhina na cike da Ajizanci, ki tausaya man gani a'gabanki bada fad'a ko ihu ko hargowaba, AA na zone da niyyar kiyafe'man duk wani a'bunda na miki Dan Allah Mufeeda badan ni'ba, Na rok'eki da Allah kiyi Hakuri.

Moopy da tinda ya fara magana jikinta yake tsuma kota ina ga wata zufa na kar yo mata! Azahirin gaskiya ta tsani Irfan tsana ba kad'an ba, baida mutunci baida Imani a idon ta ko kad'an, ta yama zata fara gan-gan cin yafe mai, bayan irin a'bunda yamata, inaa bazan iyaba ta fada cikin har gagi .

Ammar dake nesa dasu kad'an ya tsaya yana kallon ikon Allah, tin sadda k'auran nan ya tu rashi ya Fad'i, yazo ta sowa kenan yaji an'bangajeshi da karfi ya juyo dan ganin waye .Moopy ce ya gani karcet harda gudunta ta k'araso ta janye Irfan mafarin dukan da k'aura yaso yiwa Irfan ya sauka akan iska wannan kenan.
Ammar ya'ce" wai yau Irfan ne Dur'kushe a'gaban mace yana bata Hakuri, lallai ka afka D'an uwa, dan yau ka dai ya son bakomi ke d'awainiya da Irfan ba sai So, ya dai barshi ya gama haukan ya fahimta da kanshi.

A'tsawace Moopy ta'ce" ban hanya in wuce kana b'ata man lokaci, gashi a'nata kiran sallah kaji?

Irfan ya sake rarrafawa ya'ce" to Dan Allah kice kin yafeman sai in'bar rayuwarki baki daya.

Moooy tai tsaki zata canza hanyan taji ance "KIZAMA MAI YAWAN YAFIYA UWATA KODA KIN KASANCE KECE MAI GASKIYA.

Ad'imauce ta juya suka hada ido da Ammar ya d'agamata kai tabbacin hakanne! Ammar ya k'araso wajen yace Moopy keda kanki kika fad'aman wasiyyar Babanki ta karshe dake ko ba hakaba? dan haka kibi umarnin shi kawai zai ji dadi sosai a makwancinshi,kinji ko?

Idon ta ya kawo kwallah a'hankali ta'ce" shikenan na yafemai Allah ya yafemana..

Dadi sosai Ammar yaji tare da cewa mungode kwarai Hajjaju Allah ya'kara daukaka yajikan Baba.
Tace Ameen nagode zan wuce.

Ammar yace to shikenan sai nazo yau ai gida zaki kwana ko?

Moopy ta D'agamai kai ta'ce" eh Insha Allah.
Ammar yace to ba matsala an'jima ko gobe zaki iya ganina, amma ina neman Alfarma wajen ki dan Allah in'ba takura.?

Moopy ta'ce" ka fad'a kai tsaye Yayana.

Amnar ya limshe idonshi ya'ce" mud'an karasa inda yake saiki fadamai hankalinshi zaifi kwanciya Dan A'llah.

Moopy ta d'an jinkirta ta'ce" to muje."

Haka suka isa wajen Irfan da kanshi ke kasa! moooy6 ta kalleshi sosai da taimakon hasken fitilar wayar ta .
Ammar ya'ce" bloody ana magana.

Irfan ya d'ago jajayen idanuwanshi ya saukesu akan moopy da itama ta tsuramai nata. cikin kasa da murya yace kiyi hakuri dan Allah mufeeda dan girman Allah.

Moopy ta lumshe idonta tare da fad'in bakomi Allah ya yafemana na yafema, tana fadin haka tai gaba a'bunta .

Wata irin ajiyar zuciya Irfan ya sauke fuskarshi take ta ďauki Annuri, ya d'ago da sassarfa ya rungume Ammar ya'ce" sakhallahu khairan D'an uwa Nagode matuka, yaushe rabon da in'samu sawaba zuciyata inba yanzu ba, lallai ka kuntata ma zuciyar bawa babban had'arine, wallahi bakaji natsuwar data saukar man yan'zuba "inda na gano itace Moopy insha Allah na rabu da ita kenan har abada, dan nason bazan iya Auranta ba, itama bazata soni ba.

Ammar yayi dariya ya'ce" ka hakura ko?"
To ai'shikenan dama ina ciki ganin itace Moopy d'inka na barma, amma yanzu zan koma Insha Allah.
Take fara'ar fuskar Irfan ta d'auke ya'ce" ba komi Allah ya barku, ya juya da sauri ya fara tafiya.
Da gudu Ammar ya bishi ya'ce" haba mana kai kuwa kyauta kaman fa, kace bakayi nikuma inayi.
Chapter 24 · 0% Book details