← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 32

Sashe 18

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba "Ya ce Allah sarki Allah ya gafartama su da namu baki ďaya". A'zahirin gaskiya d'an samari ni nayi niyyar barin ta duk sadda kazo a'karo na ba a'dadi, zan bar ta tama ka wakar kamar yanda ka keso, ada d'in ma na fad'ama ba zanso ta hada iliminta da wasu wakoki ba, amma a'yanzu nason Uwata zata iya 'karawa da kowa ta wannan fannin bani da haufi, sai dai har gobe a'bunda nikeso in fadamaka bazan iya barin ta ta tafi wajen ka ba Ita kadai...Amma namaka Alkawari zan dinga kawota dan dama yau zanje in'sawo machine, kaga fad'uwa tazo dai-dai da zama kenan .

Rafel "Yace Alhamdulillah!!!Wallahi Baba nama rasa da bakin da zan gode ma ni hakan ba matsala bane a'wajena indai zaka bartan..

Baba Ya ce" na bar ta Allah yasanya ku fara asa'a, Allah kuma ya tsarka'ke halshenku daga fad'in abunda ba dai-dai ba.

Rafel "Ya ce Ameen ya rabbi!! Baba inba damuwa ina so mud'an fara bitar abun a'yanzu, saboda a'gobe nike so mu buga wakar, jibi kuma a'fitar da ita Insha ALLAH..

Baba "Ya ce wannan ba matsala bane, bari in'ba ku waje. "yakoma daga bakin kofar yayi zamanshi yana hango su... Anan wanda aka kira da Fahad ya dakko wata doguwar paper yabama Moopy, itama tari ke tana jin shaukin abun a'ranta.. Rafel ya fara duba rubutun cikin sanyin muryar da Allah ya hore mai ya fara sarrafa wakar kamar dan halshan shi akayi, bayan yagama yacema Moopy koza ta iya yinta akan salon da yayi tashi. "ta d'a tamai kai cike da zakuwa."

Fahad ya kunna recording d'in wayarshi, "Na d'auka na fara sarrafa halshen na kamar wadda ta shekara tana waka, cike da kwarewa na ke zubo baiti " har wani juya kaina nake ina lumshe idona, Fahad baison sadda ya aje wayar akan cinyarshi ba, yabfara yiman tafi, dan na masifar tafiya da imanin shi ..."Rafel kam har hakorin shi na kurya ina kallo saboda fara'a, ina gamawa Rafel yasa ki kuka kamar yaro... Ya ce" wallahi moopy nason mu zamuyi na farko."

Fahad ya kunna wakar!! Masha Allah Baba kanshi Yace dake waje dan yaji zazzakar murya ta a'cikin waya....

Rafel yafita ya durk'usa akan gwiwar shi ya fara ma Baba godiya kamar anyi abun angama.. "Baba ya mikar dashi tare da nuna mai bakomi yana masu fatan alkhairi."
Sukaman Sallama cikin farin ciki suka tafi.!

Washe gari muka hau machine d'in Baba sabo mukata fi Studio Rafel, haka muka dage mukayi wakar mu cikin farin ciki da jin dad'i, dan sosai ni kaina ni kejina a saman gajimare..

Bayan sati d'aya Ammi ta sauka, tasamu d'an ta Namiji mai kama dani sosai..Ranar suna a'kasa mai suna Aminullah, zoka ga murna wajen Ammi ta haifi Dan Albarka, d'an da ba lau-layi." sosai Baba ma yayi murna nikai na ba a'barni a'bayaba har kaya nasai ma Aminu nai ma Ammi d'inki mai masifar kyau naba ta, haka ta amsa ba gode bare nagode a'ranar soye Ammi ta zauna zata fara soye nazo zan kamama ta ta kwabeni, tare da cewa ban isa in samata hannu acikin aikin sunan Dan Albarka ba.. Haka na koma gefe na raku be ina jiran Baba yafito daga toilet mu koma shagon mu, Bayan yafito ya cema ta kibata ta yimaki mana!

Ammi Ta ce" ban'so, ina amfanin hannuwa na .

Baba Ya ce" Uwata muje! Haka ya tasani gaba muka fito. Muna fitawa mota na fakawa," Rafel ne da kanan shi Fahad suka fito ko wannan su bakin su a'washe sukayo kai na, Fahad harfa daka tsalle ya rungume Yayan shi Ya ce" Yaya fad'a mata.."

Rafel yayi dariya Ya ce" Baba abamu wuri muzau na."

Baba ya bud'e shagon muka shiga suma suka shigo "Rafel ya zube kasa ya fara kwararo ma Baba Addu'a, tare da faďin Baba wallahi abu ya samu karb'uwa ya kar kace ya fiddo key din mota Ya ce" Baba ga Abun da aka bamu guda biyu na d'auki da'ya na ba Moopy daya, sai kuma kud'i million d'aya gasunan zan dauki rabi inba ta rabi..

Baba ya jin jina Abun tare da jin farin ciki a'ranshi Yace lallai Uwata an'fara abu asa'a, Allah yayi jagora, amma anan wajen bakai rabon adalci ba gaskiya ina na shikuma dan uwan naka ?

Rafel ya sosa kai" Yace Baba har na barmai wannan motar ni zan dauki sabuwar, kana kuďin danasa mu zan bashi wani abu."

Baba "Ya ce " ba haka za aiba!! kai ka dauki dubu dari hudu, kaba Moopy dari ukku, shima a'bashi dari ukku.. Haka kam akai Fahad harda duka wa yaman godiya, rana daya sun samu manyan kyautu'tuka," nace masu bakomi."
Rafel ya fiddo wasu Paper's yasa ke ba Baba "Ya ce "Baba wannan ma wata kwangilar ce muka samu zamu sake wasu wako'kin". Baba Ya ce "kai Masha Allah! Allah yasanya Alkhairi ya kiya'ye halshen ku.. suka amsa suka mana sallama muka rabu cike da farin ciki..

Baba ya kalleni" yace Uwata kinga Abun Allah ko.
Insha Allahu saikin zama Abun da Duniya zatai alfahari dake, yanzu mu kulle shagon nan muje wajen ginin ki muji akwai wani Abun da ake bukata, kinsan kuďin sunfara kasa yanzu bai fi million d'aya ba, dan ma munfitar dana tafiyar mu hajji.
"Nace to Baba duk yanda kace."

Baba ya tashi ya fiddo mashing dinshi na haye muka tafi har goruba, muna zuwa muka iske Alhaji nan tsaye yana daukar gidan dake opposite da nawa photo, yana ganin mu ya k'araso wajen Baba yana maida wayarshi, suka gaisa.. "Yace ma Baba wallahi kana raina yanzu nike da burin kiran ka.."

"Baba Ya ce" ikon Allah Alhaji Allah yasanya muji alkhairi.
Alhajin Yabce" ameen Alkhairin nama, Wallahi kaga gidan d'ana yau an'kammala shi kasancewar jibi zai shigo nageria, to an samu kaya da yawa wanda sukai saura nace ma ma aikatan nan,su kwasa suciga ba da gina ma Mufeeda, to kaga cikin ikon Allah abu yayi har sun hada komi penti ya rage.

Baba yasaki baki yana kallon Alhajin "Yace Alhamdulillah wai kana nufin cikin wata daya har an kammala gina gidan nan ?

Alhajin yayi dariya tare da "cewa k'araso kagani" yayi gaba muka bishi a'baya yana zuwa ya tura kyauren yashiga muka bishi Masha Allah nace ganin yanda gidan ya mugun tsaru komu an'sanya harda shukoki masu maseefar kyau da wajen arbana motoci, gidan baki d'ayan shi flat guda ne.. Haka muka shiga d'aku nan muka ga falo biyu ne sama da kasa, daga sama akwai dakuna biyu k'asa ma d'aki biyu a tak'aice dai wajen ya maseefar hadu wa dai-dai da benen gidan abun kallo ne .

Baba ya duka ya fara ma Alhaji nan godiya, tare da dauko key d'in motar da a'kabani yaba Alhajin" Ya ce "Alhajin yace kasama ta Albarka yau aka kawomata shi.

Sai naga Alhajin yayi kicin-kicin da fuska tare da cewa ma Baba wai kana nufin saurayin ta yamata kyautar mota?

Baba yarike haba" Ya ce all6ah yakiya ye Alhaji taya saurayi zaima budurwa kyautar mota a'a Wallahi waka ta fara shine sukayima wani dan siyasa wakar yabasu kyautar Abun."

Alhajin yarike baki tare da cewa yo malam ai wajena akasai motocin nan wallahi, kason sana'atane, tabbas Sanata bello awaje na yake sayen motoci shekaran jiyama ya aiko aka dauki wayannan guda biyu ko, kai nakau yi maki murna ashe ke ki kayi wannan wakar data zaga'ya Duniya cikin sati d'aya nikai na dabana sauraro nakau saurari wakar nan wallahi, Allah ya'kara basira.
Baba yace ameen Alhaji.

Alhajii yami komin key din "Yace Dota Allah yasanya Alkhairi, wato sabon gida sabuwar mota ko?
Nakar ba nai dariya muka fita! Baba kece man Alhaji to yanzu wazai yi fentin dan gobe zan kawo kudin.

Alhaji Yace ba matsala kawai kaba da gobe ma war haka zaka iya zuwa ka iske an'gama.

Baba yazaro dubu dari ukku da a'kabani yaba Alhajin tare da cewa ina fatan sun isa..

Alhaji Ya yi dariya tare da zarar dubu dari da hamsin yamikoma Baba dari da hamsin, "Yace "wayan'nan sun isa, dan ma za a'hada da wayarin din nepa da sunyi yawa".

Baba Ya ce "to Masha Allah! Allah ya'kara zumunci sai goben in munzagayo.

Alhajin Ya ce" bakomi Allah yakaimu'

Muka hau machine zamuyo gida muna yaba mutuncin mitumin" nace Baba gaskiya mutumin yasan ya gudum'muwu sosai"Baba Ya ce" ai Uwata badan Abun da ya bada ba da ina tabbatar maki da cewa Wallahi sai million din nan tashige, babu Abin da zamu mashi sai fatan gama wa da duniya lafiya, ko bayan raina Moopy ban amince kiyi watsi da mutumin nan ba, ki ďaukeshi tamkar Uba kin ji ko?" nace to shikenan Baba Insha Allah ".
Munyo nisa da tafiya munzo Kofar Durbi "nace ma Baba wow Baba kaga wasu daka dakan kujeru a'cen da gadon su..

Keeee Baba yaja burki muka juyo muka dawo wajen masu kujeru nan, kamar wasa muka shiga muka tambaya suka hadamana kud'in harda na gadon dubu dari takwas, sosai muka yaba da saukin su dan sun maseefar hadu, harda dinning dinsu Baba yazaro kudin nan yace gobe za akwashi kayan zamu ciko sauran.
Nasaki baki ina kallon Baba nace haba Baba mizanyi da wayannan Uban kayan saikace Amarya?

Baba yayi dariya "Yace Wallahi Uwata jinki nike kamar jaririya sabuwar haihuwa.
In Allah ya yarda bazan bar Duniyar nan ba saina ga Rayuwar ki ta ingan ta. na share hawayen idona namai godiya muka hau mashin din mu muka tafi.

Washe gari ina gama dunkunan wata Hajiya data kawoman na bata, Baba Yace infito mu wuce.. Haka nafito muka biya muka ba masu kaya cikon su Baba Yace a'biyomu da kayan, haka suka loda ma motar su kayan ta biyo bayan mu har Gidana.
Chapter 18 · 0% Book details