← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 32

Sashe 29

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kin burgeni duk da jikanane amma kwara dakika nunamai kedin mai mutuncice, kuma baki damu dashiba, karki wani damu bazan rabakuba kinji ko ai kina sonshi ko?

Cikin kuka-kuka dariya Dariya Moopy"tace da gaske bazaki rabamu ba? wallahi ina sonshi matuk'a Inna, bantab'a fahimtar hakanba har sai bayan yabar ni, Rungume inna tayi tana cigaba da kuka.
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
ZAMAN TASHA
NA UMMY AYSHA
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
🅿�6️⃣5️⃣

""Tsohuwa ta fara bubbuga bayan Moopy cikin lallashi.
Bayan shigar Ammar office din Dr Gimba yace" Abokina yanaga mutamin jininshi ya haw sosai,ko akwai abunda yakesone?

Tsaki Ammar yayi ya fadaymai halin da ake ciki .

Likitan yace ok turomun matar tashi.

Fitowa yayi fuska a'daure "yace likita nason ganin ki'.

Cikin buguwar da zuciyarta tayi da mugun k'arfi tace ni?

Ammar yace eh ke.

Jiki a'sabule tabi bayanshi. Tsohuwa tace kai karku d'aukeni shawaraki mana, ni nan za abarni tsaye kamar bishiya aduwa, muje tare.

Haka suka jera suka isa har bakin office din. Ammar ya rike hannun Tsohuwa itakuma Moopy ta shiga ciki.

Tsaye ta iske raf'keken likitan nan yanata kai da kawo, cikin bacin rai yace saboda Allah yasamishi sonki arai shiyasa kikayi amfani da damar kika kuntatamishi? Ciwon zuciya hawan jini duk suntaru sun nakasamai rayuwa, to burinki yacika Irfan na gab dabarin doran duniya, in yaso sai kijika ki cinye ,duk wanda bai taimaki waniba Wallahi batayanda Allah zai taimakeshi,kinji na gayamiki.

Kuka sosai Moopy keyi" tace ka taimakaman Wallahi ina sonshi dan girman Allah ka gwadamun d'akin da yake.

Eh aikwara kije kimai kallon bankwana ko,ya kusa bar Miki duniyar kishakata, wuce muje yafada yana kunshe dariyar dake cinshi ganin yanda du ta gigice.

A'sab'ule tabi bayanshi suka fito ganin su Ammar bakin kofar yacemusu muna zuwa. haka yak'arasa da ita har bakin kofar d'akin kana yajuyo.

Cikin mugun sauri ta banka k'ofar tashiga ta rufe harda sanyamata key.

Kwance ta ganshi sanbal kamar gawa, cikin sauri ta k'arasa wajenshi bata tsaya komiba ta faďa a'kanshi ta fashe da kuka, kirjinshi tafara kaima Duka da gyalenta tana kaci nasara akaina kaci nasara,kasa na fad'a a'tarkon sonka da kaunarka kana zaka kwanta kafara k'ok'arin barina,in katafi dawa kakeso in rayuwa, katashi dan girman Allah mijina,duk duniya bayan Abbah banda kamarka da iyayenka, mahaifina na sonka dole in soka, Dan Allah katashi inma wasa kake kadaina mana haka mana, tafada tana rushewa da kuka sosai tana jijjigashi.
25/03/2022, 22:30 - Khadeejaht Salisu Fari: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
ZAMAN TASHA
NA UMMY AYSHA
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
🅿�6️⃣6️⃣

"""" Wash zakimin rauni fah.
Irfan ya faďa idon shi a'rufe .

Murna takama moopy "tace to katashi mana dan Allah.

Yace um um hmm cikin shagwaba .

Kunya takama moopy da sauri ta juya baya tayi shuru jin kato na shagwaba.

Nason dama kinasona Wallahi koshi Imran bakyama son dakikemun, amma saboda kibani wahala kikuma ba kanki kika tsaya jan aji ko? Moopy kinfiso kita fusatani muna fad'a ko?..

Aa Dan Allah kayi hakuri nidai komi yawuce, kadaina tina baya mu fuskanci abunda ke gabanmu.

Irfan yace to juyo mana.

Juuowa tayi ta zubamai kyawawan idanuwanta

Ahankali yafara bud'e idanuwanshi da sukaui jawur ,saboda tsanani ciwo,nashi yazubamata yana kallonta.

Kunya ta kamata" tace ya akai kason najuya kaidama idonka rufe yake.

Sonkine ya sanar dani yabata amsa yana tsareta da ido.

Murmushi tayi ta'ce" to bari intafi gida Allah yabaka lafiya.

Da sauri Irfan ya tashi ya cire k'arin ruwan dake hannunshi" yace wallahi kafata kafarki" .

Moopy ta juyo tace aa nafasa auranka,kai raggon mazane daga wasa saika kwanta jinya, tafada tana kaima kirjinshi duka.

Dariya yayi yace ahaka kika ganni kika kyasa yam mata, harda kukan kina katashi mijina.

Dukan wasa ta fara kaimai tana ni bani bace sharri zakajamun .

Dariya sosai Irfan keyi kamar ba wanda aka kawo awa biyu data wuceba cikin jini.

Kamo hannunta yayi ya rike yace i love you my wife.

Moopy ta kashemai ido d'aya" tace me too my husband.

Rungumeta yayi cike da farin ciki "yace ina matukar sonki matata,da sonki natashi kuma dashi nike fatan komawa ga mahaliccina, fatana gareki kiyafeni da duk kan abunda yafaru a'baya Dan Allah, karki rikeni da koda kalma d'aya:ce Moopy,kisoni kwatankwacin son da nikemiki, na rokeki wannan alfarmar"..

Moooy ta'ce" Insha Allah zaka sameni fiye da yanda kayi tinani,fatana Allah yabani ikon yimaka biyayya da sauke duk wai nawinka dake kaina.
25/03/2022, 22:30 - Khadeejaht Salisu Fari: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
ZAMAN TASHA
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
NA UMMY AYSHA
6️⃣7️⃣
""" Kallo mai cike da tsantsar farin ciki Irfaaan ya bita dashi cikin lumshe ido ya kamo mazaunanta yarike cikin raunatata murya.

" yace nasani nason zaki iya fiye da haka danke din matar Aljanna ce Mufeeda, Allah ya biyamiki dukkan nin bukatunki na Alkhairi,ya jaddada rahma a'kabarin mahaifinki."

Ameen Mufeeda tace tare da share guntu hawayen daya zubomata .

Kiyi hakuri matata kidaina hawaye inba so kike inyi ba nima.

Irfan ya faďa cikin shagwaba yana turo baki had'i da diddira kafafuwanshi kamar yaro.

Dariya takama moopy tafaramai waka tana tafi tace shikenan kazama Baby.

"Baby wa"? ya tambayeta yana kashemata ido had'e da fara taka rawa.

Baby na mana "tace tana rugawa da gudu ta bud'e kofar tafita shima fita yayi da gudu yana dariya.

Tsohuwa dake zaune ta mimmike kafafuwa tayi ta gumi tana ADDU'A Allah yatashi kafad'un. Irfan lafiya.

Moopy ta yanko da gudu takusan bitasaman k'afarta ta wuce cikin farinci.

Mamaki yakama Tsohuwa kan ta juyo sai ganin Irfan tayi shima da gudu yana bazakije ko inaba sai nagama ganinki.

Ihu tsohuwa ta sanya "tace wayyo Lukuta kazo kakawoman agaji, da tashiga ta kasheshi sai k'urwarshi tabi yota, wayyo Allah nashiga ukku ni Mai Gadon Zinari .

Wata irin dariya Irfan yayi cikin jin dadin daya kasa b'oyuwa a'fuskarshi ya dora yatsanshi akan labbanshi yacema Tsohuwa shittt my wife na biyo ba fatalwa bane.

Ido Tsohuwa ta shiga rabawa jikinta sai rawa yake,ga kwalli ta zabgama idonta kamar mai kyanda.

Irfan bai tsaya wata wata-ba yakama hannuwan tsohuwa ya cigaba da rawa yanayin waka tare da gilgiza tsoyjuwa sosai kamar yasamu tsaranshi,tin Tsohuwa na kallon shi cikin tashin hankali harta suma, baima an'kareba saida Ammar yafito daga office din likitan yaga idon Tsohuwa a kakkafe.
25/03/2022, 22:30 - Khadeejaht Salisu Fari: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
ZAMAN TASHA
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
6️⃣8️⃣
NA UMMY AYSHA

"""Aguje Ammar yayo kanshi ya rike Irfan da k'arfi" yace Irfan kana lafiya kuwa ?tafa suma Dan Allah ka saketamana.

Jin abunda yace yasa Irfan Bud'e idanuwan shi yazubama Tsohuwa ido, shikanshi juwa yake gani na K'ok'ari kayar dashi, a'hankali ya kwantar da ita asaman kujerun dake wurin shima ya zauna, yajawo hannu Ammar da k'arfi har saida ya tsoratashi.

IRFAN ya saki murmushi "yace Ammar ta amince wallahi, sona take ba kadan ba itama,dan Allah Daddy ya taimaka ya barmu mu tare.

Ammar yace nidai ba wannan ba!miyasamu Tsohuwa ta sume hakane?

Irfan yace babu abunda namata,inaga murna take tayani shiyasa ta sheke.

Ammar ya tashi yashiga office din likita sai gashi sun fito tare, hannun likitan rike da ruwan roba yana zuwa ya duk'a akan Tsohuwa ya wanke hannunshi, ya D'ibi ruwa a'tafin hannunshi kana ya zubar, lemar da tarage yasa yashama fuskar Tsohuwa, amma ko gezau batai ba.

Hankali tashe Irfan" yace mikenan?

Likita yace karka damu tashiga furgicine.

Fuzge robar ruwan Irfan yayi da k'arfi ya kwararama Tsohuwa su duka ajiki.

Ii/hu ta sanya da mugun k'arfi ta tashi tana faďin shikenan sunkasheni, gani kiyama su suna Duniya suna karantamun Inna A'a D'ainakal k'ausar, Allah yashayar dani ruwan Alkausara,to nasha har nayi wanka. wayyo yar cakwal kinji Dad'i kin rabani da duniya hankalinki ya kwanta, Banga D'an Irfanu ba ta fashe da kuka.
25/03/2022, 22:30 - Khadeejaht Salisu Fari: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️
ZAMAN TASHA
NA UMMY AYSHA
6️⃣9️⃣

""" Dariya sosai likitan yayi yatashi tsaye ya rike hannun Tsohuwa" yace mike damunki Inna"?

Tsohuwa ta Buďe ido ta ganshi cikin fararan kaya, wani dogon fitsari ta saki kamar macen Doki, Ciki kyarma"tace RABBIYALLAHU LAZI KHALAK'ANI..

Ammar ya fashe da dariya tare da "cewa to uwar tsoro Aduniya kike, mutum ya tsufa amma sai son zaman duniya, bud'e gamu gabanki inma mutuwar kikayi gamu mun'miki Rakiya.

Ahankali Tsohuwa ta Buďe idonta fess ta saukesu akan Irfan daya fada wata duniyar sai murmushi yake yana lumshe ido, kai da gani kason cikin shaukin soyayya yake mai wuyar fassarawa.

Rai ɓace Tsohuwa tayi kanshi ta sakar mai wani rankwashi mai mugun k'arfi.

Wash "yace yana dafe kanshi tare da binta da kallo.

Yadai my love ? Irfan yafad'a yana lumshe ido.

Afusace tsohuwa tace Ubankane Milo, Irfanu ni tsararkace dan ubanka dazaka furgitani? kanamun abun yan indiyawa kai ka D'an iska harda yin majaujawa dani ka yarfani da k'asa ko?

Irfan yace aa kiyi hakuri, abunda dai nikeso kisani anan shine matata ta amince dani 💯

Tsohuwa ta k'ank'ance ido" tace dama duk murna ce tasa ni ka kusan kassarani?

Eh mana soma nai inga kin mace inji daďin kwashe matata mu gudu dan nason kece zaki kawomuna cikas.Irfan yafad'a cike da zaulaya.

Kuka Tsohuwa ta sanya tare da lalubo wayarta "tace ungo lukuta latsoman number ubanshi zakaga an'sanya Wannan Yaron".

Murmushi likitan yayi yace kiyi hakuri Inna kinson ciwon so ya kwantar dashi duk cikin murna ne.

Ammar ma yace kiyi hakuri Inna murna yakamata kiyi shalelen ki yatashi ko ?.

Ahankali suka tsarata harta hakura.

Office ďin likitan suka shiga shida Irfan, yamishi yan tambayoyi bayan yasamu abunda yake bukata ya sallameshi,tinda an'samu maganin ciwon nashi cikin gaggawa.
25/03/2022, 22:32 - Khadeejaht Salisu Fari: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️
ZAMAN TASHA
♥️♥️♥️♥️♥️♥️
NA UMMY AYSHA
7️⃣0️⃣

Sallamasu yayi suka tafi gidan Tsohuwa su duka baki ďaya, suna zuwa Irfan ya faďa toilet yayi wanka yayi shiri cikin wasu kananun kaya masu masifar kyau, rigar light blue sai black din wando, sumar nan tashi tayi luf-luf gwanin kyau da sha'awa, turare yabaza kana yafito yana tako dai-dai kamar mace.

Tsohuwa tasha gabanshi tace ba gidan ubanwa zakatafi ?mizakaje kaimata kana baligi ka keb'e da ita?

"Wajen matata zani Irfan yace yana hura hanci.

Tsohuwa tace baka isaba shiyasanya na tura Modibbo da Musa Driver A d'akkosu, sudawo nan gidana da zama,kai kuma yau zaka tattara kabar mun gidana kaji na fad'ama, kanata huro katon kirjinka kamar katangar tantabaru.
Chapter 29 · 0% Book details