← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 32

Sashe 13

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Moopy tace "miyasameni ne wai saiceman kake ya jiki, nifa dan Allah kafadaman ya akai nazo nan gidan?....

Ammar yace "To gama cin abinci kana kiyi sallah sai kiji"..

Moopy tace bari inyi sallah to"bayan tayi sallah taci abinci suka zau na suna fira sama_sama anan Ammar kecewa "kanwata yakamata kibani tarihin rayuwarki ki?

Moopy tagyara zamanta tace "ka,wuce neman wannan alfarmar duk da banyi niyya fad'ama yan zu ba.".

Mal.shehu tela shine sunan mahaifinmu, yan nan Farin yaro ne, dake nan jahar katsina, sana'ar mahaifina dinki shima ya gadane a'wajen mahaifi shi malam ummaru mai sallah, mahaifina shika dai iyayenshi suka haifa tindaga shi basu sake haihuwar kowaba, Allah yarayamasu shi dasana'ar dinki malam ummaru yabiyama mahaifina kudi yayi karatun boko da isalama Amma bai waniyi zurfiba iyakarshi secondary School yatsaya, yayin da karfin malam ummaru yafara ja, dole mahaifina yafara hawan keken malam ummaru yana É—inkin suna samun abunda zasuci kuma Alhamdulillah basu taba kwan basu samu ba .
Watarana mahaifina nacikin É—inkin kayan yara na yan makaranta sai ga wata kyakkyawar bafulatana budurwa ta hadu kamar ita tayi kanta fara sol tashigo shagon, da maganarta irinta fulani tacema mahaifina ina wuni ko zaka sai fura da nono?

Mahaifina yazubamata ido dan baitaba ganinta ba yace eh amma daga ina kike kawo furar ne? kasancewar shi mutum mai kyankyami.

Tace gaskiya ni ba yar nan bace munyo gudun hijira daga yankin jiubiya duk narasa a'halina, daga ni sai mahaifina muke rayuwa sai shanuwar mu guda daya damuka tsira da ita, shiyasa na zaɓi fara sana'ar siyar da fura ina ta tsar nono ina sayarwa dan insamu abunda zanci nida mahaifina da yake kwance a'halin jiyya.

Mahaifina yatausayamata tare da faÉ—in to aina kuke anan da zama?

Da hannunta tanunamai wani kango da suke" tace acen nike rayuwa nida baffana...

Mahaifina yasake tausayamata" inda yace ta damomai furar hamsin nono na talatin sai sugar na a'shirin.

Cikin farin ciki tafara ciniki ta dama mai fura tayi kyau sosai tami ƙamai"
Sosai baba na yaji daÉ—in furar nan" anan yasake sayen fura yashiga yakaima iyayenshi.. a'takaice shakuwa mai karfi tashiga tsakanin mahaifina da yar fillo, dan daga bayama anan bakin shagon take zamanta da yar kwaryarta tana siyar da nono ta da fura, "Bayan shekara biyu maciji yasari baffanta yan unguwa suka hadu a'kaimai sitira mahaifina shine kan gaba wajen komi inda yar fillo tasha kuka ta gode Allah mahaifina yashiga yanemi alfarmar tadawo wajen iyayenshi da kwana, anan suka amince tinda ya macace baikamata ta zauna kango ba .

Bayan shekara daya da rasuwar mahaifinta baba na yanunama iyayenshi yana sha"awar auran yar fillo, iyayenshi basu wani ja maganar ba suka amince mai,anan aka tambayeta itama ta amince aka daura masu aure aka basu sashe guda daga cikin gidan kasancewar ginin d'ane da auransu da wata ďaya yar fillo tafara tsiro abubuwa kala_kala kullum mahaifina tsaye yake bakin kokarin shi amma bata gani, anan tacemai sana'arta ta fura da nono zata dawo yi,, "yace ya amince amma bai yarda ta tafi talla ba "tace bata amince ba gsky sai dai in ya yarda tadinga zaman shagonshi kamar da .
Shima yace bai yar daba amma zai iya lamunce mata tayi furar takai bakin shagonshi yasaida, Ammi" tace ita som dan macace marar yarda" haka sukaita samun saɓani daga baya iyayenshi suka shiga maganar inda suka bata hkr akan tayi umarni da abunda mijinta keso," nan tai tamasu rashin kunya akan sunfi son ɗansu a'kanta dan sunga ita marainiyace..
Babu wanda ya kulata dan sunga a'lamar fitina take nema "washe gari da sadakinta dake a'boye dubu biyar ta tafi ta siyo abunda xata siya washe gari tati furar ta tare da zuwa maďacin yan nono tasiyo nono ta mai kyau, kasancewar ta siyar da shanuwarta ta ɓoye kud'in ta tahad'a furarta, "mahaifina na zau ne shago sai ganinta ya yi ta ɗora kwarya akai tana asai fura. "Ranshi ya matukar ɓaci yace takoma gida kan ya zubar da fura" tace bazata komaba saboda ba shi yabata jarinba," ganin zata batamai rai ta ta ramai mutane yakoma shagonshi yakyaleta a'takaice haka sukaita rayuwa babu Dad'i..

Bayan shekara biyu ammi tafara kwaikwai mai masifar wahala, wanda yahanata neman kuɗinta duk yanda taso ta daure kasawa tayi daga karshe haka ta kwanta jinya cikin tausayawa mahaifina yakaita asibiti aka gano ciki ke jikinta dan wata hudu, sosai mahaifina ya yi murna inda yana zuwa yashedama iyenshi suma sukaji daɗi sun kusa ƙara yawa..

"Yana dawowa yafita yasiyoma mahaifiyata balango mai zafi da wainar shinkafa da miyar kanu, yakawomata yana zuwa yayi turus ganin ta a'durkushe tana yarfe hannu ga jini na malala ta kasanta, cikin sauri ya wurgar da ledar tare da tallabo ta yace ke lfy miyasameki? kan yace komi inna mahaifiyarshi ta faÉ—o É—akin dan taji salatinshi tana zuwa suka kama Ammi zasu fita, idon inna yafada akan da kakken bedin dake aje da ledar gishiri tadauki a'bin ta jujjuya tare da sakin salati tace minike gani haka hauwa'u da hankalinki zaki zubar da cikin ki saikace ba dan halak ba..

Ammi da azabar ciwo ya ishe ta tace natsani cikin yahanani neman kuɗina, ga wahala ina sha wlh saina fiddashi a'takaice haka sukaje a'sibiti a'kacemata ciki yafita amma tayi hkr zataga tana wahala kuma yana kumbura, har sai tayi wata ukku, a'bunka da yar karkara bata gane ba, haka tadawo taci gaba da jinyarta sai dai abunda ke bata mamaki cikinta na kunburi kuma yana motsi, amma datama inna magana sai inna tace yan cikin kine ke komawa mahallinsu dama likita yafaɗa, haka sukaitayi har cikin yakai wata tara kasancewar bata da jiki bai waniyi girma sosai ba, wata litinin Ammi tat ashi da mahaukacin ciwon ciki kankace mi tafita hayyacinta sai ihu take," inna tai tsaye kanta dan tason haihuwace tazo mata "Ammi sai saukati take tana faɗin mutuwa zatai, bata wani jimawa sai ga kan jariri ya turo" ita da ke zukunne batason sadda ta kwantaba jin abu ya dan nomata inna tai saurin karasa wa wajenta tare da hankaɗar da zanan dake jikinta, saiga yar kyakyawar jaririya ta sintilo tare da kyankyara kuka, ko uwa bata biya ba "Ammi jin kukan jariri yasata saurin tashi tana kallon inna tana kallon jaririn fuskarta ciki da zallar tsana da bacin rai.....✍️
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: ❤️💘❤️💘❤️💘❤️💘
ZAMAN TASHA
❤️💘❤️💘❤️💘❤️💘
NA UMMY AYSHA
💘❤️💘❤️💘❤️💘❤️
3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣

""Take jikin Inna ya É—auki rawa, taga irin kallon da Ammi ke mata cikin rawar murya "inna ta fara faÉ—in dan Allah Hauwa kiyi hakuri wallahi likit.....

"Ammi tadakama inna tsawa tare da faÉ—in iman shuru kina babba kina karya, wato kunyi a'mfani da duhun kaina kuka rainaman hankali ko, to kisani banyi niyyaba kuma bazan karba ba, yarinya kuma bazan bata no-no naba, kema kina dashi zaki iya bata" takarasa tana sanya hannu ta tura jaririyar da inna ta aje gefe cikin zane, sulbin ruwan faya da na ledar dakin yasanya jinjirar yin suluka daga cikin zane har bakin kofa," ta kyankyara wani mugun kuka" Inna tai kanta aguje tana É—ago yarinyar tasake yan yara kuka.
Ko ajikin Ammi saima kwanciya da tayi tana maida numfashi.

Inna" takarasa wajen Ammi da jaririyar dake wani irin kuka" tace haba dan Allah hauwa wannan laifin mumukayi maki bawai yarin yar datazo yanzuba, kijifa a'bunda kika mata ita'da bata son hawa batason saukaba, "likita yabamu shawarar mu ɓoyemaki dan yaga kinason cire cikin da yayi kwari jikinki, kuma hakan hatsari ne ga lafiyaki, shiyasanya mukai maki haka.."

Agalabaice "Ammi tace kema no-no ki dakika boye saiki fiddoshi ki bata tasha, dan nikam yanda natsani mutuwata haka natsani yarin yar nan wlh, saboda tadakusheman hanyar arzikina, da yanzu Allah ne ƙadai yason abunda zan tara.."

Inna" zatai magana saiga mahaifina yashigo!! yana shigowa yaji kuka jaririyar, da sauri yakaraso É—akin yana faÉ—in kai Masha Allah," shine Inna ko a'kirani" yakaraso da murnarshi yana washe baki .
"Inna taɗago idon ta Daya kan'kance tace ga a'bunda a'kasamu" Ta mika mai jin-jirar yakarɓa!!Yama jaririyar rikon da ba dai-dai ba na take ɗiyar ta kwalla ƙara, daga nan bata sake motsiba." cikin tashin hankali baba yamikama Inna yarinyar yana fadin Inna kallarta kamar fa bata lumfashi? ko nono takeso ?

"Inna takarbe'ta da sauri!!anan taga kafadar yarinyar tayi wani irin mugun kunburi tabbacin turatan da akai tasamu rauni" inna tazaro ido tana faÉ—in raunine jikinta ayi sauri a'kaita asibiti.

Baba yajuyo ya kalli Ammi data rintse idonta kamar mai bacci!!yace sannu hauwa tashi mutafi a'sibiti kema sai adubaki kinga jinjirama bata lfy.."danshi baison miyafaru ba"

"Inna tace kyaleta ta gaji muje in kaita!! haka ta saɓi diyar dabata numfashi ta ɓoye a hijjob suka fita, suka nufi general inda suka kaita dakin yara, Allah yasanya babban likita na nan" nan da nan aka karɓe ta a'kafara bata taimakon gaggawa".

Bayan awa biyu "likitan yafito ranshi a'ɓace yacema baba kubiyoni office " haka suka bishi jikinsu a'sanyaye dan sunga kallon da yakemasu bana mutunci bane.."

Suna shiga ko zama basuyiba yafara maseefa!! tare da kallon inna yace haba dan Allah tsohuwa, taya kin girma haihuwa ta kamaki bazaki zo asibiti da wuri ba, duba da jikinki karfi yafara yin kasa?

"Inna ta fashe da kuka tace haba likita ina ni ina haihuwa yarin yar nan" ni kaka;tace.

Likitan" yace to miyasanya mahifiya ta ba ta zoba?

Inna tai shuru" sai cen kuma tabasu labarin a'bunda yafaru .

Sosai ran baba na dana likitan yabaci!!inda likitan yace aiko sai yakai ƙara Ammi an kwatarma jariri yar hakkinta .

Baba'na yabashi hakuri tare da cewa Ammi ba cikakkiyar mai lafiya bace, tana da matsala iska Ammi yason inta falfado komi zai daidaita.
Dakyal suka shawo kanshi ya hakura! tare da basu do'ko-ki kar ama yarin-yar wanka sai dai agoge jikinta, kar a'kuskura a'goyata sai dai adinga kwantar da ita," daganan yabasu magungunan yafita yadakkomasu yarin-yar yamikama inna. "inna tace likita yanzu duk sanyin nan haka za abarta baza asamata kayaba?
"Likitan yace tabbas muddum lfy akeso tasamu" kuma tinda kinga uwarta mahaukaciyace dole kidinga sanya ido dan zata iya sake karya ta wlh.
Baba yamashi godiya suka tafi.
Chapter 13 · 0% Book details