← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 32

Sashe 22

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tinda naji wannan magana tashi bansake tina komi ba har saida nakwashi kwanikka, ni ba matatta ba ni ba mai lafiya ba, ni dai naga wata Tsohuwa ba Baba Asubi ba tana jin'yata, amma bazan iya cewa ko ya take ba saida Alhaji yasa aka dungaman rubutu kana na fara dawowa hayyacina,bayan navdawo dai-dai na zauna naci kuka na gode Allah, ba mai rarrashina na hakura na daina, ban son kuma a'dadin kwana nawa Mahaifina garai ba, saida na tambayi mai kula da Baba dan nabar ganin tsohuwar nan, yau watan Mahaifina nawa? Yaceman yakai kuson biyu kana na'sani.

Haka rayuwa tai ta tafiya bana um bana um-um, kullum daga gidan Alhaji ake kawoman abinci duk da bawani na kirki nike ciba, su Rafel kullum na zagaye dani suna ban baki, ban'kara ganin imiran ba ban kuma damu da in'son inda yake ba, saboda nayi rashin Mahaifi na hyakura banga wanda zanrasa ba in kasa hakuri.

Na samu wata ukku cur cikin kunci daga baya na fawwala ma Allah komi na dawo naci gaba da abubuwan rayuwata, inda nazama hamshakiyar mawakiyar da duniya keji dani, har na kara yin Wak'a wa wani mutum yaban mota Babba, haka na had'asu biyu kud'ad'ena kuma na tambayi Alhaji nan daya zama Mahaifina duk sati yana leko ni ya tafi, nace'mai ina bukatar gina Filina zanyi Studio na kai'na." yace man ba matsala shi yataima kaman aka hada komi a wannan karon'ma yasake man gwaninta dan wasu abubuwan duk shi yasaman" har lokacin mutane murya ta suka sani basu son ni a'fuska ba, dan banda bukatar hakan, kasance wata mai ZAMAN TASHA abun zai zama tso'gwami.

Bayan ankammala ginaman gidan gonata da Studio na fara zuba abubuwa kaji dasu kifaye Alhaji yace man ga mutumin daya kula da Bab'ana da yana jinya zai din'gaman gadi, in yaso y'ay'anshi dake gidanshi zai barman'shi ya dawo gida na yanaman gadi, na yarda da hakan dan nason Alhaji bazai man abunda bai dace ba, haka na hada Buzaye biyu Yaya da k'ane d'aya a'gidana d'aya a'gidan gonata.

Fahad shiya zameman garkuwa Studio na komi shi keyi,yayinda Rafel yasamu wani yasanya Allah yasama sabon wuri na Al'barka cikin yan watanni manyan mutane suka fahimci wajen, take na dinga kwasar ciniki naita am'fani da ribar ina kara habbaka wajen harya zama yanda ni kes, nasamu manyan kud'ad'e agidan Gona ta, hakan yasa a'sace naje unguwarmu nasamu kusa da masallaci na bada aka'faraman bohol dan inaso yazama sadakhatul jariya ga Baba na,ina fatan Allah ya sanya ladar takai a makwancinsu shida iyayenshi, bayan an'gama mutanan unguwa sukai tasa Al'barka dan basu son wayayi ba dan ban'ba ma aikatan wannan damar ba, nashiga Unguwar dan Sallamar masu aiki,na fito kenan a'mota kamar daga sama naji an'saki salati tare da "fadin ba shakka, ashe tir'bar daya d'oraki kenan kamin yabar duniya .

Da sauri na waiga naga Ammi ce da kaya a'kanta hannunta jaye da Aminu, "Na durkusa zan gai'data tace saboda bani na kawoki duniya ba ai'kwara kiman gaisuwa haka, maza to ki biyoni gida kamin in d'agamaki no-no.

Nace subhanallahi ta sakar man harara tare "da f'adin wannan motar ubanwa yabaki?
Nace wajen sana'atane a'kabani..

"Tace da kyau!! tayi gaba dole na fito na biyota muka shiga har gidan mu naita kallon gidan kamar zanga Baba, banson sadda hawaye ya sakkoman ba.
Tsawa da Ammi ta dakaman yasanya na furgita na fada d'akinta jikina na rawa, nazauna kasa ina gaisheta bata am'saba tace yawwa kikace motar kice ko? kuma kin iya kenan.?

"Nace eh Ammi nike janta.

Tayi murmushi" tace to ai shikenan kinga faduwa tazo dai-dai dazama, yanzu tashi muje nan gidan Magaji mai gyaran radio.

Naji daďin yanda Ammi taman hakan yasa na bita har gidan muka gaisa dasu tace dan Allah Big na nan ?

Maman shi "tace bayanan Yar Fillo"da yake haka suke cemata, muka fito har munzo soron gidan Ammi" tace man jirani inzo" nace to nai tsaye ina mamakin canjin danasamu yau awajen Ammi, harna fara tinanin kila ta barni in dawo gidan, inci gaba da zama gabanta, kila tana tausaya man ne ganin Babana ya rasu.

Ammi" tace muje ki kaini TASHA nan ta kofar Guga.
"Nace to Ammi"

Muka karasa wajen mota na budema ta baya ta hakimce, tare da zaunar da Aminu a'kanta ta namai wasa cikin farin ciki" sosai abun nasu ya burgini nace Allah yajikan Baba na.

Na tada motar muka tafi har TASHA, muna zuwa Ammi ta sauka tare da ceman biyoni.
Nabi bayanta mukaje tayi kwatancen wanda take nema, nan take suka had'ata da wani luteten mutum, yak'araso yana aa Yar Fillo akwai no-no.

Ammi ta ďaure fuska tare da cewa tai'mako nikeso kaman, yarinya ce gatanan mota gareta, ina so tazama yar ZAMAN TASHA saboda ta nemo man abunda zanci nida Yaro na.
Big yayi dariya ta yan duniya "yace an'gama ai ita har kar kuÉ—i ba mace ba namiji,dan haka in yanzu ki keso a'fara zamu fasa da ita kawai.

Ammi tace ta kwana gidan sauki, sai dai kuÉ—in halak nikeso bana haram ba, bada motar nan ta taba da taku zaku bata, saiku dinga fitar wa.

Big "yace ba damuwa, take ya juya ya jawo wata gof yayi parking d'inta wajena,"Yace shige akwai full lodi zamu aje taki anan in'kin dawo kya É—auka, zaki biyoni a'baya.

Ammi ta kallan ta daure fuska tare da cewa maza ki bishi yanzu nikeso ki nemo ki kawoman,dan nagama wahala nari ga nasaida komi nawa banda wani jarin kirki,maza kibishi kamin in tsinemaki, wato kin'ban wahala da cikinki yanzu kuma kin kud"ance ki nata faman shakatawar ki da kudin haram ko..?

"Na fashe da kuka nace yanzu Ammi ni zaki kawo kice inyi ZAMAN TASHA
? kawai dan in nemo maki, Wallahi na maki Al'kawarin zan dinga kawomaki komi na rayuwa batare da na zauna a'nanba,saboda duk wanda ya ganni anan mutuncina da darajata zai zube..

Ammi tayi salati tare da faÉ—in shige kuje na cemaki kamin in maki Allah ya isa.

Haka na shige mota ina kuka rai a'bace na figi motar nan batare da na tsaya jiran kowaba,ita kanta Ammi saida ta tsorata balle mutanan dake ciki, take TASHA ta dauki ihu suna "fadin Falau Yar Cara's, ba tasu nikeba haka na dauki hanyar Jibiya duk da banta ba zuwa ba, Amma nason hanyar da take. sosai nike gudu yan motar duk suka rude wasu harda kuka saida naje magamar Jibiya kana na sauk'aka, na juyo da jajayen idanuwana na tambayi wani saurayi ya gwadaman hanya, na yanka da su aguje har TASHA, ina zuwa TASHA wani yataso yace yawwa kece Big ya yima lodi ko? Nai banza dashi na fita na juya, mutanan nan suka filfito suna godiyar Allah, "nayi kasa da kaina tare da faɗin kuyi hakuri dan Allah, bawanda yaceman komi nafara ƙoƙarin shiga motar, mutumin yakawoman wasu mutane suna gama shiga ya mikoman kudi na karba nayi Katsina, anan na samu Ammi tsaye nayi parking din motar tare da fitowa na bata kudin zan shiga motana "tace idan baki dawo gobe ba Allah ya isa tsakanina dake no-no na da kika sha ban yafemaki ba.

Zuciyata ta kafe banajin komi banko kalleta ba, nafada motana nayi gida, haka nasamu Fahad tsaye yanata zagaye ya
Taso a'gigice ya tambayeni ina naje ?"ban b'oye mai komi ba na fadamai," sosai ya tausayaman tare da faÉ—in inyi haykuri da halin Ammi wata rana sai labari.

Haka rayuwa tai ta juyawa nazama mai ZAMAN TASHA karfi da yaji, Ammi ta samu wani Tsohon mashayi ta aura, tare da sai da gidanmu batare da sanina ba," tace gadon Aminu ne zata juya;mai, ta tare gidan wanan mashayin banso hakaba amma banda yanda zanyi,mijin Ammi yawareta ita kadai wata unguwa wata rana yabi dare ya kwashe duk kuÉ—aÉ—en Aminu yakama gabanshi, tashin hankalin da Ammi ta shiga yakusa sata hauka, nidai kam ban ma son yazan cema ta ba nashareta naci gaba da kawomata kuÉ—i yanda take so, daga baya ta Dangana ta Hakura, tasaman dokar duk in zani in biya gidanta wani tsohon É—akin ta wareman taceman ga kayanan in'dinga sawa rayuwar gwanjo tane kar a'ganni da masu kyau aki shiga motar.." hakan takasance duk in'zani zan biya in aje motana in sanya tsaffin kaya, ahaka har ammi ta haifi cikin da mutumin yabar ta dashi ya gudu nayi nayi in'bata kuÉ—in hidimar ta kiya, sai tamaidaman jigila so ukku arana a'haka har ta haifi Amina aka yan'kamata ÆŠan a'kuya, yanzu maganar da nikema Amina shekara biyar Aminu nada goma sha biyu, kaji labarina yah Ammar.

Ammar yace tabbas labarinki akwai ban tausai, dakuma ban mamaki, to yanzu ina Imran yake?

Moopy ta daga ka faÉ—a" tace taya zan sani har yau ban taba tambayar Daddy shiba, dan gaskiya yanzu ya kan daÉ—e bai zo wajena ba saboda yanayin ai'kinshi.

Ammar yayi murmushi tare da cewa ina zuwa..

Tsohuwa ta fasa kuka tare da fadin wallahi tallahi kece kece . ..✍️
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘❤️💘❤️💘❤️❤️💘
ZAMAN TASHA
💘❤️💘❤️💘💘❤️❤️
NA UMMY AYSHA
❤️💘❤️💘❤️💘❤️💘
🅿�4️⃣5️⃣&4️⃣6️⃣

""""" Moopy Ta'ce"nice mi?
Tsohuwa ta share hawayen ta ta'ce ina zuwa bani Wayata la'tsoman Alh.khabir.
Moopy ta karb'a ta gano Number ta kira. yana fara ring taba Tsohuwa ta'ce ya shiga.

Tsohuwa ta'ce" barshi zai kirani baya D'auka in yaga nakira kan'tama rufe baki wayarta ta fara Ring ta tashi tashige D'akin ta tare da banko kofar tace Halo Khabir kana jina kuwa?
Daga cen bangaran yace ina jinki Hajiyamu ina wuni?

Tsohuwa tace kai tureman wunin nan yah banyishi lafiya ba kaganni nan nasha kuka daza atarashi sai yacika palon nan dan tinda nagama asuba nike kuka har yanzu bai tsayaba..

Alh yayi Dariya yace ikon allah Hajiya mi yafaru haka ko yan NEPA dana turo suka maki wani abun?

Tsohuwa ta'ce" su D'in banza kai yaro ina yarin yar nan danayi jinya sadda babanta ya rasu ta kusa da gidan Irfanuuu...

Alhaji ya'ce"eh nagane wannan satinma zanje ganinta tana nan lafiya lau.

Tsohuwa ta'ce" nizan fadama kau tana lafiya ya zancen maganar ta irfanu yakamata fa ka fadamata gaskiya lamari tin kamin kazama dattijon banza a idonta...

Alhajin yayi shuru yace Hajiyarmu wani abu ya farune?
Chapter 22 · 0% Book details