← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 32

Sashe 31

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsohuwa ta'ce" kuzo ku zauna Kazallaha najin zafin in'gaisa daku baya iya jurewa dan hassada, dan yaga shi bukumishi oyoyo ba kamar yanda kuka mun ,Ai dan kunson ban cucekuba ko? Ta faďa idonta nakan Ammi da babu abunda take kallo sai Moopy da itama tinda suka had'a ido ta koma bayan Irfan ta lafe.

Ammi tace Mufeeda zogareni, Ni Ammin kice zogareni yarin yata yar Al'barka.

Kuka Moopy tasa ta'ce" Dan Allah yah irf6an karku bari ta sake karyani, Wallahi nima banson mene yasa na manta da itaba nadaina zuwa TASHA, bansaniba Wallahi ku faďamata.

Kuka Sosai Ammi keyi ta tashi tayo wurin su.

Ido rufe Moopy ta rike Irfan gam tana kuka kamar ta shid'e .

Illahirin jikinshi shikanshi rawa yake, Saboda bayason abunda katab'amai matar shi."

Cikin k'asa da murya "yace Ammi Dan Allah kija baya kaďan.

yafada yana watsamata idanuwanshi da sukayi jawur.

Cak Ammi ta tsaya bata k'arasa ba.

Daddy ya'ce" kowa yakamata ya zauna ."

Ammi ta dawo wurinta ta zauna Irfan yaja Moopy kusa dashi suka zauna tana ta sauke ajiyar zuciya....

Yanajin kamar yashige da ita D'aki ya bata kulawa ta mussamman, Ya lallasheta ya fahimtar da ita komi daya wakana.

Bayan sun zauna Daddy ya fad'amusu komi, SHIMA Irfan ya fad'amusu yanda sukayi da Amina bayan sun dauketa a'matsayin matatta.

Moopy ta gangaro wurin Ammi ta rungumeta Ta'ce" Ammi nah yanzu kin yarda dani a'matsayin Y'ar ki?

Ammi ta rungumeta Ta'ce" kwarai ko ďiyata ina sonki dama cen rud'in zuciyane kiyi hakuri."

Moopy na murmushin jin wani sanyi na ratsamata zuciya! Wai itace yau jikin Mahaifiyar ta kwance ba kwatsa ba kyara balle Hantara, Su Amina ma matsowa sukai suka rungumeta suna share Hawaye.

Tsohuwa sai washe baki take ta kalli Mamy Irfan da batace komi ba.

Rai a'ɓace Tsohuwa" tace ke kuma kinsaki halittu kamar an zanaki kina kallon mutane dai-dai kinkasa cewa komi."

Mamy tai k'asa da murya Tace" Inna nikuwa mizance
Baya ga fatan zaman lafiya da zura'a d'ayyi ba.

Baki Tsohuwa ta washe ta''ce to na yanke tarewar'su nan da wata biyu insha Allah, ke kuma ta nuna Ammi tace kije da diyarki gidanta kuzauna ki kula da ita, Tinda batadawa wanda ya fiki,kimata gyara na mussam man ciki da waje, Waima kinmason kayan gyaran jikin kuwa?.

K'asa Ammi tai da kai allamun halin fulanin ya motsa.

Irfan ya zagayo ta wurin Tsohuwa" ya'ce Dan Allah karkimun haka, Kar kirabani da ita har tsawon wata biyu zan iya rasa raina, Ni ko ba agyarataba inaso Wallahi.

Ido tsohuywa ta gwalo taxes to to D'an Iskan Ango na magana, yace za a'wayi gari aga yayi bindiga muddum ba abashi matarshi ba koda ba a'gyaramai ita ba.

Dariya su kayi Daddy ya'ce" Inna ni da abinda nagani dama abar tarewar ta nan da sati biyu, lokacin yayi dai-dai da samun hutun su Imran, kinga sai suzo ayi hidima dasu...

Tsohuwa ta'ce" bakomi Allah ya kaimu.

Mamy ta'ce" inaga zansanya wata k'awata ta turoman Falmata yar maiduguri ce ,insha Allah zata mata komi da akema Amare, kamin lokacin zakuga yanda zata murje.

Ammi tayi kasa da murya Tace" to Hajiya Allah yak'ara girma.

Murmushin kawai Mamy tayi dan itadai badason ranta za'ace d'anta ya auri yarinyar da tayi ZAMAN TASHA , Amma kuma bazata ja da hukuncin Allah ba .

Daddy ya mike ya'ce" Imran zaizo da kayan lefe sati mai zuwa insha Allah, kai kuma Irfan saika tambayeta abunda take buk'ata nagame da abunda zasuyi.

Mamy ta mike tana tafiyar k'asaita ta musu sallama tsuka tafi.

Tsohuwa tayi tsaki ta'ce" mace yar dukus kamar curin fura sai isar banza, Daga gani bataso kuma sai anyi Tinda ni uwar ubanshi ina so..

Ammi da fuskarta ke cike da fara'a na ganin iyalin ta lokaci guda ta tashi ta'ce" Inna muna godiya bari muwuce".

Tsohuwa ta'ce" kai babu inda zaku sai da daddare yanzu ku zauna muyi fira kana.

Ammi tanajin nawin ta haka suka zauna suna fira.

Har lokacin Sallah yayi suka tashi dan yo Alwallah.

Irfan yaji masifar Dad'i ganin Ammi ta tashi, yayi- wuf yaja hannun Moopy dake tsaye suka fita waje,Mota ya sata ya jata da karfi yabar gidan.....
25/03/2022, 22:32 - Khadeejaht Salisu Fari: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
ZAMAN TASHA
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
UMMY AYSHA

7️⃣5️⃣&7️⃣6️⃣

"""Gudu yake da mota sosai batare da ya juyo ba.

Moopy ta juyo cikin sassanyar muryarta ta'ce" Honey nah ina zamujene haka ka keta gudu kamar zakasaceni,? takarasa cikin sigar shagwab'a.

Sauran kad'an motar ta kwacema Irfan jin sunan da ta kirashi.

Wuri ya samu yayi parking ya kalleta sosai idonshi cike da zallar soyayyar ta ya'ce" Matata zakikasheni da salon'ki fa,bari muje zakigani.

Murmushi kawai Moopy tai ta jingina da kujera tana tino rayuwar ta tabaya gashi yau komi ya shud'e.

Jin mota ta tsaya yasata d'ago kai ta kallo inda suka tsaya.

Ido ta zaro ganin su bakin get din wani rafkeken gida da za'a iya sanya nasu ciki.

Ta kalli Irfan" tace Honey Nan mizamuyi?"

Ido yakashemata yace" Sunna zamu raya."

Sosai jikinta ya d'auki rawa idonta ya cika da kwallah" ta'ce Dan Allah karkamun haka mana, Kabarni in samu damar zama da mahaifiyata mufahimci juna.

Irfan yayi dariya tre da danna wani remote take get din yayi sama suka kutsa kai.

Gidane nagani na fad'a yaci uban nasu kyau so Goma , Bud'ewa yayi yafito yazagayo inda take ya bud'emata tare dasa hannu yajawota ta'fito illahirin jikinta rawa yake.

Dariya taso kamashi ya danne tare da russunawa a'kunnanta yace kinga yanzu wannan farantamun din da kikayi kadai kinsamu lada, kinsanya hannunki cikin namijin ki ko?

Moopy ta dago kai ta kalleshi batare da tace komi ba.

Palon gidan ya buďe suka shiga.

Masha Allah ta furta lokacin da taji sassanya kamshin d'akin da yasha kayan alatu . lallai ko Baba da baban shi, Duk yanda take kallon kyan gidanta ashe akwai wanda ya fishi...

Irgan ya budemata ko ina tare da haurawa da ita sama komi yaji ga kujeru na alfarma da gadaje.

Irfan yace Baby nah gidan nan yayi kyau kuwa?

Moopy da tamanta da abunda yace zai mata" tace sosai ma kuwa,dan yafi namu kyau.

Alhamdulillah Irfan ya'ce' Tare da cewa da bayyi ba da tabbas sai an'canza miki tsarin da kikeso, insha Allah agidan nan zamu tare .

Moopy ta rife ido tare da fita da sauri daga falon dan taji kunya matuk'a.

Irfan ya biyo ta cikin sassarfa tare da kamo hannunta yasata mota suka fita suka dauki hanya ba wanda yacema kowa komi.

Gidan Tsohuwa ya maidata ko shiga bai ba ya tafi yana shaukin kasancewar shi da iyalinshi na rana d'aya kaďai.

Bayan myufee tashiga babu wanda yacemata komi sukad'anyi fira sama -sama sukama Tsohuwa sallam suka tafi.

Rayuwa suke mai cike dajin Dadi.

Ammi ta kama yaran ta tarike sosai tana kula dasu kamar babu abunda yafaru a'baya,tanajin inama tin farko haka sukayi rayuwar su,.

Shakuwa ta mussam tashiga tsakanin Moopy da maman ta cikin sati biyu, Gefe guda kuma mai gyaran jikin da Mamy tayi Al'kawari kawowa ta kawo ta taciga ba da gyara Moopy gyara na mutun ci .

Saura kwana biyu tarewar su sukayi gagarumin shagali, Inda su Rafel suka nuna bajintar suka hada dan xasu.

Washe gari akayi walima aka kai Amarya d'akinta bayan kukan da tasha kamar zata shid'e.

Da daddare Ammar da Imran sukayoma Ango rakiya yazo wurin Amaryar shi, Bayan yan barkwanci suka musu Addu'a da fatan ALKHAIRI suka tafi.

Irfan ya rakasu yadawo tarel da bata umarnin taje tayi Alwallah .

Bata musaba taje tayo wanka da Alwallah ta dawo ta iskeshi zaune bakin gado.

Sallah suka gabatar kamar yanda Shari'a ta wajabta, Bayan ya ciyar da ita taciyar dashi suka koshi sukayi hamdala. kowannen su yayi shuru bakajin komi sai bugun zuciyar su dake hau hauwa .

Irfan yayi k'arfin halin cewa kije ki kwanta Baby nima zanje D'akina kar in matasamiki nasan kin gaji ko.

Da sauri Moopy ta kad'a kai . Bankwana yamata yatafi Tare da sakin Murmushi.

Tana ganin fitar shi ta zare kayanta ta sanya na bacci masu mugun taushi, Tare da fesa turare lungu da sako tayi Addu'a ta kwanta.

Can cikin dare Mufeeda taji bakon al'amari ,kamin kace mene ta cika gidan da ihu.

Washe gari da safe Moopy keta zabga kuka kamar yarinya .

Irfan ma da zazzabi ya rufeshi yanata aikin lallashi da bata baki amma ko kallonshi batayi sai kuka .

Dakyal ta amincemi shi ya taimakama ta yamata wanka ,ya shiryata shima yayi ,kasa fita masallaci yayi saboda zafin da jikinshi , Sallah shi yayi gida yana gamawa ya had'omata Tea mai kauri Bayan tasha ta rage ya shanye tare da b'allar magani yabata,shima yasha ,yajata jikinshi sai bacci.

Rayuwa mai dadi sukeyi cike da burgewa.

Abangare su Ammi kuwa abun ba acewa kimi, So da k'auna kawai take nunama yaran ta.

Irfan na kula dasu! inda ya maida su Amina makaranta yasama ma Ammi yar aiki suna zama tare.

Bayan wata goma.

Irfan ne da gudu da Moopy a'hannunshi ya sakko da ita daga saman bene yana nishi da raf'keken cikinta sai kuka take, Tana faďin mutuwa zanyi Honey ka yafemun.

Kuka Irfan yasa ya'ce" bazaki.mutuba Matata, in kintafi kibarmawa ni? kingama.ma haihuwar kinji ko, bazan sake miki ciki ba har Abada.

Aguje yasake yin.sama ya d'akko mata hijjob inta yasamata ya sungumeta yasanya a'mota sukayi Asibiti da take Awo .

Cikin gaggawa aka karb'eta! inda Irfan ya sanya kanshi shima ciki yahana kowa zuwa wurinta , Dan yace babu shegen da zai kalle
mai.mata.

Moopy tasha wahala kamin Allah ya taimaketa haihuwar ta taso.

Tsaye Irfan yake a'gigice wurin kafarta ya samata.ido kamar yasamu tv.

Alhamdulillah ya furta ganin kan Baby ya fara fitowa.

Cike da kwarewa da sanin.makamar aiki ya karb'i haihuwar matar shi, inda santalelan d'ansu ya faďa hannun uban shi.

Da sauri ya yan ke cibi tare da fitowa yaba wata nursing Baby yace ta shiryashi.

Da sauri ta karb'a tana fadin Masha Allah.

Irfan baiko kalletaba yakoma wurin Moopy ya gyarata.sosai kana ya canzamata gado ya gangaro da ita dan kaita d'akin.hutu.

Jaririn aka.mikamai sukuma suka karbi gadon suka kaita dakin daya dace.

Waya ya zaro ya fara bugama yan uwa da abokan arziki dan danan Asibiti ta cika.
Chapter 31 · 0% Book details