Sashe 23
Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsohuwa ta'ce" yo abubuwa mana kai dai kaji abunda nacema inkuma kakiya alhaki na akanka tom..
Alhajin yace ash'sha Hajiya karki yi fushi yanzu haka ina abuja wani aiki yakawoni nafadama Irfam ya fadamaki dan nata kiranki baki dagaba.
Tsohuwa tace ina wani abune shiyasa Allah yatsare sai kadawo ta kashe wayarta ta fito palo tana fadin yar Cakwal ba'inda zaki yau anan zaki kwana in mak....
Kantakarasa taga wayam ba Moopy ba a'lamun ta aguje Tsohuwa tashige D'akin irfan ta iske Ammar nata gogema irfan jikinshi da towel dan zazzabi yake.
Taohuwa tace Ammar ya haka katafi ka mayar da itane?
Ammar yace wace kenan?
Tsohuwa tace uwaka yarinyar daka barmu afalo mana yar Cakwal.
Azabure ya'ce wai kina nufin Bata gidan nan ne?
Tsohuwa tace Wallahi bata nan! daga shiga in amsa waya na fito naga bata nan.
Ammar ya'ce" ya ilahi dama neman hanyar guduwa take, bari in'bita mugani ko zan sameta gidan ta, ya fara k'ok'arin mikewa" IRFAN dake kwance magashiyan ya rike mai k'afa tare da fad'in kamani in'tashi
Tsohuwa ta ya mutse fuska ta'ce" a'yaufa maza na jinya, an'sha dukan Aljannu jiki yayi tsami, kai Irfanu turai ta lalataka wallahi,da maza na haihuwa da banson uban da zakaiba ranar da zaka haihu, katon banza mai kashin wando."
Irfan bai ce komi Ammar ma ya kamashi ya mikar dashi ya jinginar dashi akan gado yace bari in'dawo Bloody .
Akaro na biyu Irfan yasake ruk'oshi tare da gilgiza mai kai idonshi fal hawaye yace zanje.
Ammar ya zaro ido ya'ce ina? kason inda zani ne?..
IRFAN ya'ce" nacema zanje dan Allah ka kamani in mike tsaye...
Tsohuwa ta'ce" oni yasu k'udirar sama liman da wawan zama, yau kuma lalacewar da tasameka kenan.kai Amiru kamashi ku tafi tare, da kabarshi nan kashi zaiman dan yabani aiki.
Ammar yazo ya kamashi a'hankali suke tafiya dan jikin IRFAN kota ina ciwo yake,haka har sukaje parking lot Ammar ya jawo motarshi tare da sanya Irfan ciki,suka hau hanya Ammar ya'ce" gidanka zan kai ka dan ni zanshiga gidan Mufeeda ne.
Irfan ya'ce" nima ka kaini in nemi ya fiyarta" na fahimci abunda nike mata bai kamata ba zan bata hakuri...
Ammar ya gwalo ido yace Hmm saboda kaji Tarihinta ko, fahimci ko wacece ita ko?
Irfan ya'ce" Wallahi Billahi ko D'aya ban sani ba, kuma bana bukatar in sani, zanyi dan Allah ne banga am'fanin wannan kiyayyar danike nuna mata ba. ka gafa ko son ganina batayi,in Na mutu a'wannan halin nason tana da hakki mai girma kaina, tinda har karyata na sakeyi. yafada hawaye na gangaro mai a'fusaka.
Ammar ya jinjina maganar IRFAN suka dauki hanyar gidan Moopy, suna isa mai gadin ta ya'ce" masu ba kowa a'gidan ko Inna ma bata nan.."
Ammar yayi mamaki sosai yace to ina Moopy ta fita?..
Mai gadin yace wallahi bansani ba, tinda rana naga wucewar ta har yanzu bata dawo ba.
Ammar ya'ce" to shikenan!! ya tada motar suka tafi, a'tak'aice duk inda Ammar ya son zaiga Moopy a'ranar ya nema ya rasa,Hankalin Irfan yafi na Ammar tashi, dan sosai yake kwadayin ya ganshi gabanta yabata hakuri akan abunda ya kemata, amma ina ya makaro dan Moopy tayi nisan kiwo.
CIKIN sati d'aya Irfan ya zabge ya lalace ga suma duk tamai yawa,ya nemi komawa mahaukacin karfi da yaji, yauma kwance yake a'd'akinshi na gidansu yana zane zane a paper, Mamy ta shigo tace Son wai kuwa lafiya kake kwana biyu baka fita ko ina, ko d'an Studio din kabar zuwa ko wakar kake rubutawa a'nan. ta fad'a tana d'akko takaddar gabanshi....
. Irfan ya kad'a kanshi yace aa nabar wakar ma har a'bada Mamy, saina nemi yafiyarta in'ta yafeman rayuwata zata dawo kamar kullum, banson mi yakainiba har na k'ara karyata na zageta, na zagi Mahaifinta,har yar TASHA nace mata......
Mamy ta saki halittu tana kallon ikon Allah! ta'ce" Irfan wai kana nufin so ne yasaka kuka haka?
Irfan ya'ce" aa Mamy banason ta ko kad'an, kawai yafiyart a nike nema, na cuceta na mata ba dai-dai ba daga tazo yimana Taimako..
Mamy ta'ce" wacece ita? waye Mahaifinta da take baka wahala haka? tace bazata yafemaka bane!?
Irfan ya d'aga ka fada ya'ce i don't know Mamy, banson komi na taba, naje gidan ta bila a'dadin amma bata nan, nason kuma ni naja har tai fushi ta gudu.sai dai matsala ta ban'son wacece ita ba, banson gidan iyayenta ba. in da take ZAMAN TASHA kawai nasani sai gidanta..
Mamy ta zaro ido ta'ce" wai kana nufin ZAMAN TASHA take? kuma gida gare ta ita kad'ai. inaaaa Impossible Wallahi kama canza tinani tin wuri kamin ka b'allo ma kanka ruwa, bazan taba Amincewa ba dan ko mahaukaci ya ganka ya son kafad'a a'tarkon So.
Irfan ya'ce" Noo Mamy kidaina ceman haka, taya zan so Yar ZAMAN TASHA, har a'bada Wallahi ina ne mantane kawai dan sauke hakkinta daya rataya a'wuyana
Rai a'ɓace mamy tace to naji, kuma ni Mahaifiyarka ban lamincema zarcewa daga nan ba kaji na fadama, kagama abinda zakai kazo kayi aski kazama kamar sabon kamu. zan baka sako ka kaiwa k'awata Hajiya Amina yar'tama Yusra ta dawo zaku gaisa da ita .
Irfan ya kalleta ya'ce to Mamy kiyi Hakuri mana kina ta fushi.
Tace ba komi tare da tashi ta fita fuska a'daure.dan ba taso yasamu damar son wata yarinya bayan tana da zab'in da tamai tin kamin yadawo kasar da zama.
Yau takama Alhamis dai-dai da ranar da Moopy tai Al'kawarin bayyana ma mutane kanta .
Karfe Hudu na yamma filin Kara-Kanda Stadium din shake yake da mutane bila a'dadin,manya da yara maza da mata kai harma da ma gidanta, bakaji sautin komi saina zazzakar wakar moopy da a'keta kunnawa. IRFAN na sahun gaba shida Ammar dan duk yanda yaso ganin Moopy halin dayake ciki yasanya yace da yafasa,da kyal Ammar ya matsamai suka fito badan ya soba, tinda yazo wajen gabanshi ke faduwa gashi taki zuwa har 5 takusa saura kwata," ya'ce Ammar barin wurin nan zanyi, kason banajin dad'i ko?
Ammar ya'ce" kayi Hakuri mana in Biyar tayi ba tazoba sai mu wuce.
Badon Irfan ya soba ya koma ya zauna yaci gaba da latse latsenshi a'waya. yana rubutu na neman moopy duk wata kafar sadarwarshi fatanshi Allah ya gwadamai ita ya sauke nawin dake kanshi....
Kimanin 20mnt yakama 5:05 DJ yasaki wani Mahaukacin ihu ganin wasu daka-dakan motoci masu numfashi na shigowa wurin, ta speaker yace Alhamdulillah wadda ake zaman jira tazo wato hajiya MOOPYYYYYYYYYY.
Jikake Raf!!! Raf!!! RAF!! Wuri ya ka came da hayaniya, mutane suka tashi suna ta ihu. sai da aka d'auki dogon lokaci idon kowa a'kan motocin guda biyar rass masu mugun kyau, da daukar ido, aka fara bude ta farko rafel yafito yana gyara Babbar rigarshi, ta biyu kuma Fahad ne shima ya dauki danyen wanka, ata ukkun Hajiya Moopy ta ziro farar kafarta datasha maroon Din takalmin daya dace da farar fatar''ta taziro jikinta baki daya ya Allah masha Allah mutanan suka fara ihu suna fadin masha Allah lallai Allah mai halitta" yanayin zakin muryar ta yanayin kyauwun da rabbi yamata, lallai dole ta b'oye kanta wannan. wasu na kusa da Irfan suka fad'a. Irfan ya juyo yama Ammar magana amma wayam bashi ba a'lamunshi, mamaki yakamashi a'hankali ya'ce ko ina yaje? yafara kai kallonshi saitin da yakejin a'na fadin ka ganta cen tsaye wallahi itace .
Irfan ya d'ago idonshi dan kallon Masoyiyar shi da yakejin bugun zuciyarshi na linkuwa ta dalilin tsayuwar'ta a'filin. idonshi karaf yafada ana Ammar dake tsaye kusa da Moopy shima yasha shadda fara kal kamar Ango.Ammar yad'aga mai gira tare da kashemai ido d'aya ya nunamai Moopy dake tsaye ta kasa motsawa dan hakanan taji babtajin dad'in tsayuwar wurin. amma tana a'lakanta hakan da yawon mutane.
Hankali tashe IRFAN ya zubama Ammar idonshi da ya rikid'e cikin lokaci yakoma jajur, yausbe Ammar yazama haka da har zai fifita mace a'kanshi? kenan yason inda Moopy take amma ya;barshi yanata wahala gashi dan baida kunya da mutunci harda zuwa da ita kallo, lallai kam yau sai yama Ammar rashin mutunci na karshe...
.lDj ya fara fad'in Alhamdulillah hausa wa na fad'in mai wuri yazo mai tabarma ya nad'e
Batare da Bata lokaci ba zamu fara a'bunda ya kawomu muna maki murna da zuwa hajiya Mufeeda Abubukar Tela, inba damuwa ki daure ki karaso dan muyi a'bunda yataramu kasancewar tin dazu masoyanki ke son ganin wannan kyakyawar fuskar taki dake kama dawata daran goma sha biyu.. .
Ammar ya'ce" k'anwata kiyi Bissimillah tare da Addu'a ki karasa wajen kinji...
Moopy ta rintse idonta ta fara Addu'a, take zuciyarta ta samu natsuwa atare suka d'aga k'afafuwansu su Hudu curr ,sun sata a'tsakiya suka doshi saman dandamali da aka k'awatashi da manyan-manyan sifiku .
Wawa sakarai mahaukaci Irfan yazama dan da ido kawai yake binta yaga ina zata wai, harda kutsawa cikin maza mamaki bai kasheshiba saida yaga ta karbi speaker ta fara kwararo Addu'oi cikin zazzakar muryar ta, idonta a'lumshe hawaye duk ya jike lashes dinta,saida ta kwashi minti goma kana ta da kata. ta danyi shuru sukai magana da Fahad kana ta fara magana muryarta na rawa alamar rashin sabo....
ASSALAMU ALAIKUM YA YAN UWANA MUSULMI, DA FARKO DAI INA MAI MATUKAR GODIYA DA FATAN ALKHAIRI A'GAREKU, TA YANDA KUKA AMSA GAYYATA TA KUKA AJE AI'KINKU DAN SON GANIN MASOYIYARKU. AZAHIRIN GASKIYA BANSON TA YANDA ZAN BAYYANA FARIN CIKIN DANIKE CIKI BA, SAI DAI INA MAKU FATAN ALKHAIRI NAGODE ALLAH YA MAYAR DAKU LAFIYA....
Fahad ya karbi speaker ya k'ara godiya wa mutanan wurin kana ya bude wata doguwar takadda ya'ce Alhamdulillah ga sakwan nin mutane munsamu dan yiwa Hajiya Moopy tambayoyi, dan haka zamu fara jerantosu a'gurguje duba da lokacin da bamu dashi,duk da tambayoyin sunkuson zuwa d'aya dan haka zamu hadasu a jimlace mu bada am'sarsu.
Tambayar farko a'kace MIYAJA RA'AYINKI KIKA FARA WAKA?
Moopy tai murmushi ta'ce malamina shiya fara umarata ta dayin Waka, bayan Amincewar Babana daga baya Yayana Rafel gashi gabana shida yah fahad suka k'ara k'arfafaman gwiwa, har na taka nasarar da nike ciki.
Aka sake tafa mata dan sosai ta burge mutane..
Tambaya ta biyu MIYE KIKA FI SO A ABINCI?