← Book details Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 32

Sashe 15

Zaman Tasha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba yace bari in rufe shagon in biki, dan nima duk yau ban shi gaba, haka ya rufe muka shiga soron gidanmu tare mukai sallama shuru!! sai da muka karasa tsakar gida anan naga Ammi nata wanke kayan gwanjo ta, da a'lama ɓaci sukai. "ko am'samana batai ba wannan bai hanani duka wa nace Ammi ina wuni ba.
Ta É—ago a'fusace tare da dungureman kai tace matsa cen yal banza dawata shegiyar muryarki kamar an sakamaki radio cikin makwoshi, haka kawai kika sheman dodon kunne."..

Baba yaja hannu na muka fada É—akin Inna tare da sallama mukaji shuru!! muka yaye labulen É—akin muka fada...

Atare nida Baba na muka saki wani mahaukacin ihun daya janyo hankalin Ammi tayo É—akin a'guje .

Gabaki dayan ban'gwon É—akin Inna ya faÉ—i kana kallon bayan gidan mu, kasar baki daya ta ruf'zo har kan gadon Inna ta.
Cikin kuka nafara kiran Inna-Inna!! tare da rugawa waje na bude toilet dinmu ba Inna babu a'lamunta,na dawo É—akin ina kuka, banson sadda na haye gadon ba, anan naci karo da hannun Inna nasaki kuka tare da faÉ—in baba ga Inna ta nan, dan Allah Baba a'É—agoman Inna dan Allah karta mutu tabar ni, bani da kowa sai Inna ta, Inna dan Allah kitashi in kintafi nima zan biki, sada nace kibar ni mukwanta tare kika ki yarda.."

Baba da yake kuka shida Ammi suka hayo gadon, da sauri sakafara ƙoƙarin jawo kasar amma ina ta yiwa Inna runfa, aguje na fita waje nafara ihu ina ne man ɗauki,yan tsirarun mutane da basufi ukku ba suka biyoni mukashigo har dakyar suka dinga zaro kasar har Allah yabasu sa'a suka zaro Inna da jikinta ya yi kaca_kaca da jini, aguje nayi kanta ina kiran sunan ta tare da neman ta tashi tafadaman miya faru.

Wani acikinsune naji yana fadin sai hakuri da a'lama ya daÉ—e da dan neta dan gaskiya Allah ya amshi a'bunshi."

Jin furucin bawan Allah nan yasani yan ke jiki na'fad'i!!daga nan ban sake sanin a'bunda ya faruba sai ranar da Inna tacika kwana shidda da rasuwa!
Agigi ce natashi ina kiran Inna! inna!! wai kinji nayi mafalki kin rasu Inna fito inganki dan Allah, nafad'a jikina na rawa..

Kaka na dake gefe zau ne da casbaha da baba suka yo kaina suna kallona kowannansu idon shi cike da hawaye.

Baba yakama hannunan yarike yace "uwata a islamiya nason ansha fad'amaku illar yiwa mamaci kuka ko ba haka ba? sannan nason an'fadamaku kudunka hak'uri da k'addara mai kyau ko akasin haka ko ba haka ba?.

Dan haka "Inna Allah yakarb'i ranta ba muda yan da zamuyi sai dai abu d'aya data ke bukata anan shine mubita da addu'a, dan wata rana muma haka za a'wayi gari ba bumu a'doron duniya kinji ko uwata?

Nafashe da kuka nace ma Baba to yanzu wazai dingaman kwalliya yana saman kaya baba?.

Baba yabud'e baki zai magana Ammi tafi to daga É—akinta ta duka ta gaida kaka tare da gaida baba na" abunda bata tabayi ba tin bayan mutuwar auransu.
Baba ya amsa cikin mamaki.
Ammi cikin sanyin murya ta fara bama Baba hak'uri akan a'bunda yafaru kwanaki, tare dasa ke masu ta a'ziyya tace a'shirye take data rike Moopy a'yanzu.
Bakaramin daɗi baba yaji ba shida kaka suka samata albarka!!" takama hannuna tashiga dani ɗakin ta duk a'tsorace nike da ita, dan ban saba ke ɓewa da itaba .

Munashaiga taban a'binci. "na gilgiza mata kai a'lamun bazanci ba." ta zaroman ido tare da faÉ—in banason iskanci maza ci kiban kwanan," haka nafara tura abincin ba dan daÉ—i ba, bayan nagama nayi sallah nadawo wajen kaka nazauna nafara mai magana Inna,'." kaka sai yaban hakuri yace in bita da addu'a ita tafi bukata.

Bayan kwana arba'in É—in Inna da sati biyu, kaka yatashi da amai da gudawa, bai wani jimaba ya amsa kiran mahaliccin shi.
"Nan da nan rana tazameman zafi inuwa ƙuna," dan Ammi a'gabansu take lallaɓani bayan idonsu kuma zagi ne sai duka ke shiga tsakanina da ita.

Bayan anyi sadaka kaka!! Baba ya yi sallama wa Ammi yace ta fito, bayan tafito cikin ladabi ta gaidashi ya amsa tare dayin shuru.
Azuciyar Ammi fatanta Allah yasanya abunda take tinanine zai wakana.

Ilaiko sai gashi Baba yafara mata magana akan tana da ra'ayin a'maida auransu ko-ko yasamo wata, dan gaskiya yagaji dazama ba mata, gaya babu iyaye dole yabukaci mai de bemai kewa.

,,Jin a'bunda yace yasa Ammi cikin rawar murya tace ta amince,washe gari aka maida auran su baba da Ammi, nan suka fara sabuwar rayuwa a'inda a'ka d'ibi dakin inna aka gyaraman baba yasaman sabuwar katifana ina kwana.
Wata laraba ina zau ne malamin makarantar mu ya aiko kirana, akan in dawo makaranta," Baba dake É—akin Ammi yaceman in tashi in sanya hijjob infita, haka nafita na isa wajen malam na zau na, na gaisheshi yaman gaisuwa daga nan muka dasa daga inda muka tsaya.

Bayan sati biyu makaranta islamiya mu aka fara ba da hardar maulidi !!nima a'kabani tawa, bayan angama malam yari keman littafi nakawo ta cikin sassanyar muryata mai daÉ—in sauraro, wanda sanadin hakan yasanya har nakai karshe malam baisani ba, sai da nacemai malam nayi dai-dai?
"Malam mubarak ya É—i mauce yace kwaraiko Mufeedah, Allah ya yi ki da zakin murya mai sama ma a'boci sauraro natsuwa, anya kuwa bake za ki re ramana wakar da zamusanya ba ranar da zamuyi maulidin.?

Nai dariya ban ce komiba.
Kamar wasa kullum malam sai yaman magana, har wata rana yazo da duguwar farar t akadda yabani tare da cewa dan Allah mufeeda ki kwatanta raira wakar nan, ina ganin za ki iya cimma nasara ."

Kamar wasa naji abun yashiga raina! nan nafarayi duk da ba wani kwarewa nai da rai rawar ba, amma kasancewar na iya hausa sosai sai abun bai-ban wahala sosai ba.
Har wata litinin muntashi daga makaranta," malam Mubarak yaceman yanaso muyi magana in tsaya shagon baba na zai iskeni anan."

Nace mai to ba matsala" cikin tafiya ta ta natsuwa data zame man jiki, nashiga shagon Baba na, na iskeshi ya yi tagumi nakarasa wajenshi tare da zare hannunshi nace Baba miyasame ka?

Baba yarungumeni sosai tare da fashewa da kuka, yace narasa mikikayima mahaifiyarki ba tun yau na fahimci kalar tsanar datakemaki ba mufee, dama bata baki abinci amma baki faÉ—aman ba sai É—azu dana zo shiga naji tana maki faÉ—an a'kan bazata baki ba?

Nai murmushi tare da zare jikina daga nashi nace" haba Baba bakomi ni bana mason abinci, kuma inna zo wanke wanke ina samun kanzo inci, kuma in kaban kudi ina sayen wani abu makaranta inci, ita Ammi sai tace sai naje tallah ba tare daka sani ba, wai in zanje boko kar inshiga in wuce tallah, nikuma nace aa inason karatu inaso inzama babba likita Baba in'dunga ma mata allura ko?
Baba yayi murmushi yashare hawayanshi yace "Allah yacikamaki burinki Moopy, sai dai ina so in'saki islamiya yamma, karki yarda kiyi tallah!! daga yan zu in kindawo boko zamushiga cikin gidan kiyi bukatar da zakiyi zamu dawo nan shago in koyamaki dinki, in hudu tayi zanyi alwallah la'asar zamu shiga kisanya ka yanki kitai islamiya, in kindawo ki zau na ta mangari ba abinci kuma maci nawa ki rabu da ita kinji ko?

"Nadagamai kai dan nima naji daÉ—in hakan sosai."
Muna zau ne muna fira malam mubarak ya yi sallama yashigo, bayan sungaisa da Baba yake ma Baba bayani, akan dan Allah inba damuwa sunaso a'barni muje STUDIO in rai ramasu wata waka dazasuyi maulidi da ita.
Baba ya jinkirta zuwa cen yace to wazai tafi da ita? sanna mamana bata iya waka ba kar'tamaku shirme duba da duka yanxu tacika shekara 11"

Malam ya yi murmushi yace wallahi Malam Bukar na hango baiwa mai tarin yawa game da moopy, Dan Allah karka hana mu wannan damar data samemu, baka damasaniya ko Yarka zata iya ko bazata iya ba, fatana dai kawai kasama abun albarka."

Baba yace to shikenan "mama na" za ki iya kuwa?.
Cikin murna na kadamai kai a'lamar eh.
Yace to masha Allah yau she za ayi abun? zan shirya da kaina in kaita?
Malam mubarak ya sake yabawa da tarbiyya da Baba ya
ÆŠorani akai, yace gobe ne bayan azahar.
Baba yace bakomi Allah yakaimu.
Malam yace Ameen yakama gabanshi.
Washe gari ina kwance Ammi tashigo ta zabgaman mari, tare da faÉ—in tashi kisanya kayan makarantarki, ki É—auki kaya kitai tallah, ai bazakiman zau ne cikin gida ba kina zubaman wannan shegun idanuwan naki kamar goruba ba".
Na tashi a'gigice ina matsawa ina bata hak'uri tare da cewa dan Allah Ammi kiyi hakuri ni karatu nikeso.?
Tayo kaina gadan-gadan "Baba yashigo ɗakin ya yadakama ta tsawa" tare da furta duk ranar da hannunki yasake kuskuran kaiwa jikin uwata wlh tallahi sai ranki ya ɓaci wadda batason ciwon kanta ba.

A'fusace Ammi tace wlh bazan aje wannan zabge'giyar yarinyar a'gidan nan ba bata neman man kudi ba, haka kawai to ni k'ake so inje ko-ko? bayan Allah yasanya da ranta da lafiyar ta.

Baba yace ai bawani yasaki talla ba ke kika sa kanki, dan haka sai ki É—auka kitafi tinda ke baki da ma'faÉ—i, yayi tsaye kaina na shirya mukaje shagonshi yabani tia da bread nasha na tafi school, bayan nadawo na iske Baba shago muka shiga gida yayi tsaye kaina nai wanka nashir ya cikin jar a'tamfar da Yaman sabuwa mai ratsin baki, yaban sabuwar hijob baka nasanya nafito.

Baba yace Masha Allah uwata tafi ta kowa kinyi kyau sosai .
Nai dariya tare da cewa Baba nida bana kwalliya ban'ma iyaba, wanka kawai na iya sai shafa mai, Inna ke man kwalliya yanzu kuma batanan.
Baba yace ki mata addu'a nan gaba zaki iya, ke kyankima ai ajini yake uwata ko bakiyi wanka ba.
Haka mukaita labari har na fito muka dawo shagon shi, Baba yabani abinci naci muna fira malam mubarak yashigo shagon .
Bayan sun gaisa da Baba muka taso muka hau a'daidaita mukayi wani Studio bayan munje aka tarbemu a'inda malam yafara masu magana akan yanaso in masu wakar maulidi.
Mai Studio yayi dariya yace malam ga yam matanan sai wannan yar yarinyar taya zata iya?
Chapter 15 · 0% Book details