← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 94

Sashe 93

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tawakaltu na shiga ta hangi Ameera tana sallah, saida ta salkame ta nuna mata hanyar bathroom, itama shiga tayi ta dauro alwallah ta tada sallah, Ameera komawa tayi gefe ta hada kai da gwaiwa cos ita kadai ta san abinda takeji. Bayan Tawakaltu ta idar da sallah ta kalleta
"Sannu sis..kina jin jiki..." Tafada tana kallon ta, Ahankali Ameera ta daga kai
"Yauwa...pls dama kema haka abun yayi maki?..." Ta tambayi tawa cikin sanyin murya
"Gaskiya bai yimin haka ba...kawai ni dacin baki da kasala ke damuna... Ke mai zafi kika ciyo..." Tafada cikin zolaya. Murmushin karfin hali Ameera tayi
"Wallahi sis...har na gaji...in haka ciki yake gaskiya duk Dan da baiji maganan uwarshi ba ya shiga uku...."
"Hmmm haka ne...Dan bai San wahalan da uwa take sha kanshi ba amma ya girma ya nuna ya fi uwar wayau da hankali..." Ahankali Ameera ta girgiza kai
"Allah ka kiyashemu da yaran da basu jin maganan iyayensu..."
"Ameen..." Tawa ta amsa mata, hiransu suka cigaba dayi har su Salem suka dawo daga masjid. Salem zama yayi inda ya tashi shi kuma Khalid yayi arranging dinning table da abincin da aka kawo daga gidansu
"Guy kayiwa Tawakaltu magana tafiya zamuyi..." Inji Salem,
"Muyi dinner tare mana..." Inji Khalid
"No...zamu tafi..." Yafada yana kallon agogon hannun shi. Khalid bai kara cewa komai ba ya shiga ciki ya kira Tawakaltu, ahankali Ameera ta mike tana cewa Tawakaltu
"Dan Allah sis ki dinga zuwa dubani tunda kince kina yola har ki haihu..."
"To...in mai house ya amince...".
Dukkan su fitowa sukayi, Salem na ganinsu ya mike, Tawakaltu ta karasa wurin shi ya rike mata hannu, shi kuma Khalid ya zagaye hannun shi ga kugun Ameera suka rakasu har bakin mota Sannan Khalid ya dauketa in a bridal style suka koma ciki.

Daga wannan ranar Friendship dinsu ya dawo, duk ranar da Salem ya shigo yola Sai sunje gidan Khalid don har kusan wata biyu Ameera bata samu saukiba.

Tsakanin Ameera da Tawakaltu shakuwa ce sosai don har su Salem cewa suke kar a munafurcesu, don kullum suna cikin waya da junasu in har basu tare.

Sultan kam ba karamin soyewa suke da Habeeba ba, duk family sun San da soyayyar su, dukda sauran shekara daya ta gama daga Oxford university sultan yaki wai dole suyi aure before then kuma yayi alkawarin zai barta tayi aiki a duk kasan da take so.

Yanzu Tawakaltu na jira taga ta yanda labor zai fara don lokacin ta yayi kawai tana jiran time, babu yanda Salem baiyiba don Umma ta barsu su tafi abroad haihuwa amma taki tana cewa mai sa a sauka lafiya chan shine a nan din haka bazaa sata zaryan kasan wajeba. Dole Salem ya hakura ya kira wata kwararriyar doc daga london, matar ta San aikinta sosai don har su pregnancy exercise take sa ta. Tawakaltu kam abun duniya ya isheta don ji take kaman ta cire cikin ta yarda don tunda ta shiga watanta takejin nauyin cikin, yanzu Salem ya bar zolayan ta don kiris take jira ta fara kuka, tun jiya Salem ya dawo yola kuma baida niyyan tafiya da Umma ta tambayeshi cewa yayi yana nan har Sai Tawakaltu ta haihu, kai Umma ta girgiza tana mamakin rashin kunyan Salem Sai kuma ta tuna cewa ba yaro bane shi.

Kullum Tawakaltu cikin yiwa Umma adua take don ba karamin kulawa take bata ba, duk abinda take so shi zata ci balle cikinta ba mai selecting abinci bane. Sannan kullum tana bata maganin masu ciki tana sha ga wasu mami ta aiko mata.

Daman da akwai home hospital a gidansu Salem don haka abubuwan da ake bukata wurin haihu aka saya aka sanya wurin yanda koda haihuwan ta zo basai sun tafi waje haihuwa ba. Salem kullum cikin online shopping yake dukda sunyi shopping a kasar waje amma gani yake kayan basu isaba.

Yau tana zaune kasan carpet bayan sallan ishai doc Vicky tana dan ne mata kafafunta, Salem ne ya bude kofa ya shigo, kallon shi tayi ta kauda kanta kaman bata ganshi ba cos yanda take jin haushin shi Allah kadai ya sani, din gani take shi yasata cikin wannan conditions kuma shi kullum cikin gayunshi yake, gaisawa sukayi da doc Vicky t fita ya karaso kusa daita
"Babyna ya kike?.." Ya tambayeta yana zama nan kasan inda take,
"Lafiya..." Ta amsa mashi atakaice, murmushi yayi
"Princess nayi wani laifi ne?../" bata kalleshi ba tace
"Wayace kayi laifi?..."
"Naga tunjiya kaman kina fushi dani...jiya ma kin bani hakkina kikayi...." Galla mashi harara tayi
"Kai kullum hakkinka...ni baka tausaya min?...baka ganin yanda nake?....ni wallahi ta kaina nake...ji nake inama ina iya baka ajiyan wannan cikin... Am tired.." Ta karashe maganan kaman zatayi kuka, hannun ta ya kama yayi mata kiss
"Sorry.. Kin kusa hutawa insha Allah... Daman aski inyazo gaban goshi yafi zafi....sannu kinji..." Bata amsa ba ta kara kallon shi ta galla mashi harara again,
"Ni banason wannan sannun...." Dariya yayi
"Me kike so?..."
"Nima ban saniba...kawai am tired...."
"Bari in hada maki ruwan wanka...." Ya fada yana mikewa,
Bathroom ya shiga ya hada mata ruwan wanka yadawo ya dauketa suka shiga ciki, kayanta ya cire mata yafara kokarin cire nashi, kallon shi tayi
"Me zakayi?..."
"Wanka zamuyi tare...."
"Aa...ka tafi part dinka kayi wankan..." Murmushi yayi din ta gane manufarsa, bai saurareta ba ya cire kayan zo kusa daita
"Babyna...let's do it ...kilan kafin tomorrow kin haihu and I will be lonely for a while...." Yafada yana kissing wuyanta, kallon big belly dinta tayi tana mamakin yanda baya gajiya da abu daya har ya fara koya mata hakin shi, ahankali ta dan zame tana cewa
"Ni marata ke yimin ciwo..." Tsayawa kallon ta yayi
"Tun yaushe yake yi maki ciwo?..." Ya tambayeta sounding very caring
"Dazun... "
"Kin fadawa Vicky?..." Girgiza kai tayi
"AI ba sosai yakemin ciwoba...yazo kadan ya koma ya dawo.. " yanda take maganan in I don't care tune yasa Salem ya tsaya kallon ta
"Amma baby an fada maki kome ke damunki ki dinga fada mata... Kilan you are having a contractions..." Murmushi tayi tana cewa
"In haka ake contractions da kullum zan dinga haihuwa..." Tafada tana dariya, wanka sukayi tare da hot romance suka fito, kara tambayan ta yayi ko tana jin zafin mararta ta amsa mashi da No

Cikin wardrobe ya shiga ya dauko mata kayan bacci ta saka ta hau gado, lokacin kuma ta farajin ciwon maran, amma bata fada mashi yayi bata good night ya tafi ya kwanta, itama kwanciya tayi.

Har ten maran na kara ciwo ahankali amma bata dauki ciwon serious ba saboda daman in zatayi period tana irin wannan ciwon.
Fitsari tajeyi taga wani abu kaman mucus mai hade da jini, da sauri ta fito ta tada Vicky da ke kwance gefen gadon ta fada mata abinda ta gani, safa ta dauko ta umarceta data kwanta ba musu ta kwanta, dubata tayi ta fada mata she's in labor, tawa mamaki take wai ashe daman haka haihuwa keda sauki?, nace you must be joking,

Around 4am abun ya zama gaskiya don banda yarfe hannuwa babu abinda take har lokacin baa sanar dasu Umma da Salem ba, kuka tafarayi tana yarfe hannuwa da zafin ya bari Sai ta goge hawayenta, chan Sai ta fara kuka, Vicky sai danne mata waist take, karfe biyar taji contractions din ya zama unbelievable
"Wayyo ki kira salem...mutuwa zanyi...." Ta dinka maimaitawa Vicky da turanci, Vicky kiran number Umma tayi sai na Salem ta sanar dasu halin da ake ciki, tawa durkusawa tayi gaban gado ta dora kanta ta fara bacci, ko minti biyu bata yiba ta farka ta fara kuka sosai, lokaci daya Salem da Umma suka shigo, tawa Sai zufa take kaman babu ac a dakin, duk hankalin Salem ya tashi, Umma sannu ta dingayi mata amma babu bakin amsawa Sai kuka,
"Please a kaita wurin haihuwn..." Inji Umma,
"Stand..." Vicky ta umarceta ahankali, da sauri tawa ta girgiza kanta tana cewa
"Ban Iya tsayawa...." Tafada cikin kuka
"Wayyo bayana...Mara ta
.." Ta dinga maimaitawa,
"Baby sorry..." Inji Salem dake magana kaman shi ke labour, Salem ne ya daga ta tsaye Sai ihu take, duk yanda Umma ke hana ihu Sai tace
"Wayyo Ku barni inyi kona ji sauki....Dan Allah Ku kiramin mami..." Da kyar suka isa mini hospital Ta shiga tana tafiya da kyar don data daga kafa daya Sai tayi minti biyar bata daga dayanba, Salem yaso daukanta amma doc ya hana wai the more she walks the better

Ba karamin wahala tasha ba don duk hankalin su ya tashi mussanman Salem don cewa ya dingayi ayi mata cs kawai don wahalan yayi mata yawa, har kuka sai da yayi don Umma hanashi shiga tayi kuma daga baya ya barjin kukanta Sai ya fara tunanin kilan ma mutuwa tayi, buga kofan ya farayi da karfi yana cewa
"Umma meyasa Tawakaltu ta bar kuka?...Umma in mutuwa tayi Ku fadamin...." Da kyar Abba ya jashi daga wurin, kaman mahaukaci ya koma, alwallah yayi ya tafi masjid ya dinga sallah nafila.
Chapter 93 · 0% Book details