← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 94

Sashe 15

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Haba..alh. Wane irin aurene wannan?.. Ya zaayi mu aurar da yarmu ga wanda baa zauna akayi magana da magabatan shiba?..gaskiya am smelling something fishy.." Mom ta fada lokacin da dad ya fada mata yanda sukayi da Salem. Dad tabe baki yayi
"Ina ruwanki..yarinyan da baki damu daitaba? ..ai ko saida tanayi ba damuwanki bane"
"Ya zaayi kace ban damu daitaba..ai ko bakomai ni na haifeta..kawai halin da takeyi ke banso Amman ba wai banason yataba.." Dad banza yayi daita ya fiddo wayanshi yafara kiran yan gidan radio station ayi mashi sanarwan bikin yarshi, sannan ya kira yan gidan TV ya gaya masu ayi mashi sanarwa. Mom baki ta bude tana kallon shi, yana gama wayan ya mike zai fita mom tayi saurin tare gabanshi tana cewa
"Yanzu alh baka tunanin wannan abun ba yanda ya kamata bane?..ya zaayi auren yata kwara daya babu wedding event.. Babu lefe....babu miji wurin daurin auren..sannan the most annoying part of all ace yan uwa bazasu rakata gidanta don su san mazaunin taba?..gaskiya something is wrong" dad dirty look ya watsa mata sannan yace
"Aniyanki ya biki..." Yana kaiwa nan ya fice ya nufi dakin ameera.
Ameera kam tunda tayi ido hudu da Salem tazama speechless, don kyaunshi ya wuce yanda take tunani, cos yaune ranar farko da ta taba ganin shi atunaninta , daman tana yawan ganishi cikin news sannan tana following dinshi a social Media, Amman sam photo baya yi mashi adalci don a kasa yafi cikin photo kyau sau dubu.
Dad ameera yashiga ya gaya mata yanda sukayi da Salem, ko kadan ameera batayi tunanin wani abuba, asalima farincikine cikin ranta don bata taba hawan jirgiba Amman yanzu tata zataje Spain tare da the most handsome guy amatsayin mijinta.
Nikam nace ameera you better stop dream cos they is no chance in hell.

💚💙💜💛❤

Tawa kam wacegari ta zuba ido don ganin Salem Amman baizoba, duk sai ta tsinci kanta da bakin cikin rashin ganinshi. Ranan wajen aikinta saida suka gane wani abu na damun ta, Amman dasun tambayeta saitace bakomai. Wacegari ma which is Friday ta zuba ido zuwanshi Amman babu shi.
Yau asabar, dawuri tawa ta dawo daga restaurant don basu yin abinci dayawa. Tana zaune dakin su tayi tagumi duk abin duniya ya isheta, banda tunanin Salem babu abinda takeyi ita kanta abin tsoro yake bata don tunda take bata taba jin mutum na yawan fado mata a raiba sai yanzu, kallon agogon wayanta tayi taga karfe 4 sannan tace
"Allah yasa lafiya wannan sir Salem din baizoba...Allah kasashi yazo yau...inason ganinshi.." Karaf sai kunnen mami dake dawowa daga bathroom
"Me kike cewa?" Mami ta tambayeta, da sauri tawa ta dawo hankalinta,
"Mami ba komai" mami kallon ta tayi tare da tabe bakinta sannan ta wuce cikin kuryan dakin.

💛❤💜💙💚
Akan hanyan dawowan Salem daga gidansu ameera ya cewa Abdul ya bi ta hanyan restaurant din su Tawakaltu, ba masu Abdul yabi ta hanyan
"Sir wurin kaman a rufe yake.." Abdul yafada yana kallon wurin daga nesa, Salem kallon wurin yayi, ranshi batcewa yayi don niyyan shi ya tsaya cikin motan shi ya ganta ko yadan samu jin dadi cikin zuciyanshi. Haka suka tafi gida ranshi babu dadi don banda tawa babu wacce yake son gani.
Kallon agogon hannunshi yayi yaga har 5pm dan guntun tsaki yaja don yasan makeup artist dinshi bazai iya zuwa ya chanza mashi fuska ba har yaje gidansu tawa.

Wacegari which is Sunday tun 11 aka chanzawa Salem fuska, 11:30 daidai ya isa gidansu tawa kasancewan babu nesa tsakanin tukuntawa da zoo road, ya zuwa Salem yayi parking a inuwan wani bushiyan neem, sannan ya fita yana neman yaron dazai aika kiranta, bai dade da tsayuwaba saiga wani almajiri yazo wucewa, kirashi Salem yayi yace mashi yakira mashi tawa.
Tawa data gama wankin ta dana mami tare da yin wanke da gyara dakinsu cos basu zuwa aiki ranar lahadi saboda Matan da take saidawa abinci Christian ne, tana kwance tana sauraron sanarwan auren dan tsohon shugaban kasa dazaayi sati mai zuwa aka aiko kiran ta, da sauri ta mike tsaye dukda ta fidda ran zuwa Salem, almajiri na sallama ranta ya bata shine, mami dake kwance kurya tace
"tawa tani?" Maana waye?
"Mami ban saniba bari in leka in gani" ta amsawa mami tana fita daga dakin ko gyale babu jikin ta don Allah 2 take taga mai kiran ta, sanye take da atampha wax dinkin skirt da blouse, fuskanta ko powder babu Amman she's not looking bad, dankwali kawai ne kanta, already almajirin ya fita, ahankali tayi sadaf2 ta taho ta tsaya bayan kofan su tana leken mai kiran ta, a lokacin Salem na tsaye jikin motan hannunshi biyu cikin aljihunshi yana sauraren abinda almajiri ke gaya mashi, tawa na ganin shi ne ta saki wani kayattacen murmushi, shikam Salem baisan tana tsaye wurin, juyawa dazaiyi kofan gidansu sai sukayi ido hudu daita, da sauri ta maida kanta tare da jinginawa jikin bango hannunta dafe da kirjinta dake harbawa da karfi, idanuwa ta lumshe at the same time tana murmushi.
Shima Salem murmushi yayi don yaga irin kallon datakeyi mashi
"You also love me.." Ya fadawa kanshi sannan ya taka zuwa kofar gidan, itakam tawa har lokacin tana tsaya bayan kofan still hannunta kan kirjinta sai cizon lebenta na kasa take tana fidda numfashi ahankali, Salem Dan lekawa yayi yaganta, idanuwanta rufe don haka batasan yana wurin ba , kallon ta yayi from head to toe
"Beauty in disguise.." Ya fada cikin ranshi, tawa bude ido tayi ahankali aikam suka karayi four eyes aikam da gudu ta shiga gida tare da shigewa dakin su, yabi bayan ta da kallon sannan ya sake cewa
_"Perfect shape_ ".

"tani?" Mami ta karacewa, ahankali tawa dakenishi tace "mami mutumin da zan raka kasuwane " tawa ta amsawa mami, kurya dakin ta shiga ta bude wata katuwan ghana most go ta fiddo hijjab Amman ba mai tsawo ba, ta saka sannan ta saka wani flat shoes Wanda kudin ta bazai wuce 1500 ba ta saka, batare da shafa wani abu afuskantaba ta fito tare dacewa mami bari inje
"wurin shi", da sauri mami tace
" kice mashi ya shigo ciki ke ba bahaushiya bace dazaki tsaya rabe2 a waje"
"Yes mami" ta amsa mata sannan ta fita.
Har lokacin Salem bai bar wajen ba, tana fitowa ta durkusa har kasa sannan tace
"Ina kwana?" Mamaki ne ya kama Salem don tunda yake bai taba ganin budurwan da zata kai akalla 18 ta durkusawa saurayiba, da sauri Yafara kalle2 kar mutane su gansu sannan yace
"Oremi tashi mana" yafada ahankali,
"Ai baka amsaba" ta fada muryan ta na rawa
"Lafia lau..please tashi" sai lokacin ta mike Amman kanta kasa tace
"Sir kashigo ciki" cikin zolaya yace
"Ya mukayi dake?..banace banason kina kirana sir ba?" Dan murmushi tawa tayi Amman still bata daga kanta ba tace
"Sorry.. Oremi ka shigo ciki" tsaya kallon inda take avoiding gaze dinshi yayi sannan yace
"Yau tawa kunya ta kikeji ne..kodan na kamaki kina lekena?" Ya fada cikin funny tune,
"Ni ba lekenka nekeba.." Tafada still muryan ta bai bar rawaba, ya gane dalilin rawan muryan ta, yasan hakan na faruwa in mutum yayi maka kwarjini,
"Please ka shigo ciki" ta kara gaya mashi,
"OK" ya amsa mata, juyawa tayi tashiga shikuma ya bayan ta yana tunanin abubuwa daban2 cikin zuciyanshi, yanayin gidan ya kalla yaga gidan talakawane sosai don mutane dake gidan duk talakawane da ganinsu, yarane ke tawasa gidan, daki tawa tashiga shima ya shiga, kallon dakin yayi yaga bakomai sai kujerun roba guda uku sai ledan daki, Amman dakin ko kadan babu kazanta, daya daga cikin kujerun ya zauna, daki tawa tashiga yaji tana kuskus sannan ta fito ta kara fita waje, Salem kam tunani yake
_"Anan princess dina ta rayu...ranakun wahalanki a numbered"_yafada cikin ranshi, gani yayi wata mata tafito daga cikin dakin, sauka yayi daga kan kujrean dayake ya durkusa ya gaidata cikin girmamawa amsawa tayi da murmushi fuskanta har iyayenshi ta tambaya ,sannan ta juya zata koma ciki Dan kara juyawa tayi ta kalleshi sai ta lurada yanda hannuwanshi da kafafunshi suke fari kal sai tayi tunanin kilan wahalan rayuwa ne yasa fuskanshi baki.
Bata dade da shiga dakiba tawa ta dawo, maltina yaga ta ta fiddo daga cikin ledan hanunta, Dan murmushi yayi sannan yace
"Irin wannan tarban haka.." Murmushi kawai tawa tayi tashiga kurya ta dauko wani plastic cup ta Juye maltinan sannan ta durkusa ta mika mashi, amsan cup din yayi tare da hadawa da hannunta, da sauri ta janye hannunta saboda wani taushi da shocking dataji.

💚💜💙❤💛
ZAKISAN KONI WAYE
💚💜💛💙❤
®zuwairat(ummu maryam)

1⃣9⃣
Chapter 15 · 0% Book details