← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 94

Sashe 92

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewan doc ne, tambayoyi ya fara yimata, tana bashi amsa,
"Yaushe kika ga period dinki last..." Doc ya tambayeta, kallon Khalid tayi Sannan tace
" na mance
.." Tafada bakinta na rawa, murmushi yayi yana cewa
"Kuna honeymoon kin mance ko?..." Ya fada yana kallon Khalid, hararanshi Khalid yayi yana murmushi,
"Well from all indications your wife is pregnant... Dukda banyi test ba amma symptoms ne na pregnancy.. Sai ka kawota hospital mu duba lafiyanta..." Tunda yace pregnant Khalid ya wace baki don murna, itakanta Ameera saida ta sake murmushi, kanta kar kirjinshi. Bayan doc ya tafi Khalid ya dauketa ya rungume yana yimata godiya kaman ita ta halicci cikin.

Sanar da iyayenshi yayi suma sunyi murna sosai. Suna kwance bayan sun dawo daga hospital Sai tunanin Salem yake, bai mantaba sanda Tawakaltu ta samu ciki saida Salem ya sanar dashi
"Angel ina tunanin Salem..."
"Pls Ku shirya..." Ta fada cikin sanyin murya,
"Baby baya picking calls dina....har yanzu fushi yake dani...wallahi it is disturbing me..." Kara rungume shi tayi tana cewa
"Kaje wurin shi mana...ka bashi hakuri cos kai ka bata mashi rai..." Inji Ameera dake Kara kankame mijin ta kaman Zaa kwace matashi.
"Sai kinji sauki...I can't leave you now... " yafada yana shafa cikinta.

Abangaren su Salem kam har yanzu Tawakaltu na wurin Umma amma babu abinda hakan ke hana Salem don duk kwana biyu yake zuwa yola, Umma Sai mamakin shi take don da Sai yayi wata baizo gida ba amma yanzu every two days Sai yazo.
Yanzu cikinta ya kai wata shida going to seven duk fuskan ta ya chanza ka pimples, duk sanda Salem yazo yaje inda take Sai ya durkusa kasa yace
"Hajiya inawuni?..." Hakan yana bawa tawa haushi sosai, at times Sai ya kura mata ido ya tuntsure da Dariya, ta shika tayi fam ga takuran ciki ga na Salem.
Suna zaune kan dinning table dukkan su har Abba suna cin lunch, Salem ya daga kai ya kalli tawa ya tuntsure da Dariya, kallon shi tayi ta galla mashi harara ya daga mata gira,
"Zakuje gidan abokinka ko?..." Inji umma, Da sauri Salem ya kalleta,
"Umma wane abokina?..." Ya tambayeta don sam ya manta da su Khalid, hararanshi tayi
"Kana nufin bakasan Khalid ya dawoba?..." Da sauri ya saki murmushi
"Oho...nasani mana...bansan shi kike magana ba..."
"Aboki nawa gareka?..."
"Shi kadai...." Inji Salem, Abba kam baice kala ba cos shi yana daga cikin policy nashi baya magana while eating.

Bayan sun gama lunch ya tafi part dinshi yayi kwanciyan shi, har 4:30 bai nuna alaman zaije wurin Khalid ba donshi har yau bai bar jin zafin abinda Khalid yayi mashi ba, Umma ce ta shigo part dinshi, zama tayi shima ya mike zaune
"Habibi ka fada min gaskiyan abinda ke faruwa tsakanin ka da Khalid..." Da sauri ya saki murmushi
"Babu komai.."
"Da komai mana...Khalid da ya tsaya ya taya ka komai lokacin bikinka bakazo nashina dukda nasan haka nan kaki zu...Sannan yanzu na fada maka ka kai matarka amma nuna alaman kana son zuwa ba...son what is happening..."
"Umma ba komai.... Daman cewa nayi bari rana ta sauka Sai muje tunda na kirashi ya fada min inda gidan yake..."
"To kuyi sauri kuje... Baason mai ciki kan titi da magrub..." Tafada tana barin dakin.

Tawakaltu ya kira ya fada mata ta shirya zasu fita

Bata yi wasting time ba tayi wanka ta aka jallabiya ko kwalliya batayiba don ta kanta take, shima Salem wanka yayi ya shirya tare da sukaje dakin Umma sukayi mata sallama Umma tace
"Ku gaida su..."

Cikin mota suka shiga driver ya jasu sukafita,
"Ka kaini gidana..." Salem ya umarceshi, Tawakaltu kallon shi tayi
"Umma tace gidan sir Khalid zamu..."
"Baby I can't go to Khalids house...remember he denied my presence at his wedding..." Yafada yana jin haushi har cikin ranshi
"Amma ai yana kiranka...kai ne baka picking... Ni dai gaskiya ka kaini gidan..." Tafada tana harde hannuwanta kan kirjinta,
"No...muje gidana ..."
"Wallahi kasa driver ya kaini ko kuma in fadawa Umma " tafada kaman zatayi kuka.

Tsayawa yayi yana kallon ta, aikam kuka tafarayi tana cewa
"Kasa akaini..." Rarrashin ta yayi don ko kadan bayason kukanta, fadawa driver inda zasu yayi don yasan gidan.

Wurin bashi da wani nisa sosai don haka babu bata lokaci suka isa gidan, Salem kallon Tawakaltu yayi
"Princess ki shiga ki fito..."
"Bazaka shigaba?..."
"No..." Ya amsa mata atakaice, fita tayi driver ya fito yayi knocking a gidan, maigadi ya bude ta shiga, daya daga cikin gidan Wanda yayi kama da daakwai mutane tayi knocking, shuru baa bude ba, tafi minti biyar tana danna door bell.

Alokacin Ameera na kwance jikin Khalid don evening fever take, yana jin ana knocking amma bayason tashi, dole Ameera tasashi mikewa.

Tawakaltu har ta juya ya bude kofan, mamaki ne kwance kan fuskan shi,
"Aa...Ashe kece...come in..." Yafada yana komawa gefe, murmushi tayi ta shiga, gaisawa sukayi,
"Ya akayi kika gane nan?..." Ya tambayeta
"Tare muke dashi..." Da sauri Khalid yace.
"Yana INA?..."
"Yana waje..."
"To bari in shigo dashi kafin in kirawo Aisha...daman bata da lafiya ..." Yafada yana fita daga falon.
"Allah yasa ka shawo kanshi..." Inji tawa cikin ranta.

Khalid na fita chan waje ha hangi wata dunkulellen mota yasan Sai Salem, wurin motan ya nufa, Salem na ganishi ya daure fuska irin yana fushin nan. Khalid bude motan yayi
"Haba guy...fushin ne har yanzu shine bazaka shigo cikin gidana ba?..." Inji Khalid, Salem kallon shi yayi yaga yanda ya chanza
"Ni da baa son tarayya dani?...me zanyi cikin gidan ka..." Khalid shiga yayi cikin motan ya fara bashi hakuri, daman Salem yayi missing dinshi,
"Yanzu ko shigo ciki..." Inji Khalid, babu musu Salem ya fito, suka shiga cikin gidan.
Tawakaltu dadi taji sosai data ga Salem tare da Khalid, zama yayi gefen tawa shi kuma Khalid ya shiga inda Ameera ke kwance daga ita Sai pant and bra,Ahankali ya tabata ya bude ido daman ba bacci takeba,
"Baby...munyi visitors..." Ahankali tace.
"Su waye?...".
" Salem da matanshi... " da sauri ta mike zaune tana cewa
"Da gaske sir Salem da Tawakaltu sun zo?..."
"Yes..." Ahankali ta mike, jallabiya Khalid ya dauko mata tare da Vail, saka mata kayan yayi Sannan ta yafa Vail suka fito hannun shi rike da nata, suna fitowa Salem ya kalleta, itama ta chanza sosai amma alhamdulillah bai ji komai ba, rungume juna sukayi da Tawakaltu, gaisawa sukayi da Salem Sannan kowacce ta koma gefan mijinta, Khalid Dora kan Ameera yayi kan kafadanshi don yanajin tana nishi2 kasa2 Wanda shi kadai ke jin hakan. Hira sukayi sosai kaman ba friends dake fushi da junansu few minutes back ba.

Pls manage..
💙💜❤💛💚
ZAKISAN KONI WAYE
💛💚❤💙💜

®zuwairat( ummu Maryam)

8⃣3⃣

*My Sadnaf,Allah ya barmin ke ya kara basera, you are* *awesome and free of jealousy..Allah ya kara tsaremin ke daga sharrin masu sharri. The whole page is yours.*💋💋💋

Ameera Sai kara lafewa take jikin Khalid don sam bata jin dadin zaman, Salem da Khalid Sai hira suke ita kuma Tawakaltu hankalin ta na kan film da ake nunawa cikin MBC 2, suna cikin hira Ameera ta zame ta dora kanta kan cinyan Khalid tare dayin pillow da hannun ta, Khalid kallon ta yayi tare dayi mata magana cikin kunnenta, kai kawa ta gyada mashi,Salem kallon su yayi
"Guy bata da lafiya ne?..." Ya tambayeta yana kallon yanda Ameera ta lumshe idanuwa kaman mai bacci, murmushi Khalid yayi Sannan yace
"We're pregnant..." Idanuwa Salem ya kwalo yana cewa
"Woww...congrats..." Yafada Sannan ya kalli Ameera
"Sis congrats..." Ameera murmushi kawai tayi, Kara kallon Khalid yayi
"Mun dai girme ku..." Yafada cikin zolaya, Dariya Khalid yayi yana shafa kan Ameera
"Ba komai... AI baifi five months ba..." Tawa kam batasan abinda suke cewa ba don ko kadan hankalinta bai wajen, suna nan zaune aka kawo dinner daga government house, Khalid amsa yayi ya ajiye kan dinning, alokacin ana kiran sallan magrub
"Guy bari in kai Angel inyi mata alwallah Sai mu tafi masjid...." Inji Khalid, Khalid Dariya yayi yana cewa
"To mai angel...." Inji Salem, dukkan su Dariya sukayi, Khalid mikewa yayi ya dauki ameera sukayi hanyan bedroom din da suka fito, tawa kallonsu tayi ta saki murmushi tare da kallon Salem, shima kallon tayi
"Ya akayine?...ko kema so kike in dauke ki...Hajiya..." Bai idaba ta dauki pillow ta wurgamashi, dariya
Yana cewa
"Hajiya me nayi maki?..." Ya tambayeta yana kare fuskan shi da wani pillow yana dariya,
"Wallahi ka bar kirana Hajiya?..." Ta fada kaman zatayi kuka, Dariya yayi yana cewa
"Kwantar da hankalin ki....makka zaki haihu...innamu..." Yafada yana dariya sosai, buga kafa tafarayi tana cewa
"Ka dura min ciki kazo kana zolayata ko?..." Dariya Salem ya dingayi sosai
"Wai na dura mata ciki...wa yace ki budemin kafa?..." Pillow ta kara dauka ta buga mashi ya kauce yana dariya.

Khalid nashiga yayi wa Ameera alwallah Sannan shima yayi alwallah, har lokacin jikin ta zafi sosai
"Baby ko in kara maidaki hospital in su Salem sun tafi?..naga har yanzu bai saukaba..." Ahankali ta girgiza mashi kai
"Ai...mom tace in bar zuwa hospital wai ko naje babu abinda zasuyi min
..." Ta fada gwanin ban tausayi, kiss yayi mata ya shimfida mata praying mat, Sannan yace
"Baby Bari muje masjid..." Kai ta gyada mashi tare dacewa
"Ka fadawa sis Tawakaltu ta shigo nan tayi sallah..."
"Ok..." Ya amsa mata Sannan ya fita, yana zuwa yaga Tawakaltu sai jifawa Salem pillow take shikuma yana kaucewa yana dariya, shima Khalid murmushi yayi ya karasa inda suke yana cewa
"Wanda kukayi a gida bai isheku ba?..." Inji Khalid, Salem yana dariya yace.
"Wai don nace mata hajiya shine take fushi...."
"Sis rabu dashi...ki shiga ciki kiyi sallah... Kaikuma ga shiga chan kayi alwallah mu tafi..." Ahankali tawa ta mike tana hararan Salem, gwalo Salem yayi mata
"Zamuje gidane.." Tafada mashi Ahankali Dariya Salem yayi yana cewa
"In muje gida ki hana ni...." Da sauri ta shige shikuma Khalid ya saki dariyar rainin hankali yana cewa
"Ka San dadin abun yanzu ko....gashi ko kunyata bakaji..." Hararanshi yayi
"Da inji kunyarka gara... Inji kunyar dan akuya..."
Yafada yana mikewa, inda Khalid ya nuna mashi ya shiga ya dauro alwallah suka tafi masjid.
Chapter 92 · 0% Book details