← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 94

Sashe 48

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tawa shiga cikin palace tayi, tundaga bakin palace din tayi kneeling tafara rarrafawa har gaban oba, su Abba da OBJ kallon ikon Allah kawaisuke, Salem na tafe bayan ta, tafiya yake ahankali yana kallon yanda take kuka tana crawling kasa, cikin shessheka tafara cewa
"Grandpa.. Nasan shi....I know him...and... I love him... Am...sorry..." Yanda take maganan kaman ranta zai fita yasa oba daga mata hannu, amma batayi shuru ba ta cigaba dacewa
"Grandpa... I love.. Him..." Kai oba ya gyada mata alaman I understand, mami na tsaye bakin fada tana jin abinda tawa take cewa, duk mutanen wurin jikin su yayi sanyi Abba kam kaman zaiyi kuka yakeji, OBJ kam baki ya saki don tunda yake bai taba ganin event din da ya bashi tausayi irin wannan ba, Salem har lokacin bai bar hawaye ba ahankali shima yayi kneeling bayan ta, saida ya goge hawaye shi ya daidai ta murya sannan yafara cewa
"I promise... To take care of her...i will make sure she's happy.... She will be the only gueen of my heart... I will do everything.... For her...." Mami duk tana jin abinda yake cewa oba daga kai yayi ya kalleta
"History is repeating itself..." Oba ya fada cikin ranshi, kallon tawa da Salem yayi
"Ni ba dangin uban Tawakaltu bane...am amatsayin na na sarkin gari da kuma grandpa dinta...na baka Tawakaltu..." Da sauri OBJ da sauran mutane suka kwanta kasa suna godiya, shima Salem kwantawa yayi, duk yanmatan gidan suna tsaye bakin window suna kallon kuma suna jin abinda ake cewa, dukkan su ihu suka fara suna tsalle, tima hannu tasa bayan kunnenta kaman tana sauraron wani few seconds later tace
"I can hear a wedding bell ringing.." Dukkan su ihu suka karayi, jikin mami ba kwari ta bar bakin palace ta koma part dinta, dukkan mutanen komawa sukayi suka zauna, ahankali Salem ya mike yakara kneeling, har lokacin tawa bata tashi ba, ahankali ta juya zamanta ta fuskanci Salem, cikin rawan murya tace
"Am sorry..." Girgiza mata kai yi
"No...am sorry for hitting you..." Yafada cikin whisper yana kallon yanda ya bar hannun shi kan fuskanta. Ahankali ta mike shima ya mike, tafiya ta farayi amma kaman iska na kadata, da kyar ta kai baki palace, Salem na bin bayanta don inda babu Abba awajen da daukan ta zaiyiko gaban uban waye, tana fita yanmatan suka rungume ta ta fada jikin su tana kuka, dukkan su tsaya kallon sir Salem in flesh and blood sukayi, Dan murmushi yayi sannan yace
"Excuse me ladies..." Dukkan su daria sukayi suka sakar mashi tawa. Hannunta ya rike suka kama hanyan part din mami, har sun kai bakin kofan tawa tadan tirje tana girgiza mashi kai, shima girgiza mata kai yayi sannan bude kofa, mami ce zaune sai hawaye take, babu abinda take tunawa sai irin tsangwaman datasha wurin family mijinta, gani suke ita tasa ya juya masu baya wai don tana princess. Ahankali Salem ya saki hannu tawa ya zauna gaban mami, ahankali yafara cewa
"Mami... Nasan bani ke bakiso ba...halin mutanen mu da kika zauna dasu ke bakiso...Ni ina daukan maki alkawarin zan kula da yarki kaman yanda zan kula da kaina..." Mami goge hawayenta tayi sannan tace
"Allah ya ba ikon kula da yata... Dan Allah duk laifin dazatayi maka..please kar ka saketa...ka hukuntata...please" dan murmushi yayi
"Sakin mata baya cikin dictionary dina...insha Allah I will show you that we are not all the same..." Kai kawai ta gyada mashi
"Kam irin wannan wahalan Dana sha kanta zan saketa?... Ai intayimin laifi ubanta zanci mu shirya.." Yafada cikin ranshi. Mikewa yayi ya bar dakin, tawa kam rakubewa tayi jikin bango don gani take mami zata cimata for going against her order. Mami mikewa tayi ta koma bedroom dinta, da sauri tawa tashiga nata bedroom din ta kwanta tana jin dadi.
Salem na fita ya hangi yanmatan zaune cikin balcony suna ganin shi suka fara kus2 kuma maganan shi suke, kallon white leg dinshi mara takalmi sukayi, har ya Dan wucesu ya dawo wurin su,
"In-laws.. Can I know the names of these beautiful ladies?..." Ya tambayesu sounding so naughty, da sauri suka fara introducing Kansu dan murmushi yayi yana godewa Allah da bada Khalid yazo ba don yasan babu abinda zai hanashi flirting dasu in yana nan, bayan sun gama
"Lovely names.." Yafada yana saka hannu cikin aljihunshi, ATM ya fiddo sannan ya fara cewa
"Ga ATM ...Ku shiga cikin gari Ku nemawa princess dina the most expensive phone... Sannan each and every one of you should spend 200k..." Ihu suka farayi suna Neman tada palace din,
"For us?.." Suka fada gabaki dayansu, murmushi yayi yana daga gira daya
"Yes..babies...you know money is not the problem..."
"We know handsome!" Suka fada in chorus, wacce tafisu shekaru mai suna mufida ta amshi ATM din sannan ta kalli sauran
"Sis Ku kirani nan in dauko car keys.."
"OK" kawai suka amsa mata, Salem wani murmushi yayi ya kama hanyan cikin palace.

Su Salem na barin palace OBJ ya kalli oba sannan yace,
"Tunda an gama wannan sai Ku bamu list da kuma ranar introduction.." Oba dariya yayi
"So soon haka?" Abba dadi yaji yanda OBJ yasan abinda ke cikin ranshi
"Meye na wasting time kuma?... Kawai mu gama mu dauki yarmu.." Dukkan su dariya sukayi sannan oba yace
"To yanzu zan aikawa iyayen yarinyan maza...zuwa next two weeks kuzo sai Ku amshi list..." Kai OBJ ya Dan girgiza
"Ranka shi dade two weeks yayi mana yawa...ka Dan rage mana..."
"OK...bakomai... Ku dawo zuwa next week..."
"Godiya muke.. So ranar zaayi fixing din ranar introduction ko?.." wani uncle Salem ya tambayi oba
"Insha Allah..."

Salem na shigowa ya zauna kanshi kasa, acikin zuciyanshi kam dadi yakeji Mara misaltuwa.
Yanmatan sa suka tafi shopping kam basu dawoba sai 5:30pm lokacin su Salem sun dawo daga masjid suna zaune palace, hira kawai su Abba da oba suke, shikam so yake ya kara komawa wajen tawa su danyi hiran wedding preparations, hakuri yayi tunda ba yau zasu koma ba, da sun koma government house zai sabe ya dawo.
💜💙💛💚❤
ZAKISAN KONI WAYE
💛💚💙💜❤

®zuwairat(ummu maryam)

4⃣9⃣

Tawa najin anbude kofan dakinta tayi saurin mikewa zaune, mami tagani tashigo jikinta duk babu kwari, gaban tawa ne yafara disco cos gani take mami dukanta zatayi, mami batace komai ba ta zauna gefen gadon, tawa rakubewa tayi jikin bango, mami tafi minti biyar zaune batace kala ba, sai daga baya tayi ajiyan zuciya sannan tafara cewa
"Yanzu tawa duk maganan danayi maki saida kika nuna kin sanshi?.. " tafada cikin sanyin murya, tawa bata ce komai ba tafara sabon kuka, hannu mami ta daga mata alaman tayi shuru, nan take ta hadiye kukanta
"Yanzu tawa har kinyi girma da bazaki bi umarni na ba?... Ko kina ganin farincikin ki ke banaso" shuru tayi for a moment sannan tacigaba dacewa
"Sam ba haka bane...kawai banason abinda zsai tabamin ke..kuma banason ki sha wahalan Dana sha...yana making promise wai zai yi this and that... Its all lie.. There is something he sees in you..the moment ya dauki wannan abun zai ajiyeki gefe ba fata nake maki..." Tawa ji tayi gaban ta na faduwa don gani take maganan mami gaskiya ce ba kaman in ta tuna yanda yake maganan sex cikin waya, taji mami nacewa
"Kuma tunda ummanshi bata sonki koshi baiyi aureba dole zata aura mashi mata yarensu lokacin zaki koma..." Shuru tayi dataga tawa ta fara kuka sosai, mami tsaya kallon ta tayi
"Ki bar
wannan kukan cos there is no going back..." Cikin kuka tawa tace
"Mami..yace Umma ta yarda.." Baki mami ta tabe sannan tace
"Allah yasa..nidai kullum inayi maki aduan kar Allah yasa kisha wahalan Dana sha a baya..and I will continue praying for you..." Tawa batace komai ba ta cigaba da kuka, ahankali mami ta jawota jikin ta.
Chapter 48 · 0% Book details