← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 94

Sashe 86

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Around 11 ta isa ta kira number da Salem ya turo.
Bayan kaman minti 40 majed yazo cikin wata white Prada, gaisawa sukayi, ya kalleta
"Pls I want to ask for your forgiveness kan Marin danayi maki..." Murmushi tayi
"Bakomai halina ya jamin after all ni na fara marinka so nima forgive me..."
"Godiya nake..." Ya ce mata Sannan ya shiga motan shi itama tashiga nata tabi bayanshi.
Around 1pm suka iso gidan, wangale ta tadda gate din, yaran unguwan sun shika gidan,
Murmushi tayi tare dayin horn yaran suka matsa gefe ta shiga da motanta, hinde ta hanga zaune gefen compound din da kayan tireda gabanta, tana ganin motan ta mike tana kallon motan cikin ranta kam tunani take masu gidan ne sukazo don su tada su. Ahankali ta dinga takawa tana karasowa wajen motan, Ameera na gama parking ta fito, Zainabu ce ta fito daga daki tana kallon Ameera, itama hinde wangala baki tayi tana kallon ta don Sam basu ganeta ba, Zainabu na Kara kallon ta sosai ta gane aikam da gudu ta tafi suka rungume juna, har lokacin hinde bata ganeta ba
"Innamu...Ameera ce..." Inji Zainabu, nan sauran yaran da hinde suka rungume ta suna shakan kamshin turarenta. Ameera kam lumshe idanuwa tayi don jindadi don tamkar family suke a wajenta, wurin kayan saidawan hinde ta kalla tana dariya tace
"Ashe kuna nan kuna kwasan dala...." Tafada tana dariya,
"Alhamdulillah... Ai Sai godiya..." Hinde ta amsa mata, daki suka shiga, ta zauna kasan carpet, suka fara hiran bayan saduwa, Tambayanta hinde tayi me zataci tace dan wake, aikam nan hinde ta hau girki Ameera da Zainabu na zaune gefe suna hira da Zainabu
"Babu mai gane kece.." Inji Zainabu, Dariya kawai Ameera tayi Sannan Zainabu tacigaba dacewa
"Ya kuka kara da Salem?..." Ta tambayi Ameera, nan Ameera ta kwace komai ta fada mata
"To Allah ya zaba maki mafi alkhairi.." Inji Zainabu,
"Hmmm ameen.. Ai shiyasa nazo...wallahi na rasa Wanda zai bani shawara..." Inji Ameera, Zainabu gyara zama tayi
"Meke faruwa kuma?..." Labarin sultan da Khalid ta fadawa Zainabu batare data boye mata komai ba, Zainabu shuru tayi tana sauraron ikon Allah
"Yanzu meye abinyi yi?..." Zainabu ta tambayeta
"Nama ban saniba...amma gaskiya inason in rabu da Khalid saboda dangatakar dake tsakanin shi da Salem Sannan kuma ya fada min shi manemin matane...."
"Hmmm...ai don wannan ba wani abu bane saboda da bai fada maki ba bazaki Sani ba....kuma..."
"Badai kina cewa in auri mazinaci ba..." Ameera ta tambayi Zainabu looking very surprised
"Ai gwara shi da ya fada maki... To shi sultan kinsan ayar da yake shekawa?...AI ki kalli maza kawai... Wani kaman ustaz amma in kikaji abinda sukayi kare baici...."
"Koma dai meye ba zan iya auran shiba....sultan kawai zan zaba..."
"To Allah yasa haka shi yafi alkhairi.. Amma kince tin kina yarinya kika san sultan... Meyasa baisoki ba sai yanzu da duk kyawun jikin ki ya fito?... Ni gaskiya gani nake Khalid yafi sonki fiye da sultan kuma anason mace ta auri Wanda yafi sonta ba Wanda tafi soba..." Ameera tsaya kallon Zainabu tayi
"Amma wallahi kin bani mamaki....mazinaci fah?...."
"Sai maimaita mazinaci kike...inda bai fada maki ba zaki Sani?..… kuma ki tuna in har kika aureshi ya chanza halin shi saboda ke zaki samu lada babba..."
"In bai chanza ba fah....sai inyi yaya?..." Ameera ta tambayeta
"Zai chanza tunda har ya bude baki ya fada maki hakan....ni wallahi ya kwanta min..." Ameera tabe baki tayi ta kauda kanta gefe ,
"Kilan ma shine Wanda yazo nan wace garin tafiyan ki..." Inji Zainabu
"Wani yazo nan bayan tafiya ta?.."
"Eh mana....wani farin mutum mai saje... Dukda ban san Salem ba nasan bazai fi wannan mutum daya zo nan kyau ba..." Ameera shuru tayi don kwatancen Zainabu ya nuna cewa Khalid ne,
"Yanzu dan Allah ki bani shawaran abinyi..." Ameera Tafadawa Zainabu, Zainabu kallon ta tayi
"Nidai anawa tunanin... Ki zabi Khalid... Ba don kun dace ba...amma don tseratar da rayuwan shi...." Ameera gallawa Zainabu harara tayi tana cewa
"Amma in kece bazaki zabeshi..." Bata idaba Zainabu tayi Dariya Sannan tace
"Wallahi kinji rantsuwan Dan muslimi?...in nice shi zan zaba...kin San saboda me?..." Kai kawai Ameera ta girgiza mata Sannan tacigaba dacewa
"Saboda ya fada min gaskiya game kanshi....wallahi mazan talakawa iskanci sukeyi balle su da ga kudi ga kyau...don haka shawara ya rage naki..." Ameera dai shuru tayi tafara tunani,
"Hmmm...kilan shima sultan ya taba... Shi dayake da budurwa baturiya?... Su da basu dauki zina bakin komai ba...Hmmm" Tafada cikin ranta,
"Amma ki kara fadawa innamu muji nata shawaran.." Inji Zainabu.

Bayan taci Dan wake ta fadawa hinde komai,
"Gaskiya bazance ki zabi kowaba acikin su... Kawai abinda zakiyi shine intahara...kiyi shi adaren yau...Sai muga abinda zai biyo baya..." Inji hinde
"To shikenan...". Tafada tana nufan boot din motanta , budewa tayi tafara fiddo kayan da taimakon Zainabu.

Adaren ranar tayi aduointa ta kwanta bayan sun sha hira da su hinde, mafarkin datayi ya bata mamaki, don Khalid tagani da pure white jallabiya yana fada mata how much he loves her,exactly maganganun daya fada mata shekaranjiya ya dinga maimaitawa shima sultan was wearing a white cloth but not as pure as na Khalid.
The following day ta fadawa hinde mafarkin datayi.
" zabi ya rage naki..." Tafada mata.
Around ten ta kama hanyan Kano, tana shan kwanan street dinsu ta hangi wani hadadden mota tsaye wajen gate dinsu, tana karasowa wajen taga Khalid ya fito daga cikin motan, da sauri tayi parking gefe daya ta fito, gani tayi yayi mugun rama kaman ba shiba, idanuwanshi sun chanza kala, karasa wurin shi tayi shima ya nufota
"Baby why are you doing this to me?..." Ya tambayeta muryan shi na rawa
"I will marry you..." Shine abinda ta furta mashi, da sauri yace
"Are you for real or am dreaming..." Da sauri tace
"For real..."
"Thank you so much... I promise to make you happy till the end of my life... Thank you for choosing me even after you know my dirty secret..."
💙❤💜💚💛
ZAKISAN KONI WAYE
💛💚💙❤💜

®zuwairat(ummu Maryam)

7⃣9⃣

Murmushi tayi tana kallon shi
"Nima Nagode..."
"No ni keda godiya..." Yafada yana kallon eyeball dinta, kaman ya dauketa ya gudu yakeji, gani yake kaman anyi mashi albishir da gidan aljanna
"Baby zan tafi Adamawa in fadawa his excellency da first lady na samu matan aure..." Murmushi tayi
"Kashigo ciki in baka ruwa..." Da sauri ya girgiza mata kai
"I have to be on my way..." ya fada yana backwards zuwa wurin motanshi, kiss ya busa mata itama ta busa mashi Sannan ya shiga mota ya bar wajen da gudu, itama mota tashiga tayi horn aka bude mata tashiga tayi parking tayi cikin falo da gudu, da gudu ta hau upstairs har dakin mom, tana shiga ta fada jikin mom ta rungume ta
"Habibty ya hanya?".
" alhamdulillah... "
"Ya su hinde?..".
" suna lafiya.. Sunce in gaisheki..." Tafada sounding very excited
"Habibty.. Why do you seem happy... Ko da akwai abinda kikeson fadamin..." Tafada tana kallon how light up fuskan Ameera yake,
"Mommy.. I have choosen Khalid... Shi zan aura..." Tafada kanta kasa, tsaya kallon ta tayi
Mom dago fuskan ta tayi tari rike cikin palm din ta Sannan tace
"Yanzu habibty kinfi son Khalid kan sultan?..." Ahankali ta dagawa mom kai
"To Allah yasa haka shi yafi alkhairi..." Dasauri tace
"Ameen.." Kwantawa tayi kan gadon mom har dad ya dawo, wajen shi taje ta fada mashi abinda ta fadawa mom,
"Waye babanshi?.." Dad ya tambayi Ameera,
"Governor na Adamawa..." Ta amsa mashi, dadi dad yaji cikin ranshi,
"Zan zama in-law na governor..." Ya fada cikin ranshi, kunsan mai hali baya barin halinshi especially in ya zame maka jiki,
"Ki fada mashi ya turo..." Inji dad, da sauri mom ta kalleshi
"Ai ya kamata ayi bincike ko?.." Gaban Ameera faduwa yayi tana tsoron kar a binciko Khalid
"Wane irin bincike kuma?...waye baisan governor na Adamawa da mutunci da sanin ya kamata ba?..."
"AI bashi zata auraba danshi zata aura...."
"AI ba sai..." Dad bai idaba mom ta katseshi dacewa
"Zaka farako?...haka kayi lokacin aurenta da Salem... Kuma..." Da sauri dad ya daga hannun shi
"Shikenan... Ayi binciken....karki jamin sharri..." Itadai Ameera zama tayi tana sauraron su
"Tashi kije kici abinci..." Mom ta fada mata, mikewa tayi ta koma dakinta, kayan cikinta ta cire ta kwanta Sannan tayi dailing number sultan, nan ta fada mashi she have something to tell him.

Bayan sallan magrub yazo, hakuri ta fara bashi
"Pls can you hit the nail at the head?.." Ya fada mata dukda ya gane abinda ke faruwa, nan ta fada mashi ta fidda miji, murmushin karfin hali yayi Sannan yace
"Haba jewel...saboda wannan kiketa kame2 kaman kinyi abun kunya?... In baki mantaba I told you duk yanda Allah yayi daidai ne....so na dauki kaddara...." Yafada cikin sanyin murya, she never expect to hear that from him,
"Thanks for your understanding..." Tafada ahankali, baice kala ba ya mike
Ya fuskance ta, yana kallon beautiful and innocent face dinta, ahankali ya jawota jikinshi ya rungume ta, da sauri ta zame tana waige2 don ta tabbatar babu Wanda ya ganta, murmushi kawai yayi Sannan ya shiga motanshi ya tafi. Ameera komawa ciki tayi tana shakan free air don ji take kaman ta sauke mountains daga kanta.

Khalid kam yana tuki yana waya da Salem, nan ya shaida mashi Ameera ta amince zata aureshi.

Yana isa gidan su ya shaidawa first lady ya samu Matan aure, murna wurin ta baa magana Cos babu abinda take so kaman first son dinta yayi aure
Tunda Salem yayi aure take aduan Allah yasa shima yayi cos there are bird of the same feathers so there flug together. Dad dinshi ya fadawa shima wise man din cewa yayi
"Sao yanzu ka gandama kenan..." Khalid Dariya kawai yayi,
"Sai ayi bincike kan family dinsu kafin muje ayi maganan aure..." Inji his excellency,

_One week later_

Duk binciken daya kamata su dad sunyi kuma babu Wanda bai shaidan halin Khalid ba, asalima cewa akayi yafi sauran brothers dinshi mutunci, ( hmmm daman bincike baisa agane dukkan halin mutum.. Sai ka zauna dashi)
Chapter 86 · 0% Book details