← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 94

Sashe 4

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Afusace Matan tace
"Me nake gani haka...what's happening?" Tambayan data jero masu kenen Amman yarinyan bata juyo ba balle ta amsa mata sai nuna mutum da ta watsawa ruwan take tana cewa
"Yanzu ya kaji ajikinka?...don dabbanci Ashe karasa abinda zaka wanke sabon murano dina sai detergent?. …" ahankali mutum Wanda zaiyi shekara 40 yace
"Allah ya huci zuciyanki...wallahi car wash ne ya kare...Ku..." Bai karasa ba ta katseshi da cewa
"To sarkin jahilai data kare agidan nan sai ya kare a kasuwa ko?..to wallahi...." Bata karasaba Matan saman bene ta kara cewa
"Wai badaku nakeba?!" Tafada atsawace. Mutum Wanda sai rawan sanyi yake a sanadiyan ruwan sanyin da aka zuba mashi ya daga kanshi ya kalli Matan dake saman bene sannan yace
" Hajiya don na wanke motanta da klin shine ta watsamin ruwan klin din a jikina" yafada kaman zaiyi kuka, Matan komawa baya tayi da alaman kasan bene zata sauko , yarinyan tana juyawa taga babu Matan saitayi saurin komawa cikin don kar matan tarisketa, itama matan sauri take don tasan halin yarta, lokacin daga suka hadu afalo
"Ameera da gaskene abinda umar yafada?" Ta tambayi yarinyan fuskanta babu alaman wasa, Dan matsawa baya tayi sannan tace
"Mummy he wash my brand new jeep with..." Bata karasaba Matan ta sharara mata mari Wanda yasa kunnenta tsaya jin, yarinyan dafa kunnenta tayi tana kuka tana kiran daddy.Matan tacfigaba dacewa
"Maimaita abinda kikace..." Yarinyan batace komaiba sai kiran daddy take
"I said repeat what you said" ta daka mata tsawa, da sauri tafara cewa
"Mommy kiyi hakuri...ruwan klin na watsa mashi..." Wani Marin Matan ta kara mata, wani irin rikitaccen ihu ta saki still tana kiran daddy
"Ameera kika zubawa age mate din ubanki ruwa?..ameera rashin hankalinki ya kai haka? ...ni like son jawa zagi a garin?...." Cikin kuka tace
"Ni ba saan ubana bane..." Wani irin mutum duka matan ta kaimata, aikam nan yarinyan ta kwanta kasan ta rolling tana kuka tana kiran daddy na...ihunta yasa wani mutum tahowa daga saman bene da gudu don har neman silbewa yake don sauri
"Ameera daddy meya faru?" Ya tambayeta, tana ganinshi ta tashi da gudu ta fada jikinshi, riketa yayi ya sake cewa
"Ki gayamin abinda ke damunki" dakaji yanda yake magana kasan yana cikin tension kuma kasan bai hada wannan yarinyan da kowaba. Matan bata kalleshiba tashigaba dacewa
"Ameera ba baki nayi makiba Amman ke macece kuma in har baki bar wannan halin ba shi zai jamaki wahala" wani dan saurayi ne Wanda bazai fi shekara 12 ba dake zaune kan dinning da alaman yana homework Yayi saurin cewa
"Mommy jiya ma dan tace ya siya mata Mtn na 1k ya sayo na 5 hundred guda biyu tayi ta zaginshi tana cewa jakki jahili..." Ran Matan kara baci yayi ta nufe, ameera bayan daddy ta boye, shikam daddy ya hada rai sannan ya kara cewa
"Wai me kika yi take dukkanki kaman jakka?" Ya fada afusace, cikin kuka ameera tafada cewa
"Daddy wai dan umar mai wankin mota ya wanke motata da klin na zuba mashi ruwan ajikinshi shine mommy take dukana" afusace babanta yace
"Wai dan ki nunawa mai aiki Laifinshi take dukanki?" Cikin shagwaba ta dagawa ubanta kai, mutumin jiyawa yayi ya kalli Matan , itakam Matan ko kallonshi batayiba ta banbare ameera daga jikinshi zata kara dukanta mutumin yayi saurin rike mata, yana cewa
"Wai meye haka...ki bar dukanmi daughter don ta nuna..." Bata bari ya karasa ba tafara cewa
"Wallahi alh ka barni in hukunta yata tunda bakai zaa zagaba...nice uwa kuma nice zaa zaga..haka wannan yar iskan yarinyan tajtaza zana tattoo kaman wata karuwa amman ka hanani hukunta..." Mutumin Dan daria yayi sannan yace
"Hajiya banda Africa mentality.. Daga tattoo sai yarinya tazama yar iska?..kullum INA gayamiki yarainta ke damunta...watarana ko ance tayi bazata yiba...so...." Cikin fada Matan tace
"Ba wani yarinta...kawai kana goya mata baya..yanzu Aisha bata ganin uban kowa da gashin arziki...to wallahi gidan nan ni dakene..ko ki chanza ways dinki ko kuma in hallakaki dan wallahi bazan haifi yar dazata jamin tsinuwa ba..." Tana kaiwa nan ta hau stairs tabarsu, ameera cikin kuka tafara cewa
"Daddy ka kaini gidan anty Safiya...mommy bata sona" dan rarrashinta daddy yayi sannan ya haura daita dakinta, wani irin harara ta watsawa yaron
" affan zan kamaka" tacewa yaron.

Ameera dai irin yanmatan nan ne dabasu ganin kowa da gashin arziki mussaman in kana karkashinsu, daka ganta saika rantse yar barikice don komai nata irin nayan bariki, don har tattoo gareta abayan wuyanta, a bangaren samari kam babu namijin dazai ganta ya kauda kai, amman wulankanci kam kaman daita aka hallinceta don zagi kwando2 taiya kuma dad dinta is hundred percent behind her, kyakyawa ce na gidan karshe . Tana 200 level a b.u.k She's the first born sai kaninta affan Wanda Sam ba halinsu dayaba

💛♥💙💜💛💛♥

"Ma-mi am going.. Kuma insha Allah in aka bani kudi yay zan sayo maki inhaler dinki" inji wata yarinyan da ke tsaye ratayi da dan tsohon handbag, da ka kanta kasan ba bahaushiya bace, yarinyan tana da kyau Iya gwargwado don bakace, Amman inda zata sami hutu zatayi kyau fiye da yanda take, mata dake zaune kan wata tsohuwar kujera tace
"Tawakaltu..." Yarinyan ta amsa tana rusunawa kusa da Matan sannan Matan tasake cewa
"Ki dawo lafiya" ahankali yarinyan yace
"Ameen mami" yanda take maganan ya nuna tana da respect, dan rungume matan tayi sannan ta fita daga dakin room and parlour, tana fita tsakar gidan naga ashe gidan mutane ne dayawa don dakunan dake gidan zasuyi takwas kuma da ganin duk ciki da falone, wata mata dake wankeke ta gaida cikin girmamawa sai naji matan tace
"Toyin ..zaki tafi" sunan da aka kirata ya tabbatar min cewa yorubace, amsawa yayi sannan ta fita, duk yaran gidan sai bye bye sukeyi mata.

♥💛💙💙💚

Abangaren slim kam ana sauran sati daya tafiya yasa aka gyara gidanshi na Kano tare da zuba mashi sabon furniture, awurin parking kayan sawanshi kam suka samu matsala da Abdul, don Abdul cewa yayi dole ya sake siyan kaya Nigeria made tunda dukkan kayanshi designers ne, kememe slim yaki, da kyar Abdul Abdul ya shawo kanshi ya yarda aka kawo mashi kaya daga wani classic boutique suma saida Abdul ya sakasu a cikin washing machine yayi masu wanki kusan sau biyar suka dan koke sannan ya linkesu cikin watan katuwan traveling bag batare da angogesu ba, shikam Salem shuru yayi don Abdul is now the boss kaman yanda yake cewa.

💚💜💛♥💙
ZAKISAN KONI WAYE
💜💛♥💚💙
®zuwairat(ummu Maryam)

6⃣

Sauran kwana uku da tafiya Salem ya tafi yola ya shirgawa ummanshi gaskiya da karya amman ya gayawa abbanshi gaskiyan abinda zaiyi kuma ya bashi full support don abbanshi yafi ummanshi saukin kai.

Dukkan guards dinshi sunce zasu bishi Amman yace su zauna su jirashi har yadawo, da Abdul kawai zashi.

Ranar Thursday suka isa kano,kuma agidanshi na Kano suka sauka dukda Abdul nada babban gida a kano Salem cewa yayi I need my space.,

bayan kwana biyu Salem na zaune yana tunanin anya wannan ba stupid idea bane? Ya zaiyi kamanshi ace yayi descending so low don yana son true love.
"You can just back down" wata zuciya tace mashi
"No..not now.. I know it will be fun" ya fadawa kanshi, yana cikin tunanin ne Abdul yayi sallam yashigo tare da wani good looking guy. Ahankali ya amsa masu sallaman tare da daga kanshi yana kallonsu, cikin respect guy da suka shigo da Abdul ya gaida Salem cos yasan shi waye.

Bayan sun zauna Abdul yace
"Sir wannan guy din shine zai dan chanza maka kammanni da cosmetics" kallonsu Salem ya tsayayi for a moment sannan yace
"OK" guy din ya dan runtsuna sannan yace
"Alh zamu fara yanzu" ya fadawa Salem
"OK" ya sake ce mashi. Wata katuwan bag gayen ya dauko ya fiddo wasu abubuwa kaman kayan kwalliya , kallon kayan Salem yayi sannan yace
"Me zaayi da wannan cosmetic din?" Ya tambayi gayen
"Dasu zan dan chanza maka kamanninka.." Ya amsa mashi
"Hope basu da side effects" ya sake tambayanshi, dan murmushi guy din yayi sannan yace
"Not at all sir"
"OK then..let's begin" Salem yace mashi.

Kayan ya kawo gabanshi sannan ya fara dan shafa mashi kayan, Abdul kam zai kallonsu yake, da sun hada ido sai ya galla mashi harara.
Sunfi minti ashirin suna abu daya sannan guy din ya dauko gemu, mara tsawo, kallon beard din Salem yayi sannan yace
"Is this necessary?" Ya tambaya yana kallon gemun with disgust
"Yes sir...wannan zai kara badda kamanninka" Abdul ya amsa mashi, Salem baice komaiba ya mike ya dauki iPad dinshi sannan ya kunna mirror cikin, kallon kanshi yayi, sai yaga an rage mashi haske sosai, amman still duk Wanda yasanshi daya ganshi zai ganeshi, kallon guys din yayi sannan yace
"Zan koma original color dina kuwa?" Daga mashi kai yayi
"Yes sir...da akwai wani makeup remover da zan baka Wanda zakayi amfani dasdashi kullum kafin ka kwanta"
"Are you telling me kullum zaka dinga yaba min wannan abun a fuskata?" Ya tambayeshi sounding so inquisitive,
"Yes sir..kasan in kayi amfani da makeup remover komai zai goge har sai mun sake wani" guy din yayi mashi bayani
"Ni dai babu abinda zai sami fuskata ko?" Ya kara tambayan gayen
"Sir kar ka damu" yakara jaddada mashi. Sannan Salem ya koma ya zauna aka saka mashi gemun. Daya kalli madubi yaga kamanninshi ta Dan sauya.

Bayan guy din ya tafi suka fita da Abdul cikin wata old modern Toyota corolla, yana tuki Abdul na nuna mashi gari sannan yana gaya mashi sunayen wuraren.
Chapter 4 · 0% Book details