← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 94

Sashe 63

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai 11:30 suka isa Malibu California Berkeley, wani madaidicin gida mai katon grass carpet daga da swimming pool, gidan bai cikin gidaje don babu houses wurin sai lovely trees, sauka Salem yayi ya kama hannun ta suka zo baki kofan, wani wuri ya bude ya dauki keys. Bude gidan yayi suka shiga, wani katon falo ne sai Bedroom daya da kitchen sai dinning area, ga hanyan stairs, bata ankaraba taji Salem ya dauketa yayi kan stairs daita, saida ya yaje sama Sannan ya sauketa, gani tayi shima falo ne yasha red petals daga bakin kofan har wani kofan, kofan Salem ya bude taga red flowers kan gadon, dakin ya mugun tsaru
"Wa yayi wannan aikin .." Ta tambayeshi ahankali,
"Mrs Samuel mai aikina..." Ya amsa mata yana rike da hannun ta, gaban wani kofa yaje ya bude, gani tayi dukkan dakinsexy dresses ne nata da Dana Salem.
"Beautiful..." Ta fada
"Not as you..." Ya fada mata, fitowa sukayi ya nuna mata taje ta bude shi bathroom ne mai dauke da naurorin wanka kala2. Salem karasawa yayi wajen ta ya juyar da ita ya fara kissing dinta, itama kissing dinshi tayi with all her heart Sannan ya janye
"Muyi wanka...sai fara honeymoon.." Murmushi karfin hali tayi
"Ka farayi..." Bata idaba ya dauketa ya sakata cikin bathtub dake dauke da ruwan kunfa mai kamshin gaske, kayan jikin shi ya cire ya shiga ciki. Hot romance sukayi wa juna Sannan ya fito ya daura towel ya mika mata wani, amsa tayi ya fita rike da hannun ta su biyu daure da towel.
Dakin kaya suka shiga ya saka three quarters tare da polo mara nauyi ya saka ya kalli yanda tayi tsaye tana kallon kayan
"Please baby wear something sexy...ina jiranki..." Ya fada, ya taka cikin kasaita saida ya kai bakin kofan ya juya
"Don't keep your sugar waiting.." Yafada Sannan ya fita, yana zuwa ya ga wayanshi na ringing, kafin ya dauketa har ya tsinke, dubawa yayi yaga Khalid, kafin ya ajiye ya fara ringing picking yayi yaji Khalid nacewa
"Mr honey in the moon..ya kuke?.." Dariya Salem yayi
"Fine..."
"Round nawa kukayi yanzu?..." Tsaki Salem yaja yana dariya
"Kai banason iskanci... Why do you call?"
"Gaka babban Dan iska....anyway.. Ina rokonka da Allah.. Da manzon Rahama...da son da kake yiwa iyayenka...in kanason ganin annabi da banzan idanuwanka..."
"Dalla wai meye?..."
"Please in beg you with the name of Allah... Kayimin typing din letter nan ka turo min yanzu..."
"Naji...I will send it to you right away.." Yafada yana kallon kofan dakin da tawa take. Da sauri yabawa kofan baya ya dauki palmtops dinshi ya fara typing.

Tawa na ganin ya fita ta dauki wani red gown ta saka taga daidai ita saidai bai kai kwaiwanta ba amma yafi dukkan sauran kayan decency, kallon kanta tayi Sannan ta bude kofa ahankali ta fito Salem tagani tsaye, ahankali ta taka ta karasa kusa da bayanshi abinda taga yana typing ya sata kamewa waje daya
_"Ni Salem Yusuf sulaiman na saki Aisha umar Adam saki daya, biyu,..uku_ " tana kallo ya tura, jiri tafara gani, ajiye palmtop din yayi ya fara kiran Khalid
"Shege maye na sakar maka ita..." Ya fada yana juyawa daidai lokacin da tawa ta yanke jiki ta fadi kasa, da sauri ya yarda wayan yayi kanta.

💚💛💜💙❤

Bangaren ameera tunda ta kalli traditional wedding din Salem duniya yayi mata tsaye, ta chanza sosai don ba karamin rama tayi ba duk hankali su hinde ya tashi don da kyar suke samu taci abinci, kuma tunda jikaranjiya take menstral cramp kuma tasan jiya akayi daurin auren Salem da tawa, adua take kawai Allah yasa ta ga takardan sakinta yau don ta koma gidacos rabonta da waya da iyayenta tun ranar traditional wedding dinsu. Kuma tana aduan Allah yasa kar Salem ya kori su hinde daga gidan da suke.
❤💙💚💛💜
ZAKISAN KONI WAYE
💛❤💙💜💚

®zuwairat(ummu Maryam)

6⃣2⃣

Maganin ciwon ciki hinde ta ballar mata, bata amsa ba ta girgiza mata kai
"Kisha mana.." Inji hinde, Ahankali ameera ta kara girgiza mata kai
"Ki bar kawai.. Banason in samu sauki...so nake akawomin takardar sakina in je gida...so nake mom ta gan riban wulakanta mutane dana dingayi..." Tafada cikin kuka, Zainabu ma fashewa tayi da kuka, su biyu hada kai sukayi waje daya suka dinga kuka kaman anyi masu mutuwa, kawai sai sauran yaran hinde suka fashe da kuka, gidan sai ya koma kaman inda akayi mutuwa.
"Yanzu tafiya zakiyi ki barmu?.." Inji Zainabu tafada cikin kuka sosai, ameera share mata hawaye tayi hannun ta sai karma yake saboda rashin kuzari
"Ki bar kuka..muna tare insha Allah..." Kuka ya ci karfin ta, cikin kuka hinde tace
"Insha Allah bazai sakekiba..." Ameera girgiza mata kai tayi
"Nafison ya sakeni...son da nakeyi mashi bazai sani zaman yar kallo gidan mijina ba...nasan nima zan samu inda zan zama tauraruwa..." Tafada tana Dan goge hawaye dake gangarowa idonta,
"Dan Allah yanzu karfe nawa?.." Ta tambayesu, da sauri daya daga cikin yaran hinde ta fita don tambayan time cos ba agogo garesuba, baa dadeba tadawo
"Ance shabiyu da rabi.." Ta fada masu
"Allah yasa kar ya manta dani.,..I want to go home..." Tafada cikin sanyin murya
Kallon Zainabu tayi
"Ki dauko wayana da sauran kudin nan.." Da sauri ta shiga ciki, baa dadabe ta dawo da kudin da wayan, mikawa ameera tayi,
"Ki kidayasu.." Ta fada mata batare data amshi kudin ba,
"Saura dubu Dari da uku.." Ta fada mata bayan ta counting, amsan kudin tayi ta mikawa hinde
"Ki rikesu..ki fara wata yar Sana'a.." Sabon kuka hinde ta fara tana cewa
"Ai baki tafiba...ki rikesu har sai zaki tafi..." Kai ameera ta girgiza mata
"Aa ki rikesu..nasan bazan dade ba zan tafi..." Hinde amsan kudin tayi
"Ballomin sim card dina.." Tafadawa Zainabu, ba musu ta ballo mata
"Ki je ki sayo layin ki saka..nabaki wayan..." Tafadawa Zainabu
"Wayyo ni banason wayan..karki tafi..." Tafada cikin kuka sosai
"Dalla kije ki sayo sim.." Ta daka mata tsawa kaman ba ita take kuke few seconds back ba. Ahankali Zainabu ta mike tare da amsan kudi hannun hinde Sannan ta fita, itama ameera mikewa tayi tashiga wanka iska sai kadata yake, tanà fitowa ta shirya cikin daya daga cikin kayanda Salem ya ajiye mata, kallon ta hinde tayi
"Tunda kilan yau ki tafi gida.. Ki saka wannan jallabiya mai kyau mana..."
"Aa...cikin wannan kayan zanje gida.." Tafada tana kwantawa .

💛💙💜💚❤
Chapter 63 · 0% Book details