← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 94

Sashe 10

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salem kallon Abdul dake ta goge mashi hanci yayi yace
" take me to the hospital " kai kawai ya daga mashi don kunyan hada ido da Salem yake,
Cikin mota suka koma Abdul yafara tuki shi kuma Salem har lokacin hannunshi rike da cotton wool a hancinshi cos jinin ba bar zuba ba, Abdul dan kallonshi yayi
"Sir ka kwantar da kanka baya kadan" babu musu ya kwantar da kanshi baya.

Free hand dinshi yasaka cikin aljihunshi ya dauko wayanshi, wata number da aka rubuta Nigeria head of NGO yayi dialling, cikin kankanin lokaci akayi picking tare dacewa
"Sir..good afternoon.. How is your holidays"
"Fine" kawai Salem ya amsa atakaice sannan yacigaba dacewa
"Ka turo min Pictures da details na yan northern NGO"
"Sir yaushe kake bukatanshi?"
"Right now" yana kaiwa nan ya katse wayan shi, tare da lumshe idanuwanshi,
"Allah nasan kanason in koyawa yarinyan nan hankali... Don nasan haduwata da ita ba coincidence bane destiny ne" yafada cikin ranshi.

Suna zuwa hospital aka nubashi doc yace abinda ya sameshi ya zo mashi unexpected ne shiyasa yake bleeding, ice block aka sa agaban goshinshi for a moment jinin ya tsaya sannan suka bashi magunguna.

Suna kan hanyan dawowa emails suka shigo mashi, bai budeba har suka isa gida. Suna zuwa gida ya dauki makeup remover ya goge fuskanshi nan ya kara ganin hannun ameera kwance kan fuskanshi, wayan shi ya dauka ya dauki photon fuskanshi ya turawa Khalid nan take Khalid ya kirashi
"Guy meye wannan?"
"Same yarinyan nan ta mareni..."
"What... Karshen mari kenan... She really have to be taught an unforgettable lessons.. If you are not doing anything kawai ka barni in sa aiyi maganinta.." Ahankali Salem yace
"I have a plan... Zanbi shawaran ka..." Nan ya kwace abinda yayi niyyan yi ya gayawa Khalid, shewa kawai Khalid yayi yana cewa
"Best ko shaidan zai jinjina maka.."
"Ai friend nasan ba haka nan Allah yake ta hada ni daita ba...yanason in koyamata rayuwa..and am not let him down.." Cikin daria Khalid yace
"Yanzu zaka hakura da taxi driving ko?" Shuru Salem yayi for a moment kafin yace
"No.." Cikin zolaya Khalid ya kara cewa
"Haba ango gashi zakayi aure?" Salem katse wayan shi yayi ya dauki iPad dinshi ya ya bude emails dinshi.

Nan ya ga emails da shugaban NGO na Nigeria ya tura mashi,hotuna ya fara kallon don tantance dad ameera, yana cikin dubawa yaga alh umar Adam gezawa
"Yes wannan shine Wanda na ganin gidan su wannan shaidaniyan yarinyan" yafada wa kanshi, budewa yayi yafara karanta details dinshi, Ashe shine head na Kano zone,
" mere state head shine yarka take yanda ta gandama kaman yar Aliko dangote..let's see what happens... " wayanshi ya dauka ya kara kiran head na Nigeria, mutumin na picking yace mashi
"Terminate umar Adam gezawa's appointment... In yayi complain ka bashi details din da zansa secretary dina ta turo maka...ka gaya mashi ina Kano Kuma gidana nada GPS so yayi searching location dina..am sure motnashi yana da navigation"
"Yes sir " kawai mutum ya fada sannan Salem yayi hanging off.
Mikewa yayi yana cewa
"Am going to enjoy this" bathroom yashiga ya dauro alwallah sannan ya fito falo, yana shiga Abdul dake zaune yasha jinin jikinshi , ahankali Abdul ya daga kai ya kalli fuskan Salem, yaga gefen fuskanshi jajur kauda kanshi yayi, kallon shi Salem yayi
"Alh Abdul let's go to masjid" yayi maganan kaman babu abinda ke damunshi, Kallonshi Abdul yayi
"Sir am very sorry.. Ni na kawo silly idea dake jamaka wulakanci...dan Allah in ranka bazai baciba mu bar wannan hunting..." Karasaba Salem ya katseshi dacewa
"Tausayamin kake?..to for your information banason self pity sannan bani bane abin tausayi..wannan shegiyar yarinyan ce abin tausayi...kuma kaga wannan quest din yanzu muka farata don ya koyamin abubuwa da dama and most especially ya koyamin ba duk abu mai kyalli keda kyauba wato not all that glitter is gold..ka ga tafiya ta masjid" ya fita ya bar Abdul nan zaune, yana fita Abdul yabi bayan shi da sauri.

💛💙💚💜❤💜❤💛

"Mami kin san abinda ya faru wajen aikina yau?" Tawa ta tambayi mamanta, Matan girgiza kanta tayi sannan tace
"Ya zaayi in sani tunda ba wurin aikimki nakeba" Matan ta amsa mata da yarensu itakuma tawa tana magana da hausa kasancewan tanajin yarensu Amman bata Iya yinshi itakuma Maman bata Iya hausaba sosai, tawa ta cigaba dacewa
"Mami wata yarinyce ta mari wani babban mutum a gaban restaurant dinmu..wai dan ya dan gogi motanta da taxi dinshi... Wallahi mami mutum saida jini ya fita a hancinshi... Ni kuma nayita zagin yarinyan...." Da sauri mami ta katseta dacewa
"Kini...meye ruwan ki ?..kinason ki ja manako?" Dan turo baki tayi
"Mami mutum zai girme brother tajudeen fa..."
"Ina ruwanki koya girmi babanki...please karki jamana matsala... Kinga ta abinci muke ..." Ahankali tawa tace
"Yes mami.. Gobe zan saya maki inhaler ki don madam ta cire daribiyu cikin kudin aikina don na sayawa mitumin da aka Mara cotton wool... Kuma mami cotton wool din ashirin na tsaya Amman Dan zalunci ta cire min Dari biyu" ahankali Matan tace
"Naji Allah ya saka maki..Amman karki kara shiga abinda ba ruwanki"
"Yes mami" tafada sannan ta mike ta sauke abinci dake kan stove cikin Dan karamin tukunya ta zubawa mami sannan ta dauki mafici tana hurawa mami suna labari kaman yanda suka saba.

💙💚💜💛❤💚💛❤

Aranar da ameera ta mari Salem taje office din babanta take bashi labarin abinda yafaru da kuma yanda ta maka mashi mari, dad dinta jinjina mata yayi yana cewa
"That's daddy's angel" wuri ta samu ta zauna acikin daya daga cikin wasu relaxing sofa dake office din dad, sannan ta kurawa photo Salem da dad dinta dake manne jikin bango. Da alaman Salem baisan ana daukanshi photon ba Amman still he's looking breathtaking. Kurawa photo ido tayi tana tunanin
"Wannan mijin mai rabone" tafada tana lumshe idanuwanta

💚❤💛💜💙
ZAKISAN KONI WAYE
💙💚❤💛💜
®zuwairat(ummu maryam)

1⃣4⃣

Sai tunani take tana cewa
"Duk wacce Allah ya zaba amatsayin matan wannan bawan Allah ta huta...imagine being married to the most handsome and the richest guy in africa...kam kome kakeso a hannunka..ka hau the latest car...ka saka the latest version of clothes and kaci abinci daga the best cook in Nigeria sannan ka zauna in the best house Kuma ka maida kasashen waje kaman zuwa toilet..." Tana cikin tunanin wata zuciya tace mata
"Ameera ki farka daga mafarkin da kike...don sam baki da chance... Kilan bazaki taba ganin shi ba har ki mutu" bakinta ta tabe tare da gyara kwaciyanta, sai dab da magrub suka koma gida, motan dad dinta gaba nata bayan nashi.

Bayan sun gama dinner wayan dad yayi ringing, yana ganin mai kira ya gwalo idanuwanshi tare dacewa
"Allah ya sa lafia.." Yafada yana picking wayanshi
"Hello sir..good evening.." Shuru dad yayi yana sauraron abinda oganshi yake cewawa sannan yace
"Sir ban bude emails dinava " mutum magana yayi kafin dad yace
"OK sir ..bari in duba emails din" sannan ya kashe wayan.
Ameera ya kira ta dauko mashi laptop dinshi, emails dinshi yafara dubawa, nanfa yaga takardan sallama
"inna lillahi waina ilaihi rajuun..." Ya fara maimaitawa da karfi, mom da ameera sai affan suka nufeshi da tension,
"Lafiya?" Ko wannensu ke tambayanshi.. Amman
"Inna lillahi.." Kawai yake ta maimaitawa... Da kyar ya samu cewa
An koreshi daga aikinshi, ko waccensu salati ta saki, ameera kam hannu ta dora bisa kai tana kuka. Mom kam neman hawaye tayi tarasa, shikam affan kallonsu kawai yake dukda yasan rashin aiki matsalane, hannu dad na rawa ya dauki wayanshi yayi dialing number oganshi, bayan ringing kaman biyar ya amsa
"Me nayi kuka yimin haka...meye laifina?...ple..." Bai gamaba mutum ya katseshi dacewa
"Calm down.. Sir Salem ne ya bada umarni...kuma yace yana kano..so zansa secretary dina ya turo maka details sai kayi amfani da car navigation ka nemi gidan shi..." Da sauri dad ameera yace
"My car don't have a navigation... "
"OK don't worry.. Bari in kirashi..in ya bada address dinshi zan baka sai ka sameshi"
"Thank you... Thank you.." Kawai dad ameera keta maimaitawa ayayinda zufa ke ta keto mashi.

💜💛❤❤💚💙

Salem kam bayan sallan ishai ya zauna yana jiran abinda zai biyo baya, bai Dade da zamaba wayanshi yafa ringing, yana dubawa yaga Nigeria head ne ke kiran shi, ajiye wayan yayi bhai dagaba, saida yayi mashi kusan 3 miss call sannan ya daga tare dacewa
"Ya akayi kuma?" Ahankali mutum yace
"Sir..wannan alh umar Adam din yace motan shi baida navigation.. So sir in babu stress ka dan bani address dinka..." Bai karasaba Salem ya katseshi dacewa
"Listen to me...bani da lokacin raba address dina...in bashi da navigation then ya samo ma kanshi sabon aiki...and tell him zan bar Kano jibi..in har na bar Kano kar ya nemeni..." Kas ya katse wayan shi yana murmushi mugunta..Abdul dake zaune a falon yanajin abinda Salem ke cewa yasan ba abu arziki bane.

Abangaren dad ameera kam oganshi na gaya mashi yanda sukayi da Salem ya dora hannu bisa kai yanacewa
"Ina zan samu kudin siyan mota mai navigation... OK bari inkira kB mai motoci.." Yafada kaman wani Mara hankali, kiran kB yayi bayan ya daga yake gaya mashi ko suna da babban mota mai navigation, mutum yace da akwai, dad ameera ya tambayeshi nawa, kB yace 70millions,baki dad ameera ya bude kafin yace
"KB in na kawo jeep dina dana Hajiya sai murano ameera nawa zaka saya?" Daga dayan bangaren kB yace
"Gaskiya alh..tunda Kaine zan sayi jeep dinka dana hajiya million 12 each sannan na ameera million 2..."
"Haba kB wurinkafa nasayi nawa dana Hajiya million 20 each..."
"To alh ai kasuwane..." dad yaga ko an sayi dukkan motaccin gidan bazai saya mashi motan da yake bukata ba,
"To kB don Allah alfarma nake nema...zan baka million 1 ka aramin motan...gobe kawai zanyi amfani dashi sai in maido maka..." Shuru kB yayi kaman mai tunanin wani Abu sannan yace
"To alh Amman million 2 zaka bada..kasan in ba kaiba babu Wanda zan yarda inyiwa wannan alfarman..." Ba musu dad ameera ya amince.
Chapter 10 · 0% Book details