← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 94

Sashe 87

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abangaren Khalid kam suma anyi bincike amma sun gano yarinyan ta taba aure,
"Yanzu son yarinyan data taba aure zaka aura as a first wife?.." Shine tambayan da mom dinshi tayi mashi, ahankali Khalid yace
"Mom..ita nakeso....kuma duk karyan mutane ne...bata taba aureba...."
"AI ba hanaka zanyi ba tunda ba haramun bane...am happy zakayi aure" Tafada cikin jin dadi.

Bayan sati daya uncles din Khalid da wasu manyan mutane sukaje gidan su Ameera Neman aurenta, kuma da kayan saka rana sukazo, Dad dadi sosai yaji don yasan yanzu yarshi zatayi aure, anci ansha Sannan aka sa sati 8 that's two months.

Tunda daga ranan aka dauko mai koyawa Ameera abinci da sauran aikace2 gida. Ana sauran 7 weeks Khalid ya shigo Kano, ba karamin kyau yayiba, itama tayi kyau sosai saboda gyaran jikin da anty Sadiya ta fara yi mata, kasa daina kallon ta yayi, kanta kasa Sai wasa take da fingers,
"Babyna haduwanki bai faduwa..." Yafada yana murmushi, itama murmushi tayi,
"Do you have any special events in mind?.." Ya tambayeta, ahankali ta girgiza mashi kai
"So ki yarda in sa ashirya all the events?.." Ya sake tambayan ta, ahankali ta daga mashi kai, kallon ta yayi
"Baby wannan kunyan fah?...tunda nazo baki daga kai kika kalleni ba...what have I done wrong.." Ya tambayeta kaman zaiyi kuka
"Nothing..."
"Then pls look at me..." Yafada cikin whisper, daga kanta tayi suka hada ido, ido daya ya kashe mata, tayi murmushi tare da dauke kanta,
"Angel INA kikeso mu zauna?... I have two duplexes in abuja....two in yola Sai one a banana island lagos..." Ameera shuru tayi bata ce komai ba don babu abinda take tunawa kaman ya kusa ganin nakedness dinta,
"Angel say something.."
"Duk inda kakeso..." Ta fada mashi
"Ko in sayi gida nan Kano?..." Kallon tayi ta saki murmushi, Dariya yayi
"Baki idaba yarinya... You want to be close to mommy..." Ya fada yana dariya, Itama Dariya tayi don ya gano ta,
"Ai bance mu zauna nan bako..." Ta fada cikin shagwaba, Dariya ya karayi yana cewa
"sayi gida nan mu dinga sauka in Mun zo Kano..." Daga kai tayi ta harareshi
"Ga gidanmu?..." Baice komai ba ya sa hannu cikin aljihunshi ya dauko wani small jewelry box, ya bude, wani white ring ne mai dauke da diamond stone samanshi, hannun ta ya kama ya sa mata Sannan ya Kara dauko wani envelope ya saka cikin palm dinta, kallon zoben tayi ta saki murmushi cos ba karamin kyau yayi wa hannun ta ba. Sun dade suna hira batare data bude envelope dinba, sallama yayi mata ya kuma shaida mata yanzu saidai su dinga waya cos he will be very busy saboda wedding arrangements.

Tana komawa sama taga credit card ne da pin number kiranshi tayi ta tambayeshi ATM din na meye ya shaida mata ta zari any amount da take bukata for her friends anko.

Duk yanmatan dake yiwa Ameera habaici saida suka dawo suka bata hakuri don ta dama dasu, batayi masu wulakanci ba aka shiga harkoki dasu, zeenat kam bataji dadi abinda Ameera tayiwa sultan ba amma she takes everything in good faith.

Ba karamin gyara Ameera take shaba don abubuwan is to much, jikin ta ya kara kyau fiye da yanda kuke tunani, kullum cikin waya suke da Khalid.

Ana sauran sati four biki aka kawo lefenta, fadin kyau da yawan kayan is a waste of time and strength just imagine lefen yayan governor, kuma civilised one don mom din Khalid wise woman ce ta gidan karshe, akwati 18 aka kawo 12 lv sai 6 gucci traveling bag da mota daya sai kujeran makka 3, mom kam abun tsoro ya bata dad baki har kunne saboda jin dadi, duk Wanda ya zo ganin lefen Sai ya koma da baki bude, aranan Ameera da Khalid suna waya take shaida mashi kayan sunyi yawa, cewa yayi bai ma gansuba Kuma ta dauka duk yawan kayan can never be compired to her beauty.

Abangaren Salem kam duk ya damu ba don komai ba sai yanda Khalid yaki amsan komai daga hannun shi, duk abinda ya bashi Sai ya ki amsa yana cewa bayason rai Ameera ya baci, ko yanzu suna zaune da tawa tawa suna kallo shi kuma yana waya da Khalid,
"Guy gaskiya abubuwan da kakeyi is touching me... Ya zakayi min haka...we grow up together... Amma zakayi aure ka ki amince wa da komai daga gareni..." Inji Salem daga chan bangaren Khalid yace
"Just understand....banason abinda zaisa Ameera bacin rai...remember she almost dump me because of you..." Gyara zama Salem yayi Sannan yace
"Yanzu guy mace zata rabamu da kai kenan?..."
"Haba wake maganan rabuwa...it's just for the main time..." Inji Khalid,
"Ba komai...we will be coming back next week..." Inji Salem yana rike hannun tawa, da sauri Khalid yace
"I beg you in the precious names of Allah... Don't come back now... Wait until five weeks for now..." Ido Salem ya zaro
"Hope this is not what am thinking?..."
"Yes it is... In ka dawo su first lady da first love zasuyi mamakin rashin ganin ka a wedding dina...so pls just wait till after my wedding..."
"Yanzu Khalid are you saying I should not be present at your wedding?.." Ya tambayeshi afusace, ahankali Khalid yace
"am sorry but yes...." Salem bai Kara cewa komai na ya katse wayanshi tare da mikewa daga inda yake zaune kusa da Tawakaltu, da sauri ta bi bayan shi,
"What's wrong?..." Ta tambayeshi,
"Nothing..." Ya fada mata atakaice, rike mashi hannun tayi ya fixge
"I said nothing!...." Ya daka mata tsawa, da sauri ta ja baya, tana kallon shi, gaba yayi tabi bayan shi Ahankali, afusace ya juyo ya kalleta fuskan shi Sam babu walwala
"See just go back...right now am upset and I don't want to be disturbed..." Kuka tafarayi tana cewa
"So am disturbing you?...to shikenan... Let me keep my distance..." Tafada tana juyawa Ahankali tare da dafa maranta, Salem tsaya kallon ta yayi har ta zaunasai yaji bai kyauta ba cos ba ita tayi mashi laifi ba amma he's taking it on her, komawa yayi wajenta,
"Princess am sorry... Kawai rainane a bace...kiyi hakuri kinji?"... Kai ta daga mashi, hannu yasa ya goge mata hawayenta tare da jawota jikinshi.

Ahankali lokacin ke tafiya inda Khalid ya kawowa Ameera list na events da zasuyi for a whole week, kuma ko wanne rana nada dress code, ana sauran two weeks Ameera ta rabawa friends dinta iv. Yanmatan kam shirye suke don sunji abun nayine.
Gyaran da anty Sadiya takewa Ameera yafi na wancan lokacin cos ta samu enough time and money, Sannan lefen da aka kawo ya Kara nunawa cewa ba anyhow mutum zata aura ba haka yasa kullum da abinda take bata, Sannan yanzu ba laifi Ameera ta iya at least not less than 15 variety of food
Duk Wanda yaga pre wedding pics dinsu Sai yace Ameera da Khalid sis and bro ne saboda yanayin hasken su da pointed noise,guys Sai zolayan Khalid suke suna cewa ya fi abokinshi iya zabe, cikin ranshi kam saidai yace bakusan shi ya fara aurenta ba.

Yau sauran ten days saurin aure, da yamma around 5pm wani moving van ya shigo gidan, mom fitowa tayi tana kallon katon van din Sai mamaki van din take don sai gobe kayan Ameera suke isowa, driver ya fito daga cikin van tare da yaranshi, kallon mom dake ta mamaki yayi Sannan yace
"Sakone daga sultan..." Baki mom ta bude da aka fara sauke kayan, complete set ne na kujera da da gado, exactly irin na zeenat, mom komawa ciki tayi ta fadawa Ameera abinda dake faruwa, kiran sultan tayi amma baiyi picking ba..

Ana sauran nine days daurin aure governor na Kano ya amshe dukkan hotel da quest house saboda baki kuma baban Khalid babban abokinshi ne.
Tun sauran 8 days gayu suka shika garin kano, duk inda kika ratsa handsome guys kake gani daman Khalid yafi Salem hulda da guys kuma yafi shi shiga social life.

Umman da abban Salem Sai kiranshi suke suna why bai dawo ba har zaayi bikin amininshi, karya kawai yayi masu kan he's seriously sick, ammi kam cewa take
"Kuyi adua ya gane hanyar gidansu tunda ya auro mayu...kilan tana chan tana zukeshi...."

Yau aka fara events, inda kunshi aka fara dashi, cikin katon hall dukkan yanmata ne kawai Sai tsantsara masu hyena decor ake. Ga kidi yana tashi.

The following day akayi kauyawa party a gezawa gidan granny din Ameera, shigan original yan kauye akayi, Khalid kam kasa daina kallon Ameera she was looking extra stunning.
Sai Fulani night inda ango da amarya tare da friends sukayi shigan Fulani, followed by Arabian nights Sai mothers night, yawancin Matan governor sun hallaci wannan taron.
Sai picnics,

Atakaice ranar Friday akayi daurin auren Ameera da Khalid kan sadakin dubu Dari, daurin auren ya samu manyan mutanen kasa, abinka da dan governor, Khalid kam bakinshi bai rufuwa saboda
Farin ciki, bayan daurin aure aka wuce reception inda amarya ta sha silver flowy gown daga companin varsace. Khalid ma ya sanyan suit silver mai dan sheki kaman an zuba mashi ruwa.

😳😳😳😳 surprised?....don't be...am full of surprises💃🤣
💙💚💛💜❤
ZAKISAN KONI WAYE.
❤💜💛💙💚

®zuwairat(ummu Maryam)

8⃣0⃣

*My Habeeba I don't know how to show my appreciation... But I want you to know I love you, Allah ya bar kauna...* 💋💋💋
Chapter 87 · 0% Book details