← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 94

Sashe 66

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Salem na sauka down stairs ya nufi dakin da take gabanshi sai faduwa take don gani yake zata kara ci mashi uwa. Ahankali ya bude ya gangeta kwance kudundune cikin gyalen dake jikin ta, tafiya yayi a ahankali ya karasa wurin ta, yaga tana bacci, gabanta ya koma cima ya kwanta nan kasa kusa daita, fuskanshi daidai nata sai shakan numfashin ta yake, kallon yanda iduwanta suka kumbura yayi, kuma dukda tana bacci bata bar shessheka ba,
"Am sorry... Please" yafada kasan makoshinshi, ahankali ta bude idanuwanta da sukayi mata nauyi tana ganin shi tayi saurin mikewa ta matsa baya, shima mikewa yayi zaune yana kallonta
"Baby am sorry...this is not us...we should be happy... Yau ya kamata..." Bai idaba ta katseshi dacewa
"Yau yakamata ka dauke pride dina don kaji dadi sakina ko?...you will not get what you wanted... " ta fada ta sake sabon kuka, kai kawai Salem ya girgiza
"I have never slept with any woman... You are the first woman that sees my nakedness.. Wallahi..." Bai idaba ta bar wurin ta bude kofa ta koma falo, gani tayi an kawata wurin dinning table ga abinci anjera Sannan ga wani candlelight a wajen looking so romantic. Zama tayi Salem ya biyota ya zauna nan kasa kusa daita, baya ta juya mashi ya kara komawa gabanta
"Baby..please let's eat..." Yafada gwanin ban tausayi, banza tayi dashi
"Please...'" Still batayi responding dinshi ba, mikewa yayi ya rike mata hannu, buge mashi hannu tayi da karfi har ya saki kara yana rike wrist dinshi data buga don ba kadan yaji zafin bugunba, dan shaking hannu yayi ya saki kara saboda azaban da hannun keyi mashi, tawa kam ko daga kai batayiba balle ta ce mashi sannu,
"Baby kin karya min hannu..." Yafada yana cizon lips dinshi saboda kafin da hannun shi keyi mashi, batace mashi uffan ba tacigaba da kukanta, kara shaking hannun yayi ya tabbatar yaji da gaske wrist dinshi zafi, kuka yafarayi kaman yaro yana cewa
"I don't deserve the punishments.. Wallahi abinda na fada maki is nothing but the truth.. Yanzu nasan ba sona kikeba..wallahi in da nasan haka kike da taurin zuciya da ban...." Sai kuma yayi shuru, itama tawa mikewa tayi
"Da baka aureni bako?... Complete it...nima danasan haka kake da ban aureka...kuma it's not late...kana Iya maidani gidanmu... I hate you with passion... I don't care if you die...ban zama da kai..." Salem shuru yayi yana kallon ta
"Anya kece Tawakaltu Dana aura?...my Tawakaltu is nice and considerate...she's understanding..." Baki ta tabe
"Makaryaci kawai..." Ta fada Sannan ta koma kasa ta zauna ta cigaba da kuka ko bata gajiya da kukane oho. Salem tsayawa yayi yana kallon ta dama haka quite people ke da masifa, hmm lallai the devil you know is far more better than the angel you don't know, tsayawa yayi zuciyanshi na up and down Kuma hannun shi sai zugi takeyi mashi. Bai Kara cewa komaiba ya koma kan wani kujera dake falon ya zauna hannun shi daya rike da wrist dinshi don ba karamin zafi yakeji ba, hannu yasa cikin aljihunshi ya fiddo wayan shi ya kira wani abokinshi.
He can't believe this is happening.
Bayan kaman hour daya akayi ringing doorbell Ahankali yaje ya bude kofa har lokacin tawa na zauna kanta cikin kwaiwanta sai ajiyan zuciya take, wani handsome looking baturene ya shigo, gaisawa sukayi Salem ya nuna mashi hannun shi, wani briefcase dayazo dashi ya bude ya dauko wani Abu yana Dan danna hannun Salem dashi ihu Salem ya saki
"I think is fractured..." Doc. Yace, Salem Dan daga kanshi yayi ya kalli tawa ko zata daga kanta sai yaga ko gizau batayi ba, daure mashi hannun doc yayi sai dan ihu Salem yake, tawa mikewa tayi ta shige bedroom abinta Salem ya bi bayanta da kallo, doc na gamawa sukayi sallama, Ahankali ya mike da abun daure karaya hannun shi, still dakin da tawa take ya shiga, ya ganta kwance kan gado, wurin ta yaje ya zauna bakin gadon, yadan matsa kusa daita
"Please ko tea ne kisha..." Ya fada mata sounding so heart broken, banza tayi dashi,
"Please.. Kawai don't take me as your husband.. Kawai take me as a friend who cares for your wellbeing... Muje kici abinci..." Bata kalleshi ba balle ta amsa mashi. Kara mikewa tayi
"Leave me alone..stop following me.." Ta fada tana kara fita daga dakin,
"Ikon Allah.." Salem yafada yana binta falo, shi kanshi yana mamakin irin son da yake yi mata, yasan nobody tries him this way.

,,ameera kam tana ganin tafiya taki ci taki cinyewa tasan ba gidan Salem zaa kaitaba, Sannan tasan ba Kano zaa kaita ba, shuru tayi tana adua cikin ranta, bacci kawai take ji ga juwa tana gani.
Chapter 66 · 0% Book details