← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 94

Sashe 38

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salem na zuwa part din Abba ya zauna yana haki saboda yanda yayi tafiyan cikin sauri, saida numfashin sa ya daidaita sannan yace
"Abba.. Na gane waye grandpa dinta," da sauri Abba yace
"Really?.. Waye?"
"Can you believe it?.. Oba sadiku of kwara state ne grandpa dinta," kallon mamaki Abba yafara yiwa Salem
"Son are sure of what you are saying.."
"Yes Abba.. Investigation nasa aka yimin" Abba gyara zama yayi
"Wane investigation?" Sai lokacin Salem ya bawa Abba labarin da tawa ta bashi, baki Abba yabude
"Son shine kake cewa har talakawa ce?.. Ai sadikus linage are filty rich..." Dan murmushi Salem yayi
"Ai tawa a restaurant take saida abinci.." Abba shuru yayi for a moment sannan yace
"Ai abinda uwar yarinyan tayi bata kyauta ba..whatever parents come first... I think nasan lokacin da abin yafaru..I was the GCFR a lokacin..."
"To yanzu Abba meye abinyi?.." Salem ya tambayi Abba, Abba shuru yayi yana tunanin abinyi, bayan kaman 40 seconds yace
"Zan yiwa obasonjo magana sai ya rakani muje wurin oba.."
"To Abba inkuje ..." Shuru yayi sannan ya Dan doki kanshi sannan yace
"Abba am confused.. Kasan iyaye maza suke babanta ya kamata su bani ita..." Dariya Abba yayi
"I know.. Kasan am sure yarinya da mamanta basu gidan oba...so zamu shirya tsakanin ta da iyayenta..hakan zaisa mu gane whereabout dinsu"
"Gaskiya hakan yayi... Amma.." Sai kuma yayi shuru,
"Amma me?" Abba ya tambayeshi, yana Dan shafa keyanshi kaman mai jin kunya yace
"It will take a long time.." Dariya Abba yayi sosai, cikin zolaya irin na iyayen zamani yace
"Ka matsu ne?" Salem sunkuyar da kanshi kasa yayi yan dariya,
"Ai kayi kokari...35 ba wasa bane..in badai kana..." Da sauri Salem ya girgiza mashi kai
"Never.. Abba" yafada kanshi kasa, saida kunyan tadan sakeshi sannan yace
"Amma Abba there is one more problem.."
"OK..na meye?" Ahankali Salem yafara cewa
"Abba maminta bata son hausawa" dariya Abba yakarayi
"Me hausawa sukayi mata"
"Wai Abba cewa take basu da rike aure..." Dariya Salem yafara yana
cewa
"Yau aure gobe babu" yafada a irin muryan mami, Abba dariya yayi.
"In-law to be dinka kake yiwa shakiyanci ko..babu ruwana..amma maganan ta ba karya bane..saidai ba duka aka taru aka zama dayaba.. Besides we are not hausas"
"Ai Abba dukkan mu Hausa ake cemana"
"To ba matsala bane, zamu nuna masu muma muna da rikon aure"
"Insha Allah" mikewa yayi ahankali,
"Abba inason in goma gidana na nan" kai Abba ya girgiza mashi
"Kayi zamanka nan tukunna"
"OK" yafada amma badon yasoba, donshi mutum ne maison privacy, har ya kai bakin kofa Abba yace.
"Mijin Yoruba..ka kokarta kafara cin abinci don kar ayi tunanin wani ciwo gareka" murmushi jin dadi Salem yayi
"Insha Allah Abba" sannan yafita, yana fita yaga majed ya taho da wani work phone
"Sir wani nason magana da kai" fuska daure Salem yace.
"Waye?"
"Nigeria head of NGO "
"Baka fada mashi ina holiday ba?"
" Sir na fada mashi..amma yace is about family din matanka...." Bai karasa ba Salem ya tureshi yana juyawa yana kallon kofa part din Abba don ya tabbatar babu Wanda yaji abinda majed
"Kana haukane?.. Don't you know secrecy?..Dalla bani wayan.." Yafada yana kwace wayan daga hannun majed, yana amsa waya na tsikewa, fuskanshi murtuke yayi dialing number, mutumin na picking yace
"Alh ya akayi ne?" Daga chan bangaren akace
"Sir wallahi iyalen alh umar Adam gezawa ne suka addabeni..wallahi yanzu nan Matan har kuka tayimin awaya wai tunda ameera ta bar gida basu ji daga garetaba..uwar har cewa tayi tana da feeling something bad is happening to her.."
"Indeed" Salem yafada kasan makoshin shi sannan yacigaba da sauraren Abinda ake fada mashi
"Sunce basu da contact dinka shine suke son in sada su da kai..." Sai yayi shuru, Dan karamin tsaki yaja
"Wannan long story... Kawai say some body want to speak to me..is better... Connect me to them" yafada lokacin da ya karasa kofan part dinshi, bude mashi kofa akayi ya shiga ya samu wani kujera ya zauna ya dora kafa daya kan daya lokacin wayan nata ringing, muryan dad ameera yaji yayi sallama, amsawa yayi sannan yace
"Alh ya akayi ne?.." Ahankali dad ameera ya gaisheshi, ya amsa yakara cewa
"Ya akayi ne?"
"Sir kuna lafiya?"
"Lafiya.. Ko kaji rashin lafiya ta?" Da sauri dad yace
"No sir.." Ahankali yacigaba dacewa
"Ya ameera?" Yayi maganan kaman an fixgota daga bakinshi,
"Lafiya..." Bai gama magana ba yaji kaman an amshe wayan, saiji yayi ance
"Hello uncle.." Cire wayan yayi daga kunnenshi ya kalli wayan sannan ya maidata kunnenshi
"Uncle..." Ahankali Salem yace
"Sir who is this?"
"Sir nine affan...sir please am missing anty ameera... Please I want to talk to her..." Yana kaiwa nan ya fashe da kuka, Salem sai yaji duk jikinshi ya mutu, affan yacigaba dacewa
"Mom..is also crying every day.. Please sir..I want to see my anty.. Ameera..." Salem lumshe idanuwa yayi da affan yace mom dinsu tana kuka kullum, yasan hannunka baya rubewa ya yarda
"What the fuck have been doing keeping people's child.. Ina ruwana da rayuwan ta..." Ya fada cikin ranshi
"No don't say that... She deserve to be taught a lesson of life time.. .." Ji yayi affan nacewa
"Uncle are you there?.." Da sauri Salem yace
"Yes...but am not hearing what you are saying... Because you are crying... Guys don't cry..right?" Yafada kaman ba shiba, kallon shi nayi nace kaima kwananka shida babu ranar da baka kuka
"Yes sir " affan ya amsa mashi
"Don't worry you will talk to your ANTY...but please ka yimin hakuri sai gobe cos ina yola itakuma tana abuja..." Da sauri affan yace
"Yeeeeee...thank you sir..."
"No p...and tell mom not to worry gobe in na koma gida zan kai mata waya..,"
"Sir..daman bata da waya?" Salem dariya yayi
"Ai bata fadamin bata da wayaba so ban saniba...that means bata damu dakuba" yafada yana shuumin murmushi, ahankali affan yace
"Sir daman haka take but we can't do without her..."
"No matsala.. Now tell me ya karatu..."
"Fine..sir...na fadawa class mates dina sir Salem Yusuf sulaiman ne mijin anty ameeranmu sunce karya nake" dariya Salem yayi
"Don't worry..in nazo Kano zan saya maka iPad 32GB sai musha selfie dakai sai ka samu evidence..."
"Yeee...thanks... You are the best uncle in the world.."
"Am not.." Yafada cikin ranshi, affan yacigaba dacewa
"Anty ameera is lucky.." Dariya Salem yayi
"No she's not.." Kara fada cikin ranshi
"Affan baka da wayane?" Salem ya tambayeshi
"Eh..dad yace sai na gama primary school..."
"We're in 21st century.. Ka fada mashi nace ya daya maka waya kafin in kawo maka iPad..,"
"Dad kajiko?" Yaji affan nacewa da alaman wayan is on speaker, baki ya tabe sannan yayi ban kwana da affan, ya kashe waya ya kira majed yayi
"Ina wannan CCTV recorder danace ka daukomin daga wancan gidan?"
"Sir na mantashi cikin mota a abj..." Tsoki yaja tare dacewa
"Incompetent" sannan ya katse wayan.

Majed kallon Abdul yayi
"Wai sir yana da aurene?" Ya tambayi Abdul, Abdul dariya yayi sannan yace
"Ai yarinyan daka shararawa mari matarsa ce..."
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!!!" Majed ya ding maimaitawa, saida shock din ya sake shi sannan yace
"Amma meyasa sir ya kaita wannan wurin... Kuma ranar da na mareta baice komaiba?" Ahankali Abdul yabawa su majed labarin abinda ya faru da irin zagin da ameera tayiwa Salem har zuwa kan iyayenshi
"Lallai...no wonder ranar danaje take cemin bata manta abinda nayi mata ba...kuma wai zata rama when the time is right..." Inji majed daketa mamakin maganan da Abdul ya fada mashi,
"Kace mu fara yimaka kallon goodbye don babu abinda zai hanata sa sir ya koreka insu jone..." Inji isah
"Gaskiya da kyar sir ya jone da wannan yarinyan..In hakan yafaru, bazan ji dadiba...don Lucifer is better than that girl..." Inji Abdul, Jibreal kallonsu yayi yace
"Wacece yarinyan da sir keson mutuwa saboda ita?" Ya tambayi Abdul
"Yarinyan opposite din ameera ce tana da kirki sosai..sai dai ba Hausa bace..kuma ina tunanin ita sir zai aura..." Inji Abdul
"Wannan low class din?" Isa ya fada, da sauri Abdul ya fara waige2 yana cewa
"Wallahi in sir yajika...consider yourself jobless" yafada cikin muryan Salem, da sauri majed ya mike yana cewa
"I am in enough trouble already..." Yana kaiwa nan ya bar wajen, kowanne su mikewa yayi ya kama gabanshi.

Salem ji yayi kaman yaje abj yau ya sallami ameera don yasan confirm ba zama zaiyi daitaba, Amma bai da kwarin jikin da zaiyi wannan tafiyan ayau, zama yayi yana kara kiran da tawa ta kirashi daita, sayaji tana ringing da sauri ya gyara zama, jiyayi mami na
"Hello.." Da sauri ya katse wayan yana daria sannan kuma bayason ya jawa tawa fada don mami ba kadan ba wajen fada.

Wacegari da safe ya fadawa Abba da akwai wani abu important that needs his attention, Abba bai hanashi tafiya ba, wurin Umma yaje yayi mata ban kwana dukda bai wani saki daita ba sosai don yanason ya nuna mata yana matukar son tawa sannan ita tazama shaida don yasan halin family dinsu da iya shegantaka and he's not tolerating that from anyone.

Yana fitowa ya hau mota suka tafi gidanshi da pilot ya ajiye jet sannan suka wuce abuja, suna sauka gidanshi majed ya bashi CCTV recorder, falon shi ya koma ya zauna yafara kallon rayuwan ameera, dariya ya dinga yi inya ga tana tafiya zaninta na kuncewa, saida yaga draman da suka dingayi da hinde ya rike ciki kaman zai mutu,
"Kai wannan yarinyan da akwai rashin m..." Yana cikin kallo yaga inda hinde take bawa ameera shawaran tasa malami ya kira mata mijinta don ya mori jikinta,
"Village people with attitude.." Yafada kuma ya Dan ji dadin amsan ameera,
"Hmmm nasan watarana tana iya daukan shawaran ta...hinde have to go..." Haka yacigaba da kallo har yazo nan inda hinde ta badawa ameera zinari , dariya ya dinga yi, yana cewa "ga small kissable lips... Amma zagi kawai.." Yanajin sanda ameera tacewa yar hinde "zombie" ya kara tuntsure da dariya
"Kin Iya daukan photon mutum cos you are not far from the truth... Amma kema kin kusa zaman small bazawara, ,, ba yanzu ba cos you haven't learn... Saa ki daya you are not screwed.
Chapter 38 · 0% Book details