← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 94

Sashe 77

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali ta dinga tuki har takai gidansu zeenat, horn tayi maigadi ya bude gate, tana shigowa ta hangi zeenat tsaye da swiss lace dinkin riga da skirt kanta babu head, tayi mugun kyau don yanzu an fara mata gyaran amare, ameera na packing ta karaso kusa da motanta ta bude mata kofan ameera ta fito,
"Da girman kujeran ki..." Inji zeenat,
"Kedai keda girman kujeran.. Tunda kece amarya.." Ameera ta amsa mata tana dariya. Zolayan juna suka fara Sannan suka shiga ciki, wurin umma sukaje ameera ta gaidata Sannan suka koma dakin zeenat, labarin duniya suka fara har zuhr basu fitaba suna dakin, saida suka gama sallah Sannan suka fito cin lunch kasancewan mai aiki tazo kiransu, a kan dinning Umma ce zaune Sai wani cute dark guy, daka kanshi Sai ka rantse black American ne, don shi bakine amma bakin Sai sheki yake, yana sanye da armless fari da three quarter red kanshi sanye da facing cap Wanda ya maida face din baya. Kanshi kasa kuma koda su ameera suka fito bai daga kanshi ba, lokacin Umma na serving dinshi abinci, ameera na ganin shi ta saki murmushi tare da matsawa daf da zeenat Sannan tace
"Babe yaushe yaya sultan ya dawo?..." Tafada cikin whisper, Dariya zeenat tayi
"Bana fada maki zai dawoba?..." Itama ta amsa mata cikin whisper,
"Na mance ta.." Ta amsa mata ahankali suna kaiwa wurin dinning, Kara gaida Umma su biyu sukayi ta amsa amma har lokacin sultan dake cin abinci bai daga kai ba, zama sukayi Sannan ameera tace
"Yaya sultan ina wuni..."
"Lafiya..." Ya amsa atakaice batare da ya daga kanshi, ameera bataji komai ba suka fara cin abinci, zeenat kam Dan bata rai tayi, koda yake ya amsa gaisuwan ta cos mostly bai amsa gaisuwa yanmatan cewa yake they are nothing but jackass.
Ko minti biyar bai kai da fara cin abinci ba ya mike, har lokacin bai kara kallon su ameera da zeenat ba
"Ina zuwa?..." Umma ta tambayeshi, cikin wani irin cool voice yace.
"Umma am full..."
"Full din ubanka...ko spoon goma bakayiba ...amma wai am full..."
"Umma remember am an athlete...I don't eat any how...yanzu duk jikina nauyi yakemin saboda heavy food da kike duramin tun last week..." Yafada yana taba cikin shi, ameera Sai sauraron hausanshi take, don kaman ba Hausa yakeba, hausanshi har wani slant yake kaman bature, tsoki kawai Umma taja tare da girgiza kai
"Allah ya shirya ka..." Tafada, bai kara cewa komai ba ya fita daga wurin, ameera da zeenat binshi sukayi da ido cos he's looking so adorable, enjoyment is written all over him,yana fita zeenat ta fashe da Dariya
"Kardai ki bari yajiki..." Inji Umma, da sauri tayi shuru.
Suna gama lunch suka koma daki, wanka zeenat tayi suka fito don da akwai kayan da zasu sayo kasuwa, suna fitowa suka ganshi yayi relax kan wani resting chair dake cikin balcony din part dinshi, tunda suka taho ya kura masu ido yana mamakin ina zeenat ta samu balarabiya.
Kallon su yake har sukazo wucewa ta inda yake,
"Yaya na tafi kasuwa Sai na dawo..." Zeenat ta fada mashi, itakam ameera bata kara kallon inda yake ba, hannu yayiwa zeenat alaman tazo,
"Babe am coming yaya is calling me..." Ta fadawa ameera
"Ok..." Kawai tace mata. Zeenat komawa tayi wurin sultan
"Yaya gani..." Ta fada mashi bayan ta karasa wurin shi. "Who is that girl?...." Ya tambayeta yana nuna ameera data shiga motanta, muryan shi sak na turawa
"Yaya ameera ce..." Ta amsa mashi, shuru yayi kaman mai tunani,
"Ameera..." Ya fada trying to remember her
"Wacce ameera?.." Ya sake tambayan ta
"Kai yaya....Aisha diyar abokin Abba fa...." Shuru yayi still don har lokacin bai tuna taba
"Wane abokin Abba?..." Ya tambayeta sounding very inquisitive, kafa zeenat ta buga kasa
"Haba yaya...yanzu Aisha umar gezawa ka mance?... My childhood friend..." Manyan fararen idanuwanshi ya bude
"Oh....the crazy ameera... Wow...Sai yanzu na tuna...she's all grown..." Yafada yana dariya ahankali hannun shi mai dauke da designer wristwatch a bakinshi, kara kallon zeenat yayi
"Wait a minute... Ba ita bace kika cemin zatayi aure ba few months back?..."
"Eh itace..." Dan bata fuska yayi
"So she's married?..."
"No...divorced..." Kara daure fuska yayi
"Divorced?... " yafada sounding very surprised
" Wa ta aura?..." Ya sake tambayan ta
"Sir Salem..." Baki sultan ya tabe
"Waye haka?..."
"Salem Yusuf sulaiman..." Baki ya kara tabewa amma baice kalaba, yayi shuru kaman mai tunani
"Can I go?..we're running late..." Zeenat ta fada, kallon ta yayi
"Running late...kaman kuna da AP da President?... Anyway you can go.." Yafada mata.

Khalid kam suna zuwa bakin gate sukayi horning, maigadi na dubawa ya bude gate don da ganin su kasan ba mutanen banza bane, mussanman Khalid cos he looks elegant. Khalid kadai ya shiga ya fadawa mai gadi yanason ganin ameera,
"Bata dade da fitaba.." Shine amsan da maigadi ya bashi, shuru yayi kadan don mugun son ganin ta yake
"Please kasan lokacin da zata dawo?..." Ya tambayeshi,
"Rankashi dade ya zaayi insan lokacin dawowanta....ni maigadi ne..."
"Ok..." Kawai Khalid ya fada ya koma cikin mota
"Mutafi..we can come back after asar..." Ya umarce Abdul. Barin wajen sukayi.

Sai around 4 suka bar kasuwa, koda suka dawo ameera bata kara shiga ciki gidan ba, daga bakin gate ta ajiye zeenat Sannan ta wuce gida. Tana isowa su Khalid na isowa, horn tayi aka bude mata gate ta shiga shikuma Khalid ya fito daga cikin mota ya taka ya bi bayan motanta. Tana fitowa taga wani good looking guy ya nufota fuskan shi dauke da murmushi, he looks familiar amma she can point a finger at were she has seen him before. Khalid kam tunanin in wannan yarinya Salem ya samu courage din saki he's nothing but a fool who didn't know what he has until its gone, karawa yayi wajen ta tare da sallama, amsa mashi tayi fuskan ta sake,
"Ina wuni..." Ta gaidashi, Khalid shuru yayi ya kasa amsawa cos bai taba ganin mutum so beautiful har cikin voice ba, her voice was very melodious
"Lafiya lau...kin wuni lafiya?..."
"Alhamdulillah.." Ta amsa mashi atakaice. Ahankali Khalid yayi introducing kanshi gareta, ameera Dan gingina tayi da mota don she's tired and exusted,
"You are welcome... Ka zauna mana in kawo maka ruwa?..." Ta fada tana nuna mashi wasu kujeru dake cikin wani thatch canopy dake gefen compound din.
"Ok..." Ya fada ya nufi inda ta nuna mashi itakuma ta shiga cikin gidan walking so majestically.

Direct dakin mom ta shiga ta shaida mata ta dawo Sannan ta fada mata tana da visitor.

Da sauri ta shiga dakinta ta shiga bathroom ta watsa ruwa sharp2 ta fito saka blue gown da white Vail tayi sallah Sannan ta sauko downstairs ko kwalliya batayiba , perfumes kawai ta fesa, Sai sauri take don Sam batason abinda zatayi ya zama kaman wulakanci cos she have learn her lessons.
Cikin sauri tashiga kitchen ta dauko almarai milk da nestled bottle water Sai cup ta fito.
Tana fitowa Khalid ya kalli yanda dan gashin kanta daya bayyana ke sheki
"Beautiful angel..." Ya fada kasan makosinshi, tana karasowa ya mike ya amshi tray din daga hannun ta,
"Thanks" ya fada mata, da kanshi ya zuba milk din ya dan kurba Sannan ya fada mata abinda ke tafe dashi, kan ya ganta kuma yanason ta, ameera dai shuru tayi har lokacin tanason tuna inda ta sanshi,
"Bakice komai ba..." Ya fada mata, kara kallon handsome and big boy's face dinshi tayi Sannan tace
"I will need a time to think about it..."
"Ok..no problem... Ki bani digits naki saboda in kiraki....." Number ta bashi, hira suka danyi har lokacin Khalid bai bar mamakin Salem ba, shidai yasan babu abinda irin wannan yarinyan zatayi mashi ya dauki irin matakin da Salem ya dauka kanta,
"Hmmm one man's food is another man's poison or trash..." Yafada cikin ranshi, Sai around 6:00 pm sukayi ban kwana ya tafi. Ameera tana komawa ciki ta fadawa mom yanda sukayi da Khalid,
"Hmmm kin fada mashi kin taba aure?..." Kai ta girgiza mata
"I told him I will think about it..."
"Ok then...ki fada mashi kin taba aure don kar yayi finding out ya zama problem... Let me ask you... Did you like him?..." Murmushi ameera tayi
"Mom he looks cool and nice.."
"To Allah ya shige mana gaba..."
"Ameen" ta amsa Sannan ta shiga dakinta, tana shiga wayanta ya fara ringing, sunan Wanda ta gani yasata sakin murmushi, picking tayi tare da sallama, daga chan bangaren Salem yace
"Babe ya kike?..."
"Lafiya lau...ya sis Tawakaltu?..."
"Tana lafiya...she's sleeping... Yasu affan?..."
"Duk suna lafiya..."
"That's good to hear... Meye labari?..." Ya tambayeta sounding naughty,
"Babu...labari" Dariya yayi
"Anya?... You sound as if you are lying..."
"Da gaske babu labari.."
"Nidai ki fadamin ko wani ya ganemin mata..." Dariya ameera tayi
"Wacce Matan kuma?..." Ahankali yace
"ke mana.." Ameera shuru tayi batace kala ba
"Kinyi shuru..." Ya fada ahankali
"Me zance?..."
"Ki fadamin mana in wani ya ganemin ke inyi Maganin shi..." Ahankali tace
"Aini ba matarka bace..." Dan Dariya yayi
"Ke matata ce mana...ko kin manta?.."
"Ni ba matarka bace..."
"You are my wife..." Yafada cikin whisper,
"Hmmm nidai Aa..."
"Daman nasan baki sona...amma you are still my wife... Na daya kina period when I divorced you... Na biyu ban taba fada maki saki nawa nayi maki ba I only told you na sakeki...." Ameera dai shuru tayi tana sauraron ikon Allah. Salem yacigaba dacewa
"Ke matata ce..."
"Please sir can we stop this conversation?..."
"Stop calling me sir...ai you are not working under me..."
"Naji..amma can we stop this conversation?..."
"Yes...for now...ki gaida min su momcy..."
"Zasuji..."
"Ki turomin account number dinki...let me send you some money in case zaki bukaci wani abun..."
"No thanks... Bana bukatan komai..."
"Bye then..." Ya fada Sannan ya katse wayan shi. Da sauri ta kara komawa wurin mom ta fada mashi abinda Salem yace.
"Just forget about him...yanason wannan yarinyan so ko da akwai aure a tsakanin Ku yanzu bazaiso ki yanda yake son matarshi ba...so fatana shine Allah ya baki Wanda zai soki fiye da yanda yake son matarshi..."
"Ameen... Mommy.." Ta fada Sannan ta kara komawa dakinta.
💙💛💚💜❤
ZAKISAN KONI WAYE
💜❤💚💛💙

®zuwairat(ummu Maryam)

7⃣3⃣
Chapter 77 · 0% Book details